Abubuwan Dasu Kamata Ko Wanne Dan Arewa Ya Sani Game Da Yakin Biafra !

Abubuwan Dasu Kamata Ko Wanne Dan Arewa Ya Sani Game Da Yakin Biafra,Kashi Na Farko !

Daga : Hamisu Hassan Ahmed

Yakin Biafra Yakinda yai sanadiyar mutuwar mutum fiye da miliyan daya.

wani lokaci rashin tunani da hangen nesa da kuma wata kiyaiya da mutum yasama kan shi, kan iya sa Yan sanadiyar halakar yan uwan sa da sauran jamaa.

Yaki baitaba zama mafitaba inda mutane zasubar zaluntar kan su,kuma suka dau hanyar yin sulhu.

idan muka tambayi dalilin da yasa wannan gumurzu yafaru zamuji anace mana:-bambancin Addini, Ala’da,kabila, harshe.

-kisan su Sir Sardauna da Sir Tafawa Balewa, wanda kbilar inyamurai sukayi ajuyin mulkin 1966,abun da yasa yan Arewa suke neman fansa.

-juyin mulkin da yan Arewa suka jagoranta suka kashe Ironsi,shima ya ruruta karin kiyaiya tsakanin Inyamurai da Hausa Fulani.

-kisan inyamurai da hausawa sukayi bayan yan Arewa sun kwace mulki dayin Hijirar daruruwa zuwa asalin su wato kudu.

-magudin zabe na yan majalisu da kabilar Igbo suke ga yan Arewa sunyi.
wannan cin amana ta kisan su Sardauna,da kuma mummunar ramuwar gayya data faru daga kowane bangare, to suna cikin abunda ya haifar da yakin da yajawo zubar da jini awannan kasa daga baya.

ammma babban abunda yajawo yakin alokacin da yafaru shi ne: -arzikin petur da bangaren Inyamurai keda shi,wanda suke ganin bazai yuyu arika amfani da shi domin gina Arewa ba,wata kila amanta da su.

-suna ganin yan Arewa sune suka kama mafi yawancin madafun iko,har suna ganin kamar anmaida su saniyar ware, kuma suna ganin wannan yasaba ma tsarin Federation daakace anayi.

-manufofin kasashen turai irin su France da sauran su,wanda sune sukaima sojojin Biafara Trainin akasar Gabon, domin su raba arzikin Petur da su, in sunyi nasara.zamu ga yanda france tayi nan gaba da shugaban ta( De Gaulle.) bari mushiga lokacinda aka fara tawaye da gmurmuzu.

-Ojukwu da zaratan shi sun fara barazanar rabewa daga Nigeria awatan Maris a shekara ta 1967.

-domin agujema yaki hakan yasanya Shugaban kasa Gawon da Shugaban tawaye sunje kasar Ghana domin yin sulhu, alokacin da zamuga Ojukwu yanacewa:dole akoma tsarin Confedaration,wato wanda zaifi ba kowane bangare yancin sa. hakan yanuna Ojukwu bai bukatar aiki sulhu.

-30 ga watan mayu 1967 Ojukwu yasanarda yancin kasar Biyafara,suka mallake duk wurare na hukuma,kuma suka nemi duk kamfanoni masu hakkar Petur da su mika kudi zuwaga sabuwar kasar su.

akashi na 2 zamuga: Mai Nigeria tayi?wane kasashe ne suka taimaki Nigeria? suwaye Suka jagoranci kifarda Gwamnatin wasa ta Ojukwu? saboda me Ingila ta karfafa Nigeria saboda me irin su france suka karfafa Biyafara?shin kasashen Larabawa sun taimake mu?saboda me wasu kasashen Afurka suka karfafa Biafara?sabome aka kasa samun wanda zai hada kan Nigeria har yanzu?akwai lokacin da Afurka zata iya tafida yan kasar ta ba sai an nuna karfi da yaki ba?

insha Allah duk wannan zaizo anan gaba.

muna karanta Tarihi ne don kar mu rika maimata kuskure,sanan muna karanta shi don mui koyi da abunda yafi kyu.

® www.HausaMedia.Com

Leave A Reply

Your email address will not be published.