Shin Ko Za'a Iya Hana Almajiran Ci A Yankin Arewacin Nigeria ?


Shin Ko Za'a Iya Hana Almajiran Ci A Yankin Arewacin Nigeria ?

Daga Faisal Abbas NG

Alal hakika abune mawuyaci a iya hana Almajiranci A Yankin Arewacin Nigeria.

Sakamakon batun hana almajiranci a Arewacin Nigeria batune da aka dade ana kai ruwa rana akansa, wanda har yau babu wani kata maiman canji da aka samu.

Hakika almajiranci a yankin Arewacin Nigeria abune dake da asali da tushe tun kaka da kakanni, ta yadda Abun ma har ya juye ya zama kamar wani Al'ada.

Sakamakon kusan da yawa daga cikin manyan malaman da suka fito daga wannan yankin na Arewacin Nigeria zaka samu cewa suma sunyi karatun almajiranci wanda ma, yafi na yanzu tsanani da wahalarwa,  sakamakon irin yanayin da aka tsinci kai a baya na kuntatacciyar rayuwa da, kuma karancin samun ababen more rayuwa a wancan lokacin.

Wanda hakan ka iya nuni da cewa almajiran cin da, yafi na yanzu wahala, to amma inane matsalar take ?

Hakika Allah ya kawo mu wani irin zamani a yau wanda son Zuciya da mugunta sunyiwa mutanen mu yawa kama daga cikin malaman zaure harma dana tsangaya.

Wanda ada duk inda kaji ance za'a kai mutum Makaranta allows,  to zakaji ance karkara za'akaishi, ta yadda zaka samu mafiya yawan malaman wannan  wurin zaunannu ne, ko kuma zaka samu sunada muhallinsu kusan a duk garin da zasu je yawon ci rani.

Amma yanzu mafiya yawan malaman  zaka samu gardawa ne matasa, sannan kuma basu da wurin yada zango sai cikin Birane da Bariki ta yadda suke amfani,  da kananun yara suke sasu bara da roko akan tituna domin biyan wani Haraji da suka sa musu. Duk da cewa basusan cin suba basusan shansu Ba.

Wanda hakan yasha faruwa sauda dama a wasu wurare, kai harma da abunda yafi haka, sannan kuma da matsalar daukan kananun yara da basu wuce 'yan shekara biyar zuwa shida ba, da suke yi wanda hakan yana daya daga cikin abunda yake kara shafawa harkar Almajiranci bakin jini a yau.

Insha Allahu zanci gaba, inda a rubutu na gaba zamu gane laifin waye Iyaye ko malamai gardawa har zuwa yadda za'a kawo gyara a harkan Almajiranci a kuma magance wadannan Matsaloli insha Allahu.

® www.HausaMedia.Com


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia