An Kama Wani Fasto Bisa Laifin Yima Wata Mata Yar Shekara 42 Fyade

Fasto

An Kama Wani Fasto Bisa Laifin Yima Wata Mata Yar Shekara 43 Fyade.

An tsare faston kuma yan sanda sunce ya dade yana yaudaran mutane da sunan fastonci

An gurfanar da Wani fasto dan shekara 42 mai suna wasiu Lawal da yai ma wata mata yar shekaru 38 fyade ,a ranar laraba 3 ga watan agusta a wata kotun gargajiyan surulere a jihar legas.

Hukumar yada labarai ta kasa ta bada rahoton cewa faston mazaunin ikorodu ne kuma an caje shi da laifin fyade. Lauyan , Sgt Christopher Okoniko ya fada ma kotu cewan abin tuhumar ya aikata aika-aikan ne a ranan 1 ga watan yuli misalin karfe 9 na dare a Legas.

Ya ce abin tuhumar,wanda yayi ikirarin shi fasto ne, boka, kuma malami ya tilasta matan tayi jima’i da shi da sunan yana mata addu’a Matan tace ita bata san yadda ya kwana a gidan kutumin ba har sai da gari ya waye.

“Tace a ranan ta fada ma mijinta abinda ya faru wanda ya kai karan zancen ofishin yan sanda da ke ikorodu ,sai aka kamashi. Abun laifin na amfani da daki daya wajen aikin fastonci, wani daki aikin bokanci, wani daki kuma da sunan malinta.”

Laifuffukan guda biyu sun saba ma Section 258 of the Criminal Law of Lagos State, 2011. Alkali mai sharian kotun gatgajiyan, Mts Dan oni, ta ba faston belin kudi N200,000 da kadarori biyu. Tace wadanda zasu biya masa sai ya kasance ma’aikaci mai biyan haraji. An dakatad da karan zuwa ranan laraba, 14 ga watan satumba.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia