Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Bama Tsoron EFCC Ta Bincike Mu Inji Dan Majalisa Hon Ado Doguwa


Shugabannin majalisar wakilan Najeriya sun ce ba sa wata fargabar binciken da hukumar EFCC za ta yi game da danbarwar da ta baibaye kasafin kudin bana.

Hon Alhasan Ado Doguwa, shi ne mai tsawatarwa na majalisar kuma daya daga cikin wadanda ake zargi da badakalar, ya shaida wa sashen hausa na BBC cewa bai ji ko dar ba a kan batun binciken.

A cewar sa doka ce ta kafa hukumar EFCC, dan ta gudanar da bincike saboda haka a shirye yake ya amsa dukkan tambayoyin da za a masa game da kasafin kudin.

Sai dai ya musanta cewa sun yi cushen karin kudade a kasafin kudin na bana, kamar yadda tsohon shugaban kwamitin kasafin kudin Abdulmumini Jibrin ke zargin su da aikatawa.

Tun dai bayan sauke shi daga mukamin, Abdulmumini Jibrin yake ta yin tonon silili ga shugabannin majalisar, da zarge-zargen cin hanci da rashawa tsakanin su.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia