Mawaki Nazeer M Saulawa Ne Gwarzon Mawakin Shekara Na Airtel Nigeria

Nazeer M Saulawa

Mawaki Nazeer M Saulawa Ne Gwarzon Mawakin Shekara Na Airtel Nigeria

Mawaki Nazeer M Saulawa fitaccen Matashin mawaki ne dan asalin jahar Gombe wanda ya shahara kuma yayi fice a fagen wakokin Hausa na zamani duk da karancin shekarun da yake dasu

Kuma yana sahun gaba a mawakan Hausa da suka fara daura wakokin su a yanar gizo gizo a arewacin Nijeriya tun shekaru da dama

Inda Matashin mawakin yafi maida hankali a kan rera wakokin Soyayya na zamani, da kuma wakoki na fadakarwa

Inda kuma a yan shekarun nan yayi nasarar gina Studio na kansa inda yasa masa suna Hubbi Studio

Wadan Nan Sune kadan daga cikin wakokin da mawakin ya rera

- Nafisa Gimbiya
- Muradin Raina
- Zama Da Kishiya
- Karfafamin Zuciya
- Rahama
- Sirrina

Dadai Sauran Su

A madadin ma'aikatan wannan shafi, muna taya wannan Mawaki murna, kuma muna yi masa fatan Alkhairi


HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia