Home

Music

Video

Kanny

Tags:

An Sace Wasu 'Yan Kasar China Biyu A Jihar Nasarawa

Yan China

'Yansanda a jihar Nasarawa sun ce wasu 'yan bindiga sun sace 'yan kasar China biyu dake aiki a wani kamfanin tonon ma'adinai.

Kakakin rundunar 'yansanda a jihar Numan Umaru Isma'ila shaidawa Sashen Hausa Na BBC cewa, da misalin karfe biyu da minti rabi na ranar Jumma'a ne 'yan bindigar da suka far wa mutanen, a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Abuja daga kauyen Ajada.

Ya ce mutanen XJieng AI Jung mai shekaru 50, da Wenso Ping mai shekaru 45 na tafiya tare da wani jami'n tsaro, wanda shi kuma suka harba a kafa, kuma yanzu haka ana yi masa magani a wani asibiti.

Rundunar 'yansandan ta ce ta tura jami'anta cikin dazuka domin farautar 'yan bindigar, tare da hadin guiwar wasu 'yan banga da kuma shugabannin al'ummar yankin.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia