Hukumar 'Yan Sandan Jihar Kano Ta Rufe Gidan Sanata Kwankwaso


Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta rufe gidan Tsohon Gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso bayan aurar da Zawarawa 100 da gidauniyarsa ta Kwankwasiyya ta yi a asirce.

Rahotanni sun nuna cewa wadanda suka ci gajiyar auren sun yi dafifi a gidan wanda ke titin Nasarawa GRA don karbar kyaututtukan da aka yi masu alkawari.

Idan ba a manta ba, rundunar 'yan sandan jihar ta haramta gudanar da bikin Auren tun a makon da ya gabata bayan rahotannin cewa wasu na son amfani da wannan dama wajen tayar d rikici.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia