Home

Music

Video

Kanny

Tags:

An Kama Fasto Sabo Da Yayi Lalata Da Yaya Da Kanuwa


An damke Wani fasto mai suna Kokoh Emmanuel na cocin Cross Over Ministry da ke Kedjom Kekuh, kasar Kamaru, da laifin yima yan mata 2 yan gida daya ciki. Game da cewar Jaridar Cameroon report, faston yayi ma Akombom Marie claire, yar shekara 18 ciki kuma tana da cikin wata 6 yanzu, Hakazalika yayi ms Brenda Nyingmah, yar shekara 14 , tana da ciki tsawon watanni 3 yanzu.

Faston dan shekara 29 ya amsa cewa ya aikata laifin da ake zarginsa da shi bayan yan sanda sun gudanar da binciken su. Iyayen yan matan da akayi ma ciki suna mika kokon baran su da gwamnatin CPDM, ta kwato musu hakkin shari’a akan faston.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia