Adam A. Zango Ya Caccaki Masu Digiri A Shafin Instag


Fitaccen jarumin Kannywood Adam A. Zango ya caccaki mutanen da suka yi karatun boko har suka mallaki shaidar digiri.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, jarumin ya yi shagube cewa shi ba shi da shaidar kammala karatu ta digiri amma ya fi masu digiri amfani.

A cewarsa, "Idan ka mallaki digiri baka da aiki. Ni kuwa ba ni da digiri amma shekara 12 ina da aikin yi. Ko da kana da aiki idan na rera waka daya zan samu kudin da suka fi albashinka."

Da alama dai yana yin raddi ga wasu ne, wadanda bai fadi sunan su ba.

Zango ya ce bai iya turancin ba, yana mai cewa wadanda suka iya turancin sai su "ci shi" idan abinci ne, yayin da shi kuma zai rika yin larabci.

Sai dai wannan batu ya jawo masa suka daga wajen wasu masu amfani da shafukan sada zumunta, inda daya daga cikinsu ke cewa "ai ni ban taba jin Zango ya yi larabci ba."


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia