Ci Gaba Da Yakin Biafra, Wasu Kasashe Ne Suka Taimakawa Nigeria ?

Yakin Biafra


Ci Gaba Da Yakin Biafra, Wadansu Kasashe Ne Suka Taimakawa Nigeria.

YAKIN BIAFARA 3

Daga : Hamisu_Hassan_Ahmed

Saboda me wasu kasashe suka taimaki Nigeria?sannan saboda me suka taimaki Ojukwu da makamai da kudi don yakafa kasar Biafara?

yakamata musan duk wani dan tawaye ko dan taada tun daga Ojukwu,har zuwa ga Boko Haram da wannan mara hankalin Kanu,ba wai daga sama ake musu ruwan makamai ba,a'a akwai kasashen da ke basu saboda muguwar manufar su.

-Ojukwu ya mallaki jiragen sama wanda har yafara kai hare hare dasu akan garin Lagos domin yamamaye kudancin Nigeria baki daya.daga ina yasamu wannan makamai da matukan jrage?

-shugaban Gwanatin kasar Congo ne wato Moise Tshombo, ya dakko Mutanen kasar Belgium domin su jagoranci jiragen da zasu taimakama tawaye,shima wannan mutum turawan Belgium sunyi amfani da shi wurin tawaye akasar shi saboda :arzikin da yake garin su wato Katanga.kaga sunyi kama da Ojukwu anan,sannan kasar da take umarnin sa itama zaa raba ganima da ita bayan yaki.

Faransa: -kowa yasan jack fokar ,babban yaron shugaban kasar Faransa wato De Gualle,wannan mutum ya dade yana shirya mugayen abubuwa a Afurka kawai domin su mallake arzikinta.

-antambayi Morist Delonghi, wato shine ambassardo na faransa akasar Gabon, saboda me kuka taimaki Biafara ?sai yace:saboda mu kwashi man Petur,kafaji badan taimakon su ba amatsayin su na mutane,amma har yanzu Jahilai irin su Kanu suna alfahari da su.wannan mutum shine yai taima yan Biafara Training akasar Gabon,sanan da kawo musu makamai akowane lokaci.

Engila: -ta taimaki Nigeria alokacin yakin amma saboda: -itace ta hada kasar tazamo daya. -bazata yarda faransa ta mallake arzikin man Petur din da Kamfanoninta ke hakkuwa ba.saboda kasan idan Ojukwu yasamu nasara wata kila yakore su yamaye gurbin su da faransa.

Potigal: -ta taimaki Biafara, kai sune suka buga musu kudin kashewa saboda: Nigeria tana cikin kasashen da take neman yancin kasashen da Potigal ke musu mulkin zalunci.sai kuma tunanin ganimar petur.

Niger: -tana na gaba gaba wurin taimakon Nigeria, kasan da mu da Niger jiya jiya wasu kasashe suka rabamu,wato asalin daya ne ,shiyasa duk abunda yasa me mu to kamar su yasama.

Misra Egypt: -alokacin da makircin kasashen yamma ya kewa Nigeria, kawai sai Shugaba Gowon yatura sako Misara yace:na nemi taimakon kasashe da yawa amma basu taimake ni ba sai kasar Rashace ta ban jiragen yaki amma banda kwararrun matukan sa,kuma Ojukwu yafara kai hare haren jiragen sama kuma zai iya nasara,kuma nasan misra tana cikin matsala saboda yakin da take da Israel,Munaso Don Allah Jamal Abdunnasir koda abokan kane ka musu magana,kamar su Algeria su taimake mu.

Jamal Abdunnasir yakabar kiran Nigeria dukda yana cikin yaki saboda: yace: yafahimci anaso akafa wata sabuwar Israela a Afurka kamar yadda aka kafa akasashen Larabawa,yaga yadda Israela ke taimakon Ojukwu da makamai,hadin kan Nigeria shine yafi saboda idan tarabu sauran kasashen Afurka kowa zai fara tunanin haka.

daganan yabada matukan jiragen sama suka fara korar jiragen Ojukwu kasa tacika da murna, suna share ma sojan Nigeria hanya su kuma suna kutsawa,daganan har suka kai hari inda jiragen Ojukwu ke tashi, daganan aka karya karfin shi na sama gaba daya.
Nigeria bazata manta da misra ba da shugaban ta Jamal Abudun Nasir.

wanene ke bayan kanu ayau? saboda me dan Afurka bai amafana da arzikin shi? saboda me dan Afurka da mai mulki da talakka yake jin magana wasu kasashe koda kasar shi xata rushe ne?
shin raba kasa shine mafi kyau ayanzu ko ko Adalci da tsarin mulkin zaayi da gyarawa?0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia