Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Hukumar EFCC Ta Saki Tsohuwar Ma Aikaci Yar BBC Jamila Tangaza


Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya-EFCC ta saki tsohuwar ma aikaciyar shashen hausa na BBC kuma a yanzu itace shugaban sashen kula da mallakar filaye a hukumar mulki ta birnin tarayya Abuja, Hajiya Jamilah Tangaza.

Makonni biyu ne dai da su gabata hukumar ta EFCC ta kama Hajiya Jamilah Tangaza bisa Laifin karkatar da wadansu kudade a hukumar kula da mallakar filaye a birnin na abuja.

Inda a halin yanzu wata majiya mai karfi ta tabbatar mana da cewa Hajiya Jamilah Tangaza ta koma gidan ta da yammacin wannan rana ta talata.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia