Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Wani Shugaban Fulani Ya Mika Makamanshi Ga Sojoji A Jihar Zamfara


Wani shugaban Fulani makiyaya a jihar Zamfara ya mai suna Alhaji Ruwa, a bisa ra’ayin kansa, ya mika makamansa da kuma wasu albarusai ga rundunar soji ta bataliya 223 da ke karkashin Briged ta 1 da ke jihar Zamfara.

Alhaji Ruwa ya mikawa sojojin wasu bindigogi biyu kirar gida, da kuma bindigogin farauta guda uku ga sojin, ya kuma yi alkawarin shawo kan mutanensa da suma su ajiye na su makaman ba tare da bata lokaci ba.

Kakaki, kuma mai rikon mukamin Daraktan yada labarai na rundunar sojin kasa, Kanar Sani Kuka Sheka Usman ne ya bayyana hakan, ya kuma kara da cewa, Alhaji Ruwa ya dau alkawarin shawo kan sauran makiyaya da ke dauke da makamai da su fito da su mika makamansu ga gwamnati.

A cewar Kuka sheka, “ na daya daga cikin nasarorin da ake samu na raba jihar Zamfara da satar shanu da kuma ta’addancin ‘yan bindiga a yankin.”


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia