Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Nigeria Tayi Nasarar Doke Kasar Japan A Gasar Wasan Olympic A Birnin Rio.

Gasar Olympic

Tawagar kwallon kafar Mu Daganan Gida Nigeria bangaren maza ta samu nasara a kan takwararta ta kasar Japan a gasar wasannin motsa-jiki na Olympics a birnin Rio.

Tawagar 'yan wasan Namu , Dream Team, ta doke Japan da ci 5-4 a gasar Olympic duk da cewa ba su isa birnin Rio na kasar Brazil da wuri ba, lamarin da wasu masu sharhi ke ganin ya saba wa ka'ida.

A jiya da daddare ne aka yi wasan gabannin bikin bude gasar a hukumance.

Idan an jima ne za a gagarumin bikin bude gasar a hukumance.

Rahotanni daga birnin Rio da sauran biranen da za a yi wasannin gasar na cewa na dauki tsauraran matakan tsaro.

Mahkunta a kasar na fuskantar kalubale daga masu adawa da gasar, wandanda tun jiya Alhamis suka yi zanga-zanga, har wasu daga cikinsu suka yi yunkurin kashe fitilar gasar da ruwa a bokatai.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia