Allah Ya Yiwa Mahaifin Mawaki Nazifi Asnanic Rasuwa


Allah Ya Yiwa Mahaifin Shahararren Mawakin Zamanin Nan Kuma Fitacce Mawaki A Kannywood Rasuwa Wato Nazifi Asnanic, Inda Ya Rasu A Daren Jiya Juma'a Kuma Akayi Jana'izarshi Da Safiyar Yau.

Marigayin Mai Suna Malam Abdussalam Yusuf A Kano Ya Rasune Bayan Wata 'Yar Gajeruwar Rashin Lafiyar Da Yayi Fama Da Ita.

Domin Haka A Madadin Daukakin Ma'aikatan Wannan Shafi Namu Mai Tarin Albarka Muna Mika Sakon Ta'aziyyarmu Ga Daukakin Iyalan Wannan Bawan Allah, Allah Kuma Yaji Kanshi Ya Kyautata Makoncinshi Su Kuma Ya Kara Musu Hakuri Da Juriyar Wannan Rashi Ameen.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia