Sojojin Nigeria Sunyi Nasarar Hallaka Yan Bindiga Biyar A Neja Delta

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe wasu 'yan bindiga biyar da suka kai wa sojoji hari a lokacin da suke wani atisaye a yankin Niger Delta.
Kakakin rundunar sojin kasa ta kasar, Kanar Sani Usman Kukasheka ya shaida wa BBC cewa sojojin sun kama wasu da ake zargi su ashirin da bakwai, yayin da wasu 'yan bindigan kuma suka samu raunuka.
Kanar Kukasheka ya ce sojojin sun kuma kwace makamai daga hannun 'yan bindigan da suka hada da bindigogin AK-47 biyu, da karamar bindiga kirar gida, da harsasai da dai sauran su.
Ya ce sojojin sun kuma gano wani jirgin ruwa da 'yan bindigan suka gudu suka bari.
Lamarin ya auku ne yayin da sojoji daga runduna ta musanman ta 133 ke gudanar da atisaye mai taken "Murmushin Kada", da nufin yaki da masu aikata laifuka a yankin Niger Delta.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia