Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Tsagerun Niger Delta Avengers Sunce Basu Tsorata Ba Kan Samamenda Aka Kai Musu

Naija Delta Avengers


Mayakan sun bayyana cewa su basu ji tsoro ba sun kuma zargi sojoji da cewa suna wasa da yaki

Sun kuma bayyana cewa sake fasalin al’amuran Najeriya bai tsaya a kan NDA kawai ba

Tsagerun Niger Delta Avengers (NDA) sun kalubalanci sojojin Najeriya da su nuna wa duniya hotunan yan bindigan da aka kashe.

Brigadiya-Janar Mudoch Agbiniba, kakakin kungiyar NDA, ya bayyana sunan sabon shafin kungiyar a shafin Twitter wato @agbiniboND, ya kuma bayyana cewa shafin sadarwa na Twitter bazasu iya dakatar ko ta toshe yunkurinsu ba.

Sojojin sama na kasar Najeriya sunyi aikin kwanaki biyar a sansanin yan bindigan da ake zargi a yankin Arepo, jihar Ogun.

Bisa ga rahotannin sojojin, an kasha sama da yan bindiga 100 yayin da aka kama wasu da dama kuma wasu da dama sun sauke magaman yaki. A ranar Laraba 3 ga watan Augusta, sojoji sun bayyana cewa sun tursasa masu fasa guraren mai barin yankin, sun kuma kara da cewa dakarun sojojin suna biye dasu.

Bayan musayar wuta da akayi a baya, sojojin sun shirya kai mayakan kasa.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia