Dubun Wata Mata Mai Safarar 'Yan Mata Zuwa Kasashen Turai Ya Cika

Dubun Wata Mata Mai Safarar 'Yan Mata Zuwa Kasashen Turai Ya Cika


Dubun wata ta da ta yi kaurin suna wajen safarar ‘yan mata zuwa kasashen Turai domin yin karuwanci ya cika, matar mai suna Franca Asemota na yaudarar ‘yan mata zuwa Turai da karairayi, daga karshe ta mayar da su karuwai.

Jaridar Daily Mail ta Ingila ce ta bayar da labarin kama Franca Asemota ‘yar asalin Benin jihar Edo, ‘yar shakara 38, wacce ke safarar ‘yan mata daga Najeria zuwa Turai ta filin jirgin saman Heathrow.

Franca
Gadai Tanan A Daidai Lokacin Da Zami'an Tsaro Ke Taso Keyarta Zuwa Nigeria

Franka
Franca da jami’an tsaro a Ingila a lokacin da ake iza keyarta zuwa Najeriya.

Antie Franca kamar yadda ake kiranta, ta yi safafar sama da ‘yan mata 40 zuwa kasashen Turai ta Ingila, a inda ta ke dauko ‘yan matan daga gaban iyayensu a kauyukan Najeriyada zimmar cewa za ta samar musu kyakkyawar rayuwa a Turai, amma da zaran ta raba su da gida, sai ta jefa cikin kangin karuwanci da bauta.

Aunty Franca
antie Franca

Wata kotu a Ingila ce ta samu Franca da laifukan da ake tuhumarta da su guda takwas, wandanda suka hada da safarar mutane, da kuma cin zarafi; dubun ta ya cika ne a watan Satumbar shekarar 2011 a inda a lokuta daban-daban yi safarar mata zuwa rukuni-rukuni.

Mai gabatar da kara ya bayyana cewa Franca na tirsasa ‘yan mata ne idan sun isa kasar waje ta hanyar barazana ga rayuwarsu da amfanin da boka sa tsibbu idan ba su bata hadin kai ba. An kuma iza keyar ta zuwa Najeriya.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia