'Yan Gidan Yari 15 Sun Arce Daga Gidan Yarin Jihar Inugu

Yan

Daga Sani Musa Mairiga, Abuja

Akalla fursunoni goma sha biyar ne suka tsare daga gidan yarin Nsukka dake jihar Enugu a daren jiya.

Wata majiya ta tabbatarwa wakilinmu cewa fursosunan sun haye babbar katangar gidan yarin inda arce.

Babban Jami'in kula da gidan yarin Mista Lawrence Okonkwo wanda ya tabbatar da faruwan wannan almarin, ya ce jami'an hukumar kula da gidan yari ta ka wato gandirobobi suna baza komar su domin kama 'yan zaman wakafin da suka gudu.

Wasu rahotonin daga Nsukka sun ce an riga an kama biyu daga cikin fursunonin a yayin aka zafafa farautar sauran.

Duk kokarin da wakilin mu ya yi na jin ta bakin jami'in hulda da jama'a na hukumar kula da gidajen yari na kasa ya ci tura, inds ya kira wayar sa amma a kashe ya aika masa sakon kar ta kwana amma har lokacin da yake rubuta wannan labarin bai aiko da amsa ba.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia