An Kashe Sojoji Tare Da Kwace Jiragen Ruwa Uku A Niger Delta


Wasu 'yan bindiga a garin Nembe da ke jihar Bayelsa sun kashe sojoji uku a lokacin wani hari da suka kai musu a ranar Litinin.

Jama'in tsaro da mazauna yankin sun shaida wa Sashen Hausa Na BBC cewa 'yan bindigar sun kuma kwashe makaman sojojin sannan suka tsere a cikin wani karamin jirgin ruwa.

Sun kara da cewa mai yiwuwa 'yan bindigar sun kwace akalla jiragen ruwa guda uku na sojojin, wadanda aka kai wa hari a lokacin suna bakin aiki.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia