Matasa Sun Share Inda 'Yan Majalisu Suka Yi Taro A Bauchi


Matasa Sun Share Inda 'Yan Majalisu Suka Yi Taro A Bauchi

Biyo bayan taron da kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya yi a yankin da ya ke wakilta wanda ya samu rakiyar 'yan majalisun jihar Bauchi ranar Juma'a da Asabar a jiya dubban matasa sun share  filin da 'yan majalisar suka yi taro.

A cewar matasan, sun yi wannan shara ne domin su kauda dattin da 'yan majalisar suka zuba musu a yankinsu.

Matasan sun hallara a filin ne jiya Lahadi da safiya inda suka yi ta share-share da wanke-wanken wuraren da 'yan majalisun suka yi taronsu.

Indai ba a manta ba 'yan majalisun jihar Bauchi sune sahun gaba cikin 'yan majalisun kasar nan wadanda suke takun saka da talakawan da suke wakilta, inda har ya kai ga wasu daga cikin 'yan majalisunsu sun sha da kyar a mazabunsu a wasu lokuta.

Wannan sharar da matasan suka yi a cewar wasu daga cikinsu na nuni ne da irin yadda matasan suka ki jinin 'yan majalisun nasu.

Kalla Cikin Hotuna.


© ZumaTimes


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia