Ankama Wani Mai Buga Kudin Jabu A Jihar Sokoto


Hukumar tsaro na farin kaya "Nigerian Security Civil Defence" tayi nasarar damke, wani mutun mai suna Collin Nzewewe bisa laifin buga kudin jabu a jihar Sokoto.

Collin Nzewewe mai shekaru arba'in da biyu yanada 'ya'ya bakwai kuma dan asalin jihar Imo ne, a kauyen Orlu ta kudu cikin karamar humar Orlu.

Sai dai Collins Nzewewe yace wani mutum ne dan asalin kasar Nijar, mai suna Abdullazeez ya jefashi cikin wannan mummunan sana'ar ta buga kudin jabu.

Shidai collins Nzewewe tsohon mazaunin garin sokoto ne, wanda ya shafe tsawon shekaru Uku a garin na sokoto, kuma babbar sana'arsa itace gyaran Babur, amma iyalinsa suna can a jihar Imo da zama.

Kwamandan jami'an tsaron na farin kaya wato "Nigerian Security Civil Defense" na jihar Sokoto, Baban Gida Abdullahi Dutsenma, a lokacin da yake gabatar da shi tare da wasu tsageru a gaban manema labarai, yace sunbi sahun mai buga kudin jabun ne bayan da suka samu rahoto daga wasu yan kasa na gari da suka tsegunta musu game da yadda yake gudanar da harkokinsa.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia