An Kama Wani Malamin Jami'a Shida Dalibarsa Zindir A Wani Hotal


An kama wani malamin jami’ar jihar Delta zindir a Wembley hotel yayinda yak e kokarin lalata da wata dalibar shi mai suna Esther Omokinovo.

Dalibar ta fada ma jami’an yan sanda a ranan 19 ga watan yuli cewa malamin ta na jami’a ya dade yana mata wulakanci kuma yayi mata barazanar cewa indan bata bashi goyan baya yayi lalata da it aba, sai ta fadi jarabawa.

Kwana biyu bayan haka, lokacin jarabawan lissafi, yarinyar ta kai kara ofishin yan sanda domin fada musu cewan ta amince da ganawa da shi a wani wuri. Kwamishanan yan sandan jihar, Zanna Muhammad Ibrahim, ya fadi a hedkwatan yan sanda da ke asaba a ranan 6 ga watan agusta cewa an kama malamin jami’an zindir haihuwan uwarshi yayinda yak e kokarin lalata da dalibar shi.

Ibrahim yace : “ Game da amincewan da yarinyan tayi domin lalata da ita, ya kaita gidan hutun Wembley hotel,abraka, sai aka gayyaci jami’an yan sanda suka je suka kama a cikin gidan hutun zindir.”


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia