Home

Music

Video

Kanny

Tags:

EFCC Ta Sake Cika Hannu Da Tsohuwar Ministan Kudi A Jihar Gombe

Nenadi Usman

Ana zargin tsohuwar karamar Ministar da hannu a wata badakalar N23 biliyan

Tsohuwar Ministan ta amsa raba kudaden ga PDP a wasu jihohin arewa maso kudu

Sanata Nenadi Usman ta sake shiga hannun hukumar EFCC a bisa zargin hannu a wata badakalar Naira biliyan 23 da tsohuwar Ministan man fetur Diezianni Allison-Madueke ta raba.

Wani bincike na hukumar ya bankado wasu kudade kimanin Naira bilyan 1 da miliyan 85 da tsohuwar Ministan mai ta mikawa wasu tsaffin gwamnoni da kuma sanatoci, Nenadi dai ita ce daraktan kudi da mulki na yakin neman zaben Jonathan.

A cewar mata Majiya a lokacin da ake yi wa Nenadin tambayoyi , ta amsa cewa ta hadu da Diezannin gabannin babban zaben na shekarar 2015 a inda ta ba ta wata takarda mai dauke da adadin wasu kudade da aka umarce ta rarrabawa ofishin PDP da ke jihohin ta wani bankin kasuwanci.

Majiyar ta kuma kara da cewa Nenadin ta bayyana cewa: “…Ta ba jihar Bauchi Naira miliyan 500 ta hannun Sanata Garba Babayo, ta ba Gombe Naira miliyan 450 ta hannun Sanata Sa’idu Kumo, jihar Adamawa ita nma ta samu Naira miliyan 450 ta hannun James Ngilari, jihar Taraba ta karbi na ta kason na Naira miliyan 450 ta hannun Sani Danladi da kuma Sanata Joel Ikenya …”

A watan Yuli ne EFCC ta gurfanar da Nenadi da kuma Femi-fani kayode a gaban kotu a bisa zargin wasu kudade kimanin Naira biliyan 4 da miliyan 9.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia