Hukumar EFCC Na Neman Ibrahim Shehu Shema


Hukuma mai yaki da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, EFCC, ta ce, tana neman tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema ruwa a jallo.
EFCC ta sanya sanarwar ne a shafukanta na Internet, a inda ta ce "duk wanda yake da labarin wurin da tsohon gwamnan yake, to ya sanar da ita da gaggawa."
Sanarwar ta ce hukumar EFCC ta dade tana ta faman gayyatar tsohon gwamnan amma yaki amsa gayyatar.
Hukumar ta ce tun watan Disambar 2015 take neman Shema amma hakan ya faskara.
EFCC dai ta ce tana zargin Ibrahim Shehu Shema ne dai bisa zuga kudaden kwangila da suka wuce kima.
sauran laifukan sun hada da barnatar da dukiyar al'umma da yin amfani da mukaminsa ta hanyoyin da ba su da ce ba.
Yanzu dai hukumar EFCC tana rokon jama'a da su shaida mata duk inda tsohon gwamnan yake.
Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Aminu Bello Masari dai tana zargin tsohon gwamnan da sace makuden kudade daga baitul malin gwamnatin jihar.
Sai dai kuma tsohon gwamnan, Ibrahim Shema da magoya bayansa sun sha musanta zargin.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia