Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Dubun Wani Mai Saida Mushen Kaji Wa Jama'a Ya Cika A Jihar Kano


Shidai Dubun Wannan Matashi Mai Suna Isma'ila Ya Cikane A Daidai Lokacin Da Gungigayar Yan Sintiri Ta Vigilante Ta Unguwar 'Yar Akwai Dake Karamar Hukumar Tarauni Ta Kai Samame.

Matashin Yace Yana Samo Matattun Kajin Ne A Wani Gidan Gona Inda Ake Zubar Dasu Bayan Sun Mutu, Sai Ya Gyara Ya Siyar Ma Wadanda Ba Musulmai Ba Su Siya Su Tafi Dasu Garuruwansu

Sai Dai Shugaban Kungiyar 'Yan Vigilante Isiyaku Garba Yace, Wannan Shine Karo Na Uku Sama' ila Na Fadawa Tarkon Su Inda Yake Cewa Ya Tuba Kuma Yayi Alkawarin Bazai Sake Ba, Amma Yanzu Sai Gashi Ya Sake Domin Haka Bazamu Kyaleshi Ba.

Inda Kuma Ya Kara Da Cewa Koba Musulmai Zasuci Wannan Naman To Akwai Hadari, Ballantana Bamu Sani Ba Kila Kabilun Da Muke Tare Dasu, Da Wasu Bata Gari Suna Siya Suna Sa Mana A Abincin Da Muke Siya A Wurinsu. Domin Haka Yanzu Haka Mun Kammala Shirye Shirye Zamu Mikashi Zuwa Ga DPO Na Wannan Karamar Hukuma..


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia