Yan Bindiga Dadi Sun Hallaka Wani Malamin Jami'a Har Cikin Makaranta A Jihar Benue
Jami’an Mkar, Mkar (UMM). Na jihar Benue ya shiga halin juyayi da makoki a jiya 11 ga watan Augusta, lokacin da wasu yan bindiga da ba’a san ko su waye ba suka kai hari al’umman jami’an kuma suka kashe wani babban malamin jami’an.

An kashe Malamin jami’an, Mr Wilfred Aondosoo Tondo, wani malami a ne a sashen political science (kimiyyar siyasa) na makarantar, a gaban Iyalin sa. An ce masu kisan sun kai hari un guwar Tondo da misalign karfe 4:30 na asuba, kuma sun mike zuwa dakinsa inda suke addu’ar safe tare da iyalan sa. Suka harbe shi har lahira.

An bayyana cewa Tondo yana takarar kujerar chiyaman a karamar hukumar Buruku na jihar, don aka ana zargin an aiwatar da kisan ne a siyasance.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia