Sojoji Sunyi Babban Kamu Daga Dajin Sambisa Zuwa Birnin Kebbi


A Ci Gaba Da Yakin Da Rundunar Sojojin Kasar Nan Keci Gaba Dayi Kamar Kullum Ta Yadda Suketa Kara Samun Galaba Akan Yan Kungiyan Boko Haram Musamman A Yankin Arewa Maso Gabas..


Cikin Ikon Allah Yau Ma Sai Gashi Runtunar Ta Kara Samun Gagarumar Nasara Inda Tayi Nasarar Cafke Wani Kasurgumun Dan Kungiyar Ta Boko Haram A Yayinda Yake Ko Karin Arcewa Daga Dajin Sambisa.

Cikin Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce an kama Mohammed Mohammed Zauro a garin Damboa a ranar Talata.

Binciken sojin na farko ya gano cewa an kama mutumin ne a yayin da yake yunƙurin tserewa daga dajin Sambisa zuwa Birnin-kebbi na jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin ƙasar.

Sanarwar ta kuma kara da cewa sojoji sun kama wani ɗan Boko Haram, Lawal Aboi wanda ya yi ikirarin cewa da ma yana kan hanyarsa ne ta zuwa wajen sojojin domin ya miƙa wuya.

Hakan na zuwa ne a yayin da wata mujallar ƙungiyar IS ta sanar da sunan wani sabon jagorar ƙungiyar ta Boko Haram.

Wanda Hakan Ke Nuni Da Cewa Da Wahalan Gaske Tsohon Amirin Kungiyar Na Raye Wato Abubakar Shekau Kamar Dai Yadda Ake Gani Ga Sauran Kungiyoyi Ire Irensu A Duniy Inda Ba A Nada Sabon Shugaba Har Sai Bayan Wanda Ya Gaba Ceshi Ya Mutu.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia