Al-makura ya sallami kwamishinoni 9

Gwamnan jihar Nasarawa, Umar Tanlo Al-makura a jiya ya sauke kwamishinoni 9 da kuma masu bashi shawara biyu daga kan mukaminsu.

Sakataren gwamnatin jihar, Muhammad Abdullahi shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Lafia babban birnin jihar.

Abdullahi ya ce gwamnan ya gudanar da garambawul din ne a majalisar zartarwar jihar domin bawa mutanen da aka sauke damar mayar da hankalinsu kan burikansu na siyasa da suka sanya a gaba da kuma sauran burikansu na rayuwa.

Sanarwar ta lissafa kwamishinonin da abin ya shafa da suka hada da Abdulhamid Kwarra, na ma’aikatar muhalli da ma’adanai Gabriel Akaka na ma’aikatar Ruwa da Cigaban Karkara da kuma Uwargida Mary Enwongulu kwamishiniyar al’amuran mata da cigaba jama’a.

Sauran wadanda abin ya shafa sun hada da Bamaiyi; Dr Daniel Iya; Yusuf Shehu Usman, Sonny Agassi, Mohammed Yahaya,Tanko Zubair.

Source: https://ift.tt/2AlYSlE

Leave A Reply

Your email address will not be published.