Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Shin Ko Kunsan Wane Ne Al-Barnawi Sabon Shugaban Kungiyar Boko Haram

Abu Mus

Ko Kunsan Wane Ne Al-Banawi Sabon Shugaban Kungiyar Boko Haram


Mutumin da kungiyar masu fafutukar kafa daular Musulunci ta IS, ta sanar a matsayin sabon shugaban bangarenta na Yammacin Afirka, wato wacce aka fi sani da Boko Haram, ba fitacce ba ne a kungiyar.

Abu Mus’ab al-Barnawi ya taba fitowa a wani faifen bidiyo a matsayin mai magana da yawun kungiyar a watan Janairun shekara ta 2015.

Wannan kuwa ya faru ne tun kafin kungiyar ta yi muba’iya ga kungiyar ta IS, wacce ke rike da wurare da dama a kasashen Syria, Iraki da kuma Libya.

Sai dai ko a wancan lokacin ma ya rufe fuskarsa.

A jawabin da yayi a faifen bidion na baya-bayan na da IS ta fitar, alamu sun nuna cewa al-Barnawi mutum ne wanda sai ya tauna kafin ya furzar.

A cikin bidion yayi kashedin cewar duk garuruwan da suka kufce masu a yunkurin da suke yi na kafa daular musulunci za su tabbata sun shafe su daga doron kasa.

Kana ya bayanna cewa suna kyamar turbar dimokradiyya da karatun boko.


An dade ba a ji duriyar Abubakar Shekaru ba

A wata hira da yayi da wata mujallar IS a kwanakin nan, ya kara nanata cewa Boko Haram da aka fi saninsu da shi ba sunansu ba ne.

Abu Mus’ab al-Barnawi dai ya maye gurbin Abubakar Shekau wanda akafi sani a matsayin shugaban kungiyar.

Tun watan Agustan shekara ta 2015 ne dai aka daina jin duriyar Abubakar Shekau. Kuma bai ce uffan game da maye gurbin na sa ba.

Shin yana da rai ko a’a shi ne babu tabbaci kawo yanzu.

Abin da za a sa ido a gani shi ne irin tasirin da al-Barnawi zai yi a matsayin sabon shugaban, ganin cewa sojoji na ikirarin sun ci karfin kungiyar, sauran burbushinsu ne kawai ya rage.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia