Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Mutane 155 Ne Yan Bindiga Suka Hallaka Inji Gwanan Zamfara


Mutane 155 Ne 'Yan Bindiga Suka Hallaka A Jihar Zamfara, Inji Gwamna Yari

A yammacin jiya Litinin ne Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya gabatar da wani jawabi na musamman ta kafafen yada labarai ga al'ummar jihar, domin bayyana musu halin da jihar ke ciki ta fannin tsaro da kuma kokarin da gwamnati ke yi na ganin ta shawo matsalolin da ake fuskanta.


A cikin jawabin nasa, Gwamna Yari ya bayyana adadin mutanen da aka kashe a kananan hukumomin Maru, Shinkafi da Zurmi, wadanda yawan su ya kai 155, yayin da aka kiyasta a kalla mutane 48 'yan bindigar suka sace, inda suke garkuwa da su.

A yayin da Gwamna Abdulaziz Yari yake kara kwantar da hankalin jama'a su kara hakuri bisa wannan fitina ta kisan gilla da hare hare 'yan ta'adda, gwamnan ya kuma bukaci gwamnatin tarayya ta kara yawan sojojin da suke aikin tabbatar da tsaro a cikin jihar, domin iya cimma karfin maharan da suke cutar da al'ummarsa.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia