Adam A Zango: Musifar Dake Cikin Kannywood Ta Wuce Misali !

Adam A Zango: Musifar Dake Cikin Kannywood Ta Wuce Misali

Adam A. Zango: Masifar da ke cikin Kannywood ta wuce misali!


Daga Mujallar Fim

A cikin wata budaddiyar wasika da jarumin wasan kwaikwayon kuma mawaki Mai shirya finafinai, Adam A. Zango ya bayyana cewa, "Ni ba dan daudu ba ne, kuma ni ba dan maula ba ne. Sannan ni ba mushiriki ba ne, kuma ba ni da malami ko matsafi."

Ya kara da cewa, "Ni da Allah kadai na dogara. Idan kuma akwai malamin da ya ce na taba zuwa wajensa ko kuma wanda ya taba ba ni kudi kyauta ba tare da na yi masa aikin komai ba to, don girman Allah kada ya rufa min asiri. Tun daga kan 'yan siyasa, sarakuna, gwamnati, ko masu kudi, ko 'yam mata.

Ya ce, "Duk abinda da na mallaka a rayuwata gumi na ne ya bani, ba dan Adam ba. Motar hawa, gida ko fili...Don haka babu wanda ya isa ya sani in yi abin da ban yi niyya ba tunda babu wanda ya taya ni kare mutuncin daukaka ta.

DON HAKA TA HANYA DAYA KADAI ZAKU IYA DAKATAR DA DAUKAKATA...... HANYAR ITA CE KU DAKATAR DA NUMFASHINA, SAI DAI KUMA KASH HAKAN BA A HANNUNKU YA KE BA.... HABA KU YI TA YAWO DA NI KUNA BATA MIN SUNA DON KAWAI ALLAH YA FIFITA NI A KAN KU.

"Kun ce min arne, kun ce min gara, kun ce min fasiki, kun ce min mai girman kai. Amma duk da haka masoyana ba su guje ni ba, ba su daina sayen finafinai da wakokina ba.

"Haba don Allah, mai na yi muku duk wanda na taimaka a rayuwata sai ya dawo yana yaka ta!! To, na kai bango! Billahillazi la'ilaha illahuwa, duk wanda ya kara kara taba ni sai na tona masa asiri.

Sannan duk wanda ya rufa min asiri a kan abubuwan da na lissafa Allah ya tona masa nasa. Ban kira sunan kowa ba a yanzu amma nan gaba zan kira sunan ko waye idan ya kara bata min suna. Ina da ýaýa ya zama dole in fara kare mutuncina da martaba ta kafin ya shafe su. Don Allah kadai ya san gawar fari. Sannan zan ja tunga da mabiyana na Kannywood, don a haka ne kadai za a bambance tsakanin aya da tsakuwa.

Masoyana, ku gafarce ni akan abubuwan da na rubuta, an kure ni ne.

Yadda a ko'ina ake samun nagari da bata gari,  haka zalika a cikin akwai nagari da bata gari, kuma wallahi billahi daga yau ba za a kara yi min kazafi in yi shiru ba, don kowa a cikin mu ya san kowa. Shi ya sa idan aka ce mana jahilai ba na damuwa yanzu, domin nima na gano hakan. Tunda an ce amfanin ilimi aiki da shi.

Masifar da masana'antar Kannywood take ciki ya wuce misali. Saboda zalunci, fasikanci, riya, aikin ganin ido, da kuma cin amana da ake aikatawa karara. Amma daga an yi magana sai mu ce matan cikin mu ne suke janyo mana.

Wallahi matan mu ba su da laifi, domin addini bai taba bai wa mace damar zama babu mai kula da ita ba. Amna a Kannywood fim daya yarinya ko yaro za su yi sai ka ga sun bude kamfanin kan su har ma su rinka daukar sababbin 'yan wasa.

Babu tone tone domin da dama sun san inda na dosa.
Don haka mu daina jin haushin zagin da wasu  al'umma suke mana!! Mu karbi laifukan mu mu gyara wata kila nan gaba kadan su yi alfahari da mu.

Duk abin da na rubuta idan akwai karya a ciki wani ya fito ya karyata ni, ko kuma a kore ni.

Zan ci gaba...

DUK WADDA DA TA CE SAI NA NEME TA KAFIN IN SAKA TA A FIM TA FITO GIDAN TV KO REDIYO TA FADA WA DUNIYA. IDAN KUMA TA RUFA MIN ASIRI ALLAH YA TONA MATA NATA ASIRIN.

*Madogara-Mujallar Fim

Mun Samo Ne Daga Shafin Jari dar ® Zuma Times Hausa


HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia