Anba Duk Wani Inyamuri Wa'adin Watanni Uku Ya Fice Daga Yankin ArewaMun Ba Da Wa'adin Watanni Uku, Dukkanin Wani Inyamuri Ya Fice Daga Yankin Arewa, Inji Kungiyoyin Gamayyar Jama'ar Arewa.

Daga Ibrahim Ammani Kaduna

"Tun bayan da kasar nan ta samu 'yancin kai a shekarar 1960, Inyamurai ke ta haddasa rigingimu da kawo tashin tashina da nuna tsagwaron tsana da kyama ga Jama'ar Arewa, da kaddamar da kisa akan shugabannin yankin Arewa da Jama'ar su, da cusa kansu cikin dukkanin wani abu wanda zai cutar gami da haifar da rigima a yankin Arewa, da kurarinsu a kullum na cewar a raba kasa, da kiran Jama'ar Arewa cima zaune Mabarata! To lamirin ya isa haka kawai a raba kasar kowa ya kama gabanshi, ba zamu lamunci zama da Inyamurai a wata kasa mai suna Nijeriya ba, su fice mana daga yankinmu nan da watannin uku, ko mu dauki munmmunan mataki a kansu!! ".
Wadannan kalamai sun fitone daga bakin Alhaji Shetima Yerima, daya daga cikin shugabannin gamayyar Kungiyoyin cigaban Jama'ar Arewa 16, lokacin da yake jawabi a yayin wani taron manema labarai da gamayyar kungiyoyin suka kira domin bayyana matsayinsu dangane da surutan da Inyamurai sukeyi Karkashin jagorancin Tsagera Nnamdi Kanu masu rajin kafa Kasar Biafra, wanda taron ya gudana a gidan tarihi na Arewa dake Kaduna a Talatar makon nan. 

Shetima Yerima ya cigaba da cewar, tun bayan auren da Turawa suka kulla na son zuciya a tsakanin yankin Arewa da kudancin kasar nan, 'Yan Arewa ke gamuwa da wulakanci da cin zarafi daga Jama'ar kudancin Nijeriya musanman Kabilar Inyamurai, wanda kuma a fili yake kowa ya sani yankin Arewa shike rike da tattalin arzikin Nijeriya tun samun 'yancin kai har ya zuwa shekarar 1972 lokacin da Mai ya bayyana a kudanci, abin mamaki bayan samun Man Fetur da akayi a Kudanci, sai gori da wulakanci ya tashi ga Inyamurai akan Mutanen Arewa, duk suka mance abinda ya faru a baya, babu irin maganganun banza da wulakanci da ba sa fadawa 'Yan Arewa saboda Mai, to lallai ya kamata su gane Arewa ba cima zaune bane kuma lallai a raba kasar shi zai sanya a fahimci haka, a domin haka ya zama wajibi ga dukkanin wani Inyamuri gaggauta barin yankin Arewa nan da watannin uku, hakanan suma 'Yan Arewa su gaggauta dawowa Arewa kafin nan da wata uku, kowa ya tare a yankinshi domin a gane su waye masu lalaci da cima zaune tsakanin 'Yan Arewa da 'Yan Kudu. 

Kungiyoyin Jama'ar Arewan sun kara bayyana muggan Makirce-Makirce da Inyamurai ke haddasawa yankin Arewa, dukkanin wani fashi da makami da akeyi a kasar nan wanda ke sabbaba mutuwar bayin Allah wadanda ba suji basu gani ba Inyamurai nada hannu a ciki, rundunar 'Yan Sanda ta bayyana cewar Inyamurai ne keyin shigar burtu su sanya kayayyakin Fulani su kaddamar da kisa akan bayin Allah a yankin Arewa kuma kowa ya gani balo balo a gabatar dasu gaban manema labarai duniya ta gani, hakanan an samu Inyamurai da hannu dumu dumu wajen safarar makamai ga 'Yan Boko Haram, bayan Kama da dama daga cikinsu da akayi sunyi shiga irinta ta 'Yan Boko Haram sun Kai hare hare akan jama'a, to ya isa haka ba zamu cigaba da zama kasa guda da Inyamurai ba har abada. 

Jama'ar Arewa sun kara da cewar, duk inda ka zaga a Jihohin Arewa zaka taras da Inyamurai na gudanar da harkokin kasuwanci su hankali kwance, sun mallaki Gidaje da kadarori masu dimbin yawa, sannan idan ka koma yankin su dukkanin wani Nama da kayayyakin amfanin gona daga Arewa ake kai musu, amma duk da haka Dan Arewa ba'a bakin komai yake a wajensu ba, suci zarafin shi su aibantashi su kashe shi, kuma abin mamaki a kasashen su Dan Arewa bai isa ya mallaki Shago ballantana gida ba, kuma duk da haka kullum kiran su shine a raba kasa, to muma muna kira da a raba kasar nan, sannan Dattawan Arewa ya kamata suja bakunansu suyi shiru domin tasu ta kare mune Matasa daidai da Matasan Inyamurai muna fadi da babbar murya ba zamu cigaba da zama da Inyamurai a Nijeriya ba, su kwashe ya nasu ya nasu su bar mana yankinmu kafin nan da 1/10/17.0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia