Buhari Yayi Ganawar Sirri Da Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan


Shugaban Muhammadu Buhari ya gana da Goodluck Jonathan a fadar shugaban kasa da ke Abuja.


Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter.

Sai dai bai yi karin haske kan batutuwan da suka tattauna a kai ba.

A baya bayan nan dai masu tayar da kayar baya na yankin Naija Delta -- wadanda suka rika fasa bututan man fetur -- sun sha alwashin ayyana kasarsu mai cin gashin kanta a ranar daya ga watan Agusta.

Sai dai wasu rahotanni sun ambato su suna cewa sun janye aniyarsu ta ayyana kasar Naija Delta ne bayan Goodluck Jonathan ya hana su yin hakan.

Gwamnatin Shugaba Buhari dai ta kama wasu manyan jami'an tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan, cikinsu har da manyan tsofaffin jami'an tsaro da manyan jami'an jam'iyyarsa ta PDP bisa zarginsu da karbar cin hanci da wasu laifuka da suka shafi wawure kudade.

Sai dai jami'an sun yi watsi da zargin suna mai cewa siyasa ce kawai.

Shi kansa Goodluck Jonathan ya taba cewa gwamnatin ta Buhari tana gudanar da bincike a kansa a kan cin haci da rashawa.

Wannan dai ba shi ne karon farko da tsohon shugaban kasar ke ganawa da Shugaba Buhari ba.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia