Anzabi Wani Musulmi Bahaushe Kansila A Kasar Amurka


An zabi wani musulmi bahaushe dan asalin kasar Ghana a matsayin kansila a Majalisar Karamar Hukumar birnin Portland Maine da ke jihar Maine ta Amurka.

Zaben nasa na zuwa ne yayinda Musulmi da sauran baki a Amurkar ke ci gaba da nuna fargaba game da makomarsu a kasar bayan zaben Donald Trump a matsayin shugaban kasa; saboda matakan da ya ce zai dauka na ko dai kora, ko na hana wasu shiga kasar.

A cikin wata hira da sashen Hausa na BBC sabon kansilan Pious Ali ya ce aikin da ya yi na baya a hukumar ilmi ta karamar hukumar ne ya taimaka wajen zabensa.

'' (An zabe ni ne) domin mutane sun ga aikin da nake yi. Sun ga aiki na aiki ne na taimakon yara. Shi ya sa kowa na son mai taimakon yara.''

0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia