Buhari Ya Sake Farfado Da Shirin Yaki Da Rashin Da'a


A yau, Litinin ne, Gwamnatin Tarayya Karkashin Jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta sake farfado da shirin nan nasa na zamanin mulkin soja na yaki da rashin da'a inda aka kaddamar da jami'an da za su aiwatar da shirin.

Da yake karin haske game da shirin, Babban Daraktan Hukumar Wayar da Kan Jama'a na Kasa, Garba Abari ya nuna cewa matakin ya zama dole idan aka yi la'akari da halin da kasar nan ke ciki na rashin tsaro da miyagun dabi'u.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia