Ƴan majalisar dokokin jihar Benue 8 sun yi yunkurin tsige Gwamna Ortom

Rikicin majalisar dokokin jihar Benue ya dauki wani sabon salo a ranar Litinin bayan da wasu mambobin majalisar 8 dake jam’iyar APC suka mikawa gwamnan jihar takardar yunkurin tsige shi.

Ortom ya fice daga jam’iyar APC ya zuwa jam’iyar PDP kwanaki biyar da suka wuce.

Terkimbi Ikyange tsohon shugaban majalisar da aka sauke a makon da ya gabata shine ake zargi da shirya yunkurin tsige gwamnan.

Sauran yan majalisar dake adawa da Ortom sun hada da Adanyi Benjamin, Terhemba Chabo, Benjamin Nungwa, Bem Mngutyo, Adams Okloho, James Okefe da kuma Nick Eworo.
Wata majiya ta shedawa jaridar The Cable cewa Ikyange da sauran yan majalisar sun shiga harabar majalisar da karfin tsiya tare da rakiyar jami’an ƴansanda.

Daga bisani Ikyange ya fadawa yan jaridu cewa sun bawa gwamnan mako guda da ya amsa dukkanin tuhume-tuhume da suke masa.

Source: https://ift.tt/2vhRbqR

Leave A Reply

Your email address will not be published.