Nigeria Farat Daya Mun Tsiyace Inji Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Yace Tashi Guda Nigeria Ta Tsiyace Inda Yayi Kalaman Nasa A Babban Birnin Tarayya Abuja Inda Ya Kara Da Cewa..

Shekarar nan ta zo wa Najeriya cikin mawuyacin hali. Kafin mu karbi mulki ana sayar da gangar danyen man fetur a kan $100 (£77), amma da hawan mu sai ya koma $37, kuma yanzu haka ana sayar da shi daga $40 zuwa $45".

"Farat-daya mun koma kasar da ta tsiyace, amma kokarin da ake yi na tsantseni da tabbatar da gaskiya shi ke sa mutane ba sa fahimtar ainihin halin da ake ciki", in ji Shugaban na Najeriya.

Wadan Nan Kalama Na Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Dai Yayi Sune A Daidai Lokacin Da Aka Fitar Da Wani Rahoto Wanda Ke Cewa Kasar Africa Ta Kudu Itace Kasar Datafi Ko Wacce Kasa A Nahiyar Africa Karfin Tattalin Arziki.

Tun Biyo Bayan Lokacin Da Gwamnatin Kasar Nan Tayi Ikirarin Cewa Nigeria Itace Kasa Ta Farko Da Tafi Ko Wacce Kasa Karfin Tattalin Arziki A Sherar 2014 Din Data Wuce.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia