'Yan Gudun Hijira Sunyi Zanga Zanga Sabo Da Yunwa A Jihar Borno


'Yan Gudun hijira sun fito zanga-zanga a garin Maiduguri a dalilin matsanancin yunwa da rashin kulawa da gwamnati ba ta yi musu.

"Babu ruwa, babu magani, babu abinci kuma an hana mufita yin bara domin ciyarda kanmu sannan anki a maida mu garuruwan mu sai bakar wahala kawai muke sha a san-sanin gudun hijiran." Inji Aisha daga Marte wanda tana zaune ne a daya daga cikin sansanin gudun hijiran.

Daruruwan 'yan gudun hijirane dake san-sani dabam dabam a jihar Borno suka fito domin yin zanga-zanga domin nuna wa gwamnati irin halin da suka shiga a sansanonin na matsanancin yunwa da rashin ruwan sha.

'Yan gudun hijiran dai sunce suna cikin matsanancin yunwa sannan babu wata kula da suke samu daga gwamnati.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia