An Zargi Yan Kungiyar Biafra IPOB Da Yunkurin Shigo Da Makamai 2,671 Nigeria

An Zargi Yan Kungiyar Biafra IPOB Da Yunkurin Shigo Da Makamai 2,671 Nigeria

An Zargi Kungiyar IPOB Da Yunkurin Shigo Da Makamai 2,671 Cikin Nijeriya 


Daga Habu Dan Sarki

Gwamnatin Tarayya ta zargi haramtacciyar kungiyar nan ta masu fafutukar kafa kasar Biyafara wato IPOB da hannu cikin kokarin shigo da muggan makamai cikin kasar nan.

An bayyana wannan zargi ne yayin wani zama da wata babbar kotu ta gudanar a Abuja domin sauraron karar da kungiyar IPOB ta shigar tana kalubalantar matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na haramta ayyukan kungiyar, bisa zargin ayyukan ta'addanci da cin amanar kasa.

Lauyan da ya wakilci bangaren gwamnati ya yi kokarin kafa hujjoji da wasu kamen makamai da hukumar kwastam ta kasa ta yi na wasu makamai da aka yi kokarin shigowa da su kasar nan, wadanda aka gano suna da alaka da madugun kungiyar 'yan aware Nnamdi Kanu.

Ana zargin makaman suna da nasaba da wani dan kasar Turkiyya Abdulkadir Erkahman wanda ke nuna goyon baya ga yunkurin kafa kasar Biyafara, sakamakon wasu hujjoji da jami'an tsaro na asiri suka tattara.

Kungiyar IPOB dai na jayayya da matakin gwamnati na haramta ayyukan ta da sanyata a matsayin 'yar ta'adda.

©Zuma Times Hausa

Biafra IPOB leader

General Tukur Yusuf Buratai


HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia