Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Masu Fama Da Yunwa Sun ƙaru A Jihar Borno da Yobe'


'
Majalisar ɗinkin duniya ta ce, yawan masu matuƙar buƙatar tallafin abinci a yankin arewa maso gabas na Nigeria ya nunka zuwa mutane 4.5 daga watan Maris da ya gabata zuwa tsakiyar watan Agusta.

Sanarwar da jami'in hukumar samar da abinci ta majalisar ɗinkin duniya mai kula da yammacin Afirka, Abdou Dieng ya fitar ta ce, a jihohin Borno, da Yobe yawan mutanen da ke fama da rashin abinci yana ƙaruwa sosai.

Hukumar samar da abincin ta majalisar dinkin duniya ta kuma ce, rikicin Boko Haram ya raba mutane da dama da muhallinsu, da sana'oinsu; lamarin da ya jefa su cikin matuƙar matsalar ƙarancin abinci.

Alƙaluman hukumar sun ce, mutane akalla 65,000 dake zaune a yankunan da aka ƙwato daga 'yan Boko Haram suna fuskantar yanayi da ya yi kama da na bala'in yunwa mai tsanani.

Hukumar ta ƙara da cewa, tana bukatar akalla dalar Amurka miliyan 52 domin ci gaba da samar da tallafin abinci na gaggawa a arewa maso gabashin Nigeria.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia