Al’ajabi Part 2 Hausa Novel

Al'ajabi Part 2 Hausa Novel

***** AL’AJABI PART 2*****

MUM ta dade tana kallona cikin takaici jim kadan tace ” Me tayi miki kika mareta??” Na koma kan kujera na zauna nace ” zuwa… tayi ta giftani ina kallo ta kare min ban gani ba kuma tambayarta tayi min shiru.” ta kada kai tace ” lallai humaira rashin mutuncin naki yakai, kawai daga na kirata ta gifta ta gabanki shine abin duka??” Na zunburo baki nace mum ” kare min fa tayi kuma…….” Ta katse ni da cewa ” ke dalla can rufa mana baki kice kawai wulakancinki ya motsa to kin daketa kinji dadi, idan kinfi karfinta ai akwai Allah.” Ta nufi inda hanne ke zaune har yanzu bata tashi ba sai kuka da take yi. Na dan kara bata rai tare da gyara zama nace ” ni mum wlh bakya yimin adalci a komai ba zaki taba goyon bayana ba kullum nice me laifi a wurinki akan wadannan banzayen.” Nakai karshen maganar da kauda kai. Mum tace ” anki a goya miki bayan wace gsky gareki?? Ke ko kunya baki ji ba don Allah?? ki rasa wacce zaki zage kwanjinki akanta sai yar aikin gdnku wadanda yakamata ace kin jasu a jikinki ki nuna musu kauna.” Na kalli hanne na zabga mata harara nace ” wadannan shashashan matsiyatan zanja a jikina?? Allah ya kiyaye. Mum tace ” to tunda ba zaki kyalesu susha iska ba ba ruwanki dasu basu shiga rayuwarki ba kada ki kara shiga tasu idan kuma kika ku wlh zan basu dama idan kika dakesu su rama suyi miki dan banzan duka ai ba karfinsu kika fi ba. Taja hannunta suka wuce, nabi mum da kallon mamakin jin abinda ita kanta tasan bazai yiwu ba, nace ” Su dakeni fa kika ce?? ” Ta juyo da sauri tace ” Eh don ubanki “.

 Nabita da kallo ganin abin ya dau zafi da yawa ta juya suka bar falon da nake a zaune. Na gyara zama na hade rai nayi kicin-kicin kamar na fashe da kuka, wai ni ake zagi akan wannan banzar yar aikin? lallai zamanta yazo karshe a gidan nan bari dady ya dawo. BAYAN AWA DAYA naji motsin dawowar dadyna na kakalo sabon fushi da takaici, dady yana shigowa yayi ido hudu dani cikin fushi, yayi saurin ajiye jakarsa tare da tunkaro inda nake zaune ” my daughter ( daya daga cikin sunayen da yake kirana dasu ) menene ya faru haka? waye ya taba min ke?” Nayi shiru na kara hade rai kawai na juyar da kaina. Dady ya zauna gaf dani cikin kasa-kasa da murya yace ” fada min mana waye ya taba ki? uhummm?” Cikin shagwaba na mirgina kai nace ” ba mum bace…….” Me kuma tayi miki?? Ya tambaya da sauri. nace ” wai….. zata sa yan aiki su rinka dukana ” dady har wani dan babban motsi yayi tare da mai- maita abinda na fada ” su dakeki??”. na gyada kai. Ya juya da sauri ya fara kwallawa mum kira. Hajiya!!!!! Hajiya!!!!! Da saurinta ta fito izuwa falon da faddady yace ” Me yasa kika batawa humaira rai, wai ke hajiya me yasa kike haka ne don Allah…. to to yanzu me kike nufi yar aiki tafi yar da kika haifa da cikinki kenan??” Mum ta tabe baki tace ” au wai da akan wannan ne kake kwala min kira haka sai kace wani tashin hankali??” Au kina nufin shi wannan ba komai bane kenan?? kinga hajiya ran kowa zai baci a gidan nan fa.

Mum tace ” rainin nata ne yayi yawa nace zansa a dai daita mata zama. Na tsandara ihu nace kaji ko dady?? Dady ya kara rudewa ya fara zabga bala’i ta inda ya shiga batanan yake shiga ba. Zuwa can nace ” dady kawai a kori yan aikin nan dukansu “. dady ya juyo yace ” kwantar da hankalinki, abinda za’ai kenan suna ina ne??” Mum tace ” Wai suwa za’a kora?? bazai yiwu ba sbd duk cikinku ba wadda kuka dauka kuma baku kuke biyansu ba nice don haka babu me korar minsu ina jin dadin aiki dasu…… Munji tafi kici gaba da harkokinki kada ranmu ya baci duka, Allah ya baka hakuri. Ta juya ta nufi sashinta, dady ya juyo gareni ya fara rarrashina ni kuwa sai wani kara hade rai nake. Kinga manta dasu kinji humaira na, ba wanda ya isa ya taba ki duk wanda ya kara bata miki rai wlh tamuce ni dashi. Kada ki manta fa gobe iwar haka kina kasar birtaniya kin bar musu kucakar kasar tasu zaki fara rayuwa cikin turawa ba wanda zai takura miki inda iskar da zaki shaka ma ba irin wannan bace. Jin hakan da nayi yasa nadan saki raina kadan, yace ” to danyi murmushi mana ” Na saki rai sosai yace ” Yauwa ko ke fa! gobe kiyi kokari ki tashi da wuri sbd jirginki na safe ne an gama duk wasu shirye-shirye kina zuwa direct zaku daga shuuuuu!!! sai london.” yakai maganar da murmushi. Na dan tabe baki cikin shagwaba nace ” dady nifa dakai zamu tafi idan muka je sai ka dawo.” Ya dubeni yace ” to ke banda abinki ina naga lokacin binki har london kuma na dawo?

 kedai karki damu jirgin na musamman ne zaki samu duk abinda kike bukata kuma za’a kula daku sosai musamman ma ke yar lele. Nayi murmushi kawai. Daddy ya mike ya dau jakarsa bari na shiga ciki ko? “To dady” Na fada idona na kasa ya wuce. Na daga kaina na dubi katafaren agogon dake manne a jikin bango karfe 6:15pm sallar magaribar ma ai da saura na mayar da kaina ga t.v din naci gaba da kallo. $$$$$$$$$$$$ in Alhaji lfy irin wanWashe gari misalin karfe 8:00am na safe zaune muke mu uku, mum da dady na zaune a kujeru daf da juna yayinda nake zaune a kujerar dake fuskantarsu. faffadan tebirine a gabanmu kayan abinci kala- kala jere bisa kansa wadanda suka dace da karin safe, babu wanda ke magana a cikinmu. Humaira!!!!!!!!!!!!! dady ya kira sunana, na dago a hankali na dubeshi. yace ” misalin 11:30 na safen nan zaku tashi, abinda nake so dake shine kibi a hankali kuma ki kula sosai sbd kasar da zaki je ba taki bace ba wadda kike ciki bace kuma ba wadda kika saba da ita bace, kiyi abinda yakai ki kawai shine karatu ki samo abinda zanyi alfahari dashi sbd ina da comfidence 100% akanki kuma ba zaki bani ba.

 Insha-Allahu dady. Na fada tare da mayar da kaina ga kofin tea dake hannuna. Daddy ya mike yace ” bari inje na shirya na fita ina da meeting karfe tara hajiya ina takardun nan dana baki ajiyansu jiya?? Ta dago kai a karon farko tace ” Suna nan cikin lokar sama.” Ok ” ya fada tare da dubana yace ” yar lele na Allah ya kiyaye hanya, da zarar kun sauka zanyo miki waya.” To dady na fada ya juya nudi dakinsa. Na mike na koma kan kujerar dake gaf da mum nace ” Momina banji kince komai ba.” To me zance??? Ta fada kanta na duban abinda take ci. Nace yakamata kice wani abu saboda kinga tafiya zanyi ta shekaru da yawa kodai bakin cikin rabuwa dani kike yi da yawa haka har ya hana ki magana??” A’A ta fada tare da cewa ” nifa haushinki kawai nake ji ” Na bita da kallo lokaci guda nayi yar gajeriyar dariya nace ” da gaske??” ta gyada kai kawai. Na kwantar da kaina a jikinta nace ” sorry my mum ai nasan da wasa kike ba zaki taba jin haushi na ba, uhmm! mum pls sarkar nan don Allah ki bani zanyi amfani da ita acan. Ta girgiza kai tace ” kefa kika nuna halin ko in kula da ita sai yanzu zaki ce kina so??” Mum dama can ina sonta wlh zan kula da ita, Zaki bani?? nakai karshen maganar da kwantar da murya. Mum ta dubeni kadan ta kauda kai tace ” Zan baki “.

Na saki fuska hade da alamar jinjina nace ” Thank you MUM bari naje na fara shiri. ” Na nufi dakina. Misalin karfe goma 10:00am mufida tazo kawowa momi sako ta iske ina gaf da gama shirina ta tayani muka karasa na tilasta mata ta tsaya don yimin rakiya izuwa airport. MUFIDA y’a ce a wurin haj. jameela kawar mum kuma aminiyarta, mufida ce kadai zan iya cewa kawata a duniya don da ita kawai na yarda muyi kawance sbd ta wasu bangarorin halinmu yazo daya duk da muna da banbanci da ita sosai a wasu bangarorin. Misalin karfe 10:15am Nayi sallama da momi da sauran wadanda zan iya sallama dasu sauran yan aikin gidanmu kuwa da rashin mutunci muka rabu don ban hakura ba sai da nayi final. A jibgegiyar mota kirar PRADO muka fito, mufida na gefena sai kuma mutum biyu har direba dake gaba. Mukanyi hira jefi-jefi da mufida, kaina sai wani kumbura yake waini zani kasar turai. Cikin kankanin lokaci muka isa AMINU KANO international airport, tunda naga jirgin dazai daga damu na yarda bana yara bane saboda haduwarsa, ya isa a nunashi a ko’ina. Ban dauki lokaci ba aka gama tantanceni na juyo na karbi jakunkuna na mukai sallama da mufida..

 Shigata jirgin ya tabbatar min da abinda dadyna ya fada, tsaruwarsa daga ciki yafi yadda nake ganinsa daga waje domin ya wuce duk yadda nake tsammani. kai tsaye sit dina na wuce na zauna duk da cewa yaune karon farko dana shiga jirgi irin wannan amma ban yarda na nuna hakan ba don kada wadanda ke cikin jirgin su raina ni. Abinda na lura dashi shine kowa naji da kansa a cikin jirgin sbd daga manyan attajirai masu tafiya kasuwanci sai yayan attajirai masu zuwa karatu irina, babu ma zaton samun dan talaka a ciki bare a samu din. Kamar yadda aka shirya 11:00am dai dai jirgin ya daga kai tsaye izuwa birnin london tafiya mafi tsawo dana fara yi a rayuwata, jami‘an cikin jirgin kuwa sai nan nan ake damu duk abinda muka bukata ba bata lkc ake bamu. Awanni nata shudewa 2n ina sha‘awar tafiyar har sai dana gaji amma bamu iso ba, duk na kosa sbd wannan ne karon farko dana taba yin tafiya irin wannan daga karshe madai wani nannauyan barci ne ya kwashe ni ban farka ba sai AIRPORT na birnin londôn, A hankali daya bayan daya muka sakko daga cikin jirgin. wowwww!!!

 Nan fa naga abin mamaki domin ba birnin ba airport din kadai abin kallo ne ban taba tsammanin akwai wuri me kyau da kawatuwa irin wannan lallai duk yadda ake bada lbrn birnin nan ya wuce nan, duk yadda nakai da ji da kai sai dana zama kamar wata yar kauye a wurin. saukowarmu keda wuya jami‘an filin jirgin suka yo kanmu nan fa aka shiga secreening kala-kala harda wanda ban taba ji ba ko a lbr, bayan na cika duk wani sharadine aka bani damar ficewa daga airport din, ban jima ba kuwa wata jibgegiyar mota me matukar fadi da tsawo ta iso like take da banner din OXFORD UNIVERSITY bamu dauki tsawon lokaci ba ta debemu tare da mutane daban-daban da muka zo daga wurare da kasashe maban-banta, Anan ne fa naji kwalta tamkar ita ta shimfida kanta, duk inda motar tabi titine luwai- luwai ba gargada bare rami. Shuuuuuuu!!!!!

A haka motar ke tafiya tamkar jirgin sama ban-bancin kawai ita wannan a kasa take tafiya ba‘a sama ba. Gefe guda tsarin gine-ginen birnin wanda keda matukar tsayi tamkar zasu tabo can kololuwar sama sun kawatar dani matuka. gashi kowa irin rayuwar da nafi so yake yi ta ba ruwan kowa da wani, kowa ka gani harkar gabansa yakeyi. jim kadan muka iso katafariyar jami‘ar daya daga cikin mafi girma, daukaka da suna a duniya, bayan komai ya kammalu kuma kai tsaye aka yimin jagora izuwa masaukina. Ni kadai ce a sashin nawa wanda ya kunshi duk abubuwan da nake bukata.

 Nan fa na shiga karatu gadan-gadan kasancewarsa wajene da ko baka so sai kayi karatu, da farko na dauka a nigeria ne naci gaba da jiji dakai da takama sai naga ina!! domin a banza wajene da kowa keji da duk abinda nake ji dashi shima. Dole tasa na sakko na fara maraba da kowa nan da nan kuwa na tara kawaye masu yawan gaske tamkar bani ba, na saki jiki da mutane sosai. Da yake ba karatu ne irinna na nigeria ba cikin shekaru biyu kacal na kammala degree na na farko a hakan ma don mun sami dan tsaiko ina daya daga cikin wadanda suka sami sakamako me kyan gaske hakan yasa makarantar ta bani damar yin masters degree kyauta kasancewar ina jin dadin zaman yasa na amince na zarce cikin ba tare da jinkiri ba. shekara daya kuma na kammala masters, degree biyu cikin shekaru uku kacal, wannan shine tarihin kara2na da yadda na samu masters degree a kasar birtaniya. “hmmm….. Lallai gskyr Bahaushe da yace ‘Talaka bawan Allah‘ domin talakan nigeria ne zai kwashe shekaru hudu yana neman diplomer bai samu ba“ Ahmad ya fada sanda ya kauda kansa daga kan littafin lkc guda ya mayar da kansa ya dora. kammaluwar komai tasa na tattaro inawa-inawa nayo nigeria, ranar laraba misalin 12:00pm jirginmu yayo nigeria. dirarmu keda wuya dady ya iso tare da wasu daga cikin yaransa aka daukeni direct mukai gida, nan fa girman kai, takama, gadara da raina mutane ya dawo sabo fil. Na fara jin nifa yanzu nafi kowa kuma samun kamar ni sai an tona kai zaiyi wuya ma a samu mace kamar ni da tattara abubuwan da nake dasu….

Hmmm’un yanxu akapara shirin..!

Bayan kwanaki uku da dawowata ina kwance bisa doguwar kujera hannuna na rike da wani novel daya daga cikin abokan hirata a london me suna HAPPINESS DAY na prof. christiana wolein dan kasar holland, kyakykyawar fuskata nakan littafin wanda fararen idanuna ke kallo, hankalina, tunani da duk wani nazarina ya tafi ga karanta daddadan lbrn da nake yi wanda nake matukar son karasas ko don naji yadda karashen lbrn zai kasance. Magribar da nake ganin ta doso yasa na kara kaimi, Momi ta fito daga sashinta rike da wani da madai-daicin kaskon turare wanda wani daddadan kamshi ke tashi ta hanyar farin hayakin dake fita daga kaskon, ta fara zagaye faffadan falon domin kanshin ya isa ko‘ina kafin ta dawo ta ajiye shi a tsakiyar falon.

A dai-dai lkcnne dady na ya dawo, cikin fara‘a ya sallama kasancewar ya ganni a falon, ya karasa y aje jakarsa tare da zama. Kamar hadin baki nida momi muka amsa sallamar, na dago daga kwanciyar da nayi tare da aje novel din a gefena nace “Wellcome back my dady“. Yauwa yar lele na da fatan dai komai normal ko? na gyada kai kawai, momi dake gefe ta bimu da kallo tare da jinjina kai tace “uhm.. gsky ina gani kabilanci a gidannan, wato Alhaji yarka kawai ka sani ni ba mu2m bace??“ Daddy ya kyalkyale da dariya yace “kinji ki hajiya da wani zance gani kik na tashi daga nan bance miki komai ba??“ Da sauri tace “zaka iya don ba karamin aikinka bane kace bama ka ganni ba 2nda ka shigo sai da nayi magana.“ Dady ya sake yin dariya yace “ A haba sai kace wani makaho? kawai dai……..“

 Y‘arka ce a ranka!! momi ta karasa masa zancen. ya gyada kai yace “anji muje a hakan“. Momi tace “gashi kuma duk daran dadewa sai ka shigo falon nan ka tarar batanan koka manta macece dole ka aurar da ita??“ Dady yayi murmushi yace “kinga hajiya duk takaicinki kyayi ki gama ai ba akuya bace ita bare kice zan kaita kasuwa na siyar mun rabu kenan har abada.“ Duk muka fashe da dariya, dady ya kwantar da kansa jikin kujerar yace “ yauwa ni na tuna ma, humaira!! Na dago kaina a nitse domin nasan indai dady ya kira sunana kai tsaye to maganar da yake son yimin me muhimmanci ce. Yace “kasancewar kinyi kara2 me tsada a wuri m tsada kuma akan abu me tsadan gaske izuwa yanzu na sami request daga wurare daban-daban akan anaso ayi aiki dake, daga ciki akwai central ban.k da me gwamnan bankin da kansa ya rubut min takarda akan cewa suna bukatar karin kwararru da suke da sani akan tattalin arziki, akw FIRST BANK, GTI BANK, DIAMOND BANK da sauransu. Ma‘aikatar kudi ta tarayya ma na bukatar kiyi aiki dasu, sannan jami‘o‘i kamar B.U.K, A.B.U da sauransu na bukatar kiyi musu aiki a matsayin lecturer, ke harda wasu hukumomi daga kasashe waje sai kin zaba kin darje. A maimakon nayi farin ciki sai na hade rai, dady y dubeni tare da gyara zama yace “Ah ya naga kin bata rai?? lafiya??“ Na dan kumburo baki nace “dady nifa bazanyi wa aiki a duk wuraren nan ba.“ dady yace “sai a ina?? ko a bankin duniya kike s kiyi aiki??“ Na girgiza kai nace “ A‘A ni bazanyi a ko‘ina ba.“ Kafin yace wani abu momi tace “ba zakiyi ba kina nufin duk kara2n da kikai ya tashi a banza kenan??“ Dady ya dubeta yace “haba hajiya kibita a hankali mana, ya juyo gareni yace “Yar lelena me yasa bakison kiyi aiki??“ Nace dady nifa banyi kara2 don na wahalar da kaina ba, nawa ne duka albashin da za‘a biyani? duka fa bai kai kudin da gyaran gashi na keci ba. Yayan talakawa da matsiyata sune keyin kara2 do su sami aiki amma ba irina ba.“ Daddy ya kyalkyale da dariya kamar zai tuntsiro daga kan kujerar yace “gskyrki fa y‘ata.“ Momi tace “ Au wai kaima ka biye mata a hakan? Daddy yace “To karya tayi??, ya juyo gareni yace yanzu ke me kike so ayi??“

Na tabe baki kamar ba zance komabi ba daga bisani nace “ daddy nifa a duniya ba abinda ban iya ba irin kwamfuta don haka ina son na samu certificate akanta. Cikin sauri daddy yace “Tooo!!! a germany ko japan ko america zabi daya…… Na tabe baki nace “NO daddy duk basai ankai ga haka ba, anan kano nake so nayi.“ Daddy yabini da kallo yace “kina nufin a makarantar matsiyata??“ Dariya ta kwace min na girgiza kai nace “ a‘a akwai wata reshen AL- KHRAMY ta kasar saudiya da suka bude anan kan next week za‘a fara lecture, MUFIDA ma can zata fara zuwa kaga na sami abokiyar tafiya.“ Daddy ya gyara zamansa yace “kwarai naji lbrnta, to karki damu my daughter a ckn satin nan za‘a shirya miki komai next week dake za‘a budeta.“ Nayi murmushi nace “Thank you my dad“. Daddy ya mike “bari in karasa ciki, ya juyo ga momi yace “a ina kika saka min jakar nan ta jiya??“ Har yanzu takaicine akan fuskarta tace “ tana nan cikin lokar dakinka“. daddy ya sabi jakarsa ya wuce. Ni kuwa wani farin ciki ya lullubeni, gsky daddy na sona ni kaina nasan hak Hararar da momi keyi min ce tasa ban takalo wat hira da ita ba na jawo novel dina tare da kwanciy bisa luntsimemiyar kujerar da nake kai na cgb da kara2n da nakeyi a baya.

Sati daya dai-dai da faruwar haka na fara zuwa lecture a katafariyar makarantar AL-KHRAMY computer training school, 2n daga sanda na hang makarantar a shigata ta farko naji a raina tayi min sbd tsarinta. fasalin gininta kawai abin kallo ne banda kuma zubin cikinta. Tana da ma2kar fadi da girma da kuma wadatar dakunan kara2, akwai bangaren da aka ware musamman don hutawa a lkcn da ba‘a lacca wanda ya kunshi kujeru a jere daf da wasu kyawawan bishiyu da kuma filawowi dalilin da yas iskar dake kadawa a wajen ta zama me kamshi, wajen dai ya dace da hutawa ga wanda ya debo gajiyar kara2. Gefe guda akwai daki na musamman da aka ware aka cikashi da littattafai kala-kala da suka shafi darasin computer da mutum zai iya zuwa ya bincika wanda yake so, nesa kadan kuma akwai wurin cin abinci da aka ware musamman ga mas bukata. Da yake makarantar mallakar larabawa ce an war bangaren maza daban na mata daban. Ga yadda ake kaffa da dalibai ake maidasu y‘an gata. kamar yadda aka saba ranar juma‘a 12:00pm mu tashi zaune nake bisa wani dan dandamali ina jira mufida ta fito mu tafi kaina na kasa na kurawa laptop din dake bisa cinyoyina ido ina tayi, sallamar da naji anyi ce tasani dakatawa kamar n dago kai na dubi wanda yayi sallamar sbd muryar tasa ta ratsani sosai amma sai girman kan ya motsa na cgb da abinda nakeyi ko sallamar ban amsa ba. Kyakykyawan saurayin bai gajiya ba yace “ pls na gaji da tsayuwa in zauna??“ Na cilla idona tare dago fuskata nace “ka zauna mana idan ka gadama“. Mai makon ya bata rai sai yayi murmushi yace “godiya nake.“ Ya zauna bisa dandamalin nesa kadan dani, kaina na kasa amma zuciyata na sake-sake, ji nake kamar na dago kalli mu2min daya fara birgeni kar na farko a rayuwata. Jim kadan mufida ta fito ai kuwa tana kyalla ido taga wannan saurayin dake kusa dani sai ta bude baki tare da fadin “ Ah leader manyan gari kaine anan haka??“

Yayi murmushin daya kara masa kyau yace “nine wlh kinga su nazir nake jira basu fito ba dama tar kuke da wannan??“ yayi nuni dani. Eh tare muke da ita wlh ni take jira…… Na rufe laptop dina tare da diban littattafaina dake ajiye a gefena na doka tsaki na wuce nabarsu anan.“ mufida tabini da kallo kawai ta juya tare da yin murmushi tace “sai gobe ko??“ Ya gyada kai kawai dai-dai lokacinne abokansa s uku suka karaso wanda ya riga kowa karasowar yace “kai wai ya akai harka 2nkari wccn yarinyar t barka ka zauna kusa da ita??“ Ya bishi da kallo yace “kasanta ne??“ Kwarai kuwa shugaban y‘an girman kai, takama d gadara ta duniya kenan.“ duk sukai dariya, saurayin ya shafi gashin kansa yace “kai! nazir yarinyar fa ba karya wlh ta hadu“, wanda aka kira da nazir din yace “ ana fada maka matsalarta kana cewa ta hadu??“ ya harareshi yace “ mace idan batai takama da gadara ba waye zaiyi?? girman kan ne kawai matsala…. ya sake bin inda muka bari a mota da kallo.“ Ni kuwa 2nda muka tafi mufida nata bani lbrn saurayin wai mu2min kirki ne kaza-kaza nidai ba kulata ba, don kasa gane me take nufi da hakan… Ammafah….koda baxance komaiba..senaga iya gudun grman kannata…
.
Yanxu ne aslin komai ze fara

Isata gida keda wuya na ketawa ma‘aikatan gdnmu rashin mu2ncin dana saba harma sai dana mari me baiwa fulawowi ruwa sbd yayi sakacin watsa min ruwa duk kuwa da cewa ba yana sane bane, kai tsaye dakina na wuce nayi wanka naci abinci na jawo laptop dina hau aikin dana saba. Bayan kwanaki biyu da haduwa da saurayinnan da ko sunansa ban sani ba ina zaune a bakin harabar makarantar tamu a wannan karon wayata ce kawai a hannuna sakamakôn laptop dina tana hannun mufida, zuwa da wurin da nayi ne yasa a gabana dai-daikun dalibai ke isowa suna wucewa ba ruwana dasu sai dai su wuce. wasu lktn zakaga daliban na zuwa ne a group- group kamar yadda al‘adar rayuwar makaranta take. Ana cikin haka ne group din da suka fi kowanne shahara a makarantar suka zo wucewa ai kuwa caraf idon saurayinnan a kaina ya dakata tare da duban na kusa dashi yace “nazir“. Wanda aka kira da sunan nazir din yace “na‘am leader.“ wuce min da jakar nan na hango mu2niyar, nazir din ya amshi jakar ya kallo inda nake tare da cewa “wlh leader kabi a hankali yarinyar nan big class ce zaka sha mari fa inkai wasa.“ ya rike kugu tare da cewa “Ta mareni?? haba dallah sai kace a zamanin jahiliyya?? kudai ku tsaya kusha kallo.

Ya juyo ya doso inda nake, dirar daddadar muryarsa kawai naji a kunnena da fadin “Amincin Allah ya tbbta a gareki ma‘abociyar son kadaici da hutawa“. Har ga Allah wani sanyi naji a raina amma da yake ni din ce kawai sai kauda kai kamar bansan me yace ba. ya sake yin murmushi yace “kauda kanki lfy tauraruwa me haske“, na sake hade rai na kalli kasa. woww!! gsky ke daban ce ban taba ganin wanda fushi keyiwa kyau ba sai ke. Ya fada yana kallona. Na cije lebena na dubeshi zanyi magana yayi saurin cewa “ina ma kiyi magana a ckn fushi daba karamin kwarjini zaki kara ba.“ Na dan rufe idona a raina nace “BALA‘I“ na kara hade rai nace “kaga nifa ba shashasha bace da za‘a zo har inda nake a cikani da suru2 idan ina son zama a wuri me hayaniya mezai kawoni nan? murmushinsa wanda adon fuskarsa ne ya karu yace “gani nayi zaman kadaici bashi da dadi shine nazo na debe miki kewa gashi kuma nayi nasara 2nda a baya bakinki a rufe yake yanzu kuma gashi yana motsi, na girgiza kai nace “to bana so idan wurin ne yayi maka zan iya tashi nabar maka“. Ya mike tare da cewa “ kinfi karfin kina waje ace wani ya tasheki amma ki sani babu wata halitta dake iya rayuwa ita kadai dole tana bukatar mataimaki Allah ne kawai yake guda daya baya bukatar abokin tarayya amma bamu y‘an adam masu rauni ba, yaja da baya tare da dago min hannu yace “sai anjima“.

Na bishi da kallo ba karya fa gayen ya hadu wlh, tun daga zubinsa har ya zuwa kalamansa da halayensa ababan birgewa ne. Ban jima a zaune ba na tashi na shiga class ko break ban fito ba sai da aka tashi, abinda ya kara bata min rai sai dana shafe min2na 15 da tashi direba na bai iso ba bare mu tafi na zauna bisa dandamalin dana saba zama na zaro wayata na kira direban yana dagawa na balbaleshi da fada duk da hakurin da yake bani sai da nayi na gaji sannan na kashe wayar hade da doka tsaki, Allah ya wuci zuciyarki yake tauraruwa me kyalkyali, na dago kaina muka hada ido da saurayinnan na bata rai naja tsaki na kauda kai. Yace “ina bbr aminiyar taki ne na ganki ke kadai??“ sakanni talatin na dauka sannan nace “ Ta tafi koyo sallama “ Ya saki murmushi yace “sorry i took the correction“ Amma me yasa duk ranar da ake kwallawa baki nemi inuwa kin zauna ba kika zabi zama a ckn rana??“ Cikin fusata nace “ina ruwanka? wai kai wanne irin mu2m ne?“ Yace “bakar fata, musulmi kuma bahaushe, bana fatan kice na takura miki don haka kinga tafiyata, sai anjima.“

 MAYE!!!!!! na fada a raina, dai-dai lkcnne direbana ya karaso mufida ma ta fito kai tsaye muka nufo gida, inata zabgawa direban ruwan bala‘i ta inda na shiga ba tanan nake fita ba. ******* Kwanaki uku da faruwar haka misalin 11:30am mun fito break da yake ban karya ba naja mufida muka shiga restaurant aka kawo mana abinci muka fara ci, bamu dauki tsawon lkc ba muka gama. Na kira dan matashin bakin saurayin daya kawo mana abincin nace “yauwa nawa ne kudinku??“ yayi yar gajeriyar dariya yace “No ai basai kun biya ba“. Na zabga masa harara nace “kai nifa bana wasa da yaro nawa ne kudinku aka ce??“ nakai karshen maganar cikin tsawa. ya girgiza kai yace “An riga an biya muku fa“, na bishi da kallo nace “kai kada ka raina min hankali kaga nayi kama da matsiyaciyar da za‘a siya wa abinci?? To ai ni ko gaba daya restaurant din naku nagadama ina iya siya bare abincin mu2m biyu kada ka batamin rai ka batawa kanka, nawa ne kudinku??“ fuskar saurayin ta canja yace “haramun ne a aikina na karbi kudin mtm biyu akan abu daya amma idan kina musu ga wanda ya biya muku can, nabi hannunsa izuwa inda yayi min nuni caraf idanuna suka dira akan saurayinnan me lakabin leader na dauke kai tare da runtse idanuna ckn takaici, shit!!! wai wannan wane irin mtm ne?? Na tambayi kaina naja jakata dake ajiye akan tebirin dake gabana na doshi inda yake. Ko sanin nazo inda yake baiyi ba na tsaya a kansa nace “mallam abin naka kuma yana neman yayi yawa fa, daga ina dan saurararka kuma sai raini ya shiga?? cikin rashin fahimta ya ajiye kofin juice dake hannunsa ya dago kai yace “ raini kuma?? me ya faru??“ Na dan harareshi nace “idan ba haka ba meye na biya min kudin abu mafi sauki da kowa ke iya siya irin abinci??“

Fuskarsa tayi saurin canjawa zuwa murmushi yace “ wlh na zaci wani gingimemen laifi na aikatawa sarauniyar matan wannan karnin, ashe ma ba wani abu bane “ Na bishi da kallo nace “ba wani abu ba?? kayi min wulakanci irin wannan kace ba komai bane??“, ya juyar da p-cap din dake kansa izuwa baya yace “Ni banyi miki wulakanci ba a wajena kyautatawa nayi miki sbd kin cncnci fin haka a wurina bawai nayi hakan bane don kankantar dake domin kin wuce haka, kuma ni a wurina kyauta ai itace mafi girman karramawa!! Ni kuma a wurina itace mafi girman kankantarwa, nawa ka basu na biyaka?? Na fada dai-dai sanda na zaro wata yar karamar jaka daga bbr jakata. Ya dago da sauri tare da bina da wani irin kallo tamkar bai fahimci abinda na fada ba yayi saurin girgiza kai yace “baki yi kama da wadda zata maida hannun kyauta baya ba sbd nasan kinsan hakan bai dace ba, abinda nake so ki gane shine don an baki abu kin amsa ba yana nufin baki fi karfin abin bane.“ Na tabe baki nace “well!! naji 2nda kai kagadama kaga zaka iya amma ka sani idan wai kayimin haka ne don naji dadi to banji ba, kuma bazan gode maka ba sbd bani na saka ba.“ yayi saurin sakin murmushi yace “dama badon ki gode min nayi miki sbd ba nema kikai ba martabarki ce kawai takai ayi miki abinda yafi haka.“ Na juya tare da cewa “kai dai ka jiyo“.

Sai dai a zuciyata ba karamin dadin kalamansa naji ba sbd ni mtm ce me son a zigani. Na nufi inda mufida take wacce har yanzu ke zaune kawai tana kllnmu ta mike kai tsaye muka nufi class muka cgb da lacca. *** Wato 2nda nake a duniya ban taba ganin mu2m irin saurayinnan ba, ya hadu ta ko‘ina kuma ba shakka yasan abinda yake yi kalamansa kawai ke tbbr da haka, abinda nayi iya kokarina na gano na kasa shine me yasa yake burgeni? me yasa yake da kwarjini a idona? me yasa bana iya wulakantashi kamar sauran mutane??? tambayoyin dana kasa bawa kaina amsarsu kenan ***. Bayan kwanaki uku da faruwar haka, na shiga inda ban taba shiga ba library don duba wani littafi me danake ma2kar bukatarsa da wuri, al‘adata ban damu na duba littafi a library ba domin waya kawai zanyi a kawo min shima wannan din don ina bukatarsa da gaggawa ne. Ni kadai ce a cikin wajen hakan yasa nake neman nawa ckn kwanciyar hankali, motsin shigowar da naji yasa nayi saurin dago kai muka hada ido dashi nayi saurin dauke kai daga kllnsa, yadan tsaya yana kllna lkc guda ya tako tare da cewa “Amincin Allah a gareki ya tauraruwar da haskenta baya disashewa“, ko kllnsa banyi ba naci gaba da abinda nakeyi, ya tako a hankali izuwa nesa kadan dani yace “nayi sa‘a kenan yau zan taya sarauniyar mata bincike me kike nema ne??“ ko kllnsa banyi ba nace “ Idon matambayi

Ya kyalkyale da dariya yace “ kema fa kina da abi dariya gaki dai kamar ba zaki yi ba “, ya zauna a kujerar dake nesa kadan dani ya dora da cewa “nayi mamaki ma2ka dana duba kaf makarantar nan ban hango tauraruwar dake haska wannan makarantar ba ke kinga yadda duk makarantar tay duhu kuwa?? akwai bukatar ki fita ko don ki haskata“.

 Na dauke kaina daga lttfan da nake dubawa nace “kai!! ina yin abuna a nitse kazo zaka rikitani wai kai wane irin mtm ne?? Kai baka rabo da NACI?? Baki, musulmi kuma bahaushe. Ya bani amsa irin wannan a karo na biyu sannan ya dora da cewa “ina da naci musamman idan ina so na isar da wani sako aka kasa fahimtata. Na tabe baki nace “sako?? wanne irin sako kake s ka isar??“ Ya danyi shiru jimawa kadan ya mike alamar was ta fita daga fuskarsa yanayi na fadar magana da gaske ya shigeta ya taka a hankali izuwa gaba yace “ Akwai wata kalma da ake kira SO wacce a baya ban santa ba, ban fahimceta ba hasalima ba yarda da ita ba. Abinda na dauka shine ba zata iya tasiri akaina b sai gashi lkc guda na fahimci ashe SO gsky ne domin tamkar kwayar virus yake wajen saurin fadada, yana da ma2kar gudu a cikin jini hakan kesawa yayi saurin bin sassan jiki kwatankwacin yadda yabi jinina ya hana min duk wani sukuni…. Nayi saurin jan wani dan karamin tsaki nace “ To ina ruwana?? “ Ya juyo izuwa gareni yace “abinda kika kasa fahimta shine na kamu da sonki duk da cewa ban sanki ba bansan daga inda kike ba hasalima ko sunanki ban sani ba, wannan na daga cikin aikin SO ba ruwansa da kyau, muni, asali ko kuma banbancin akida.

INA SONKI!!! kalmar da bana shayin fadarta a ko‘ina domin na tbbtr shine abinda ke ckn zuciyata. Nayi saurin dago kaina idanuwana suka zaro tamkar zasu fado, Kana sona?? Tambayar dana fara yi masa kenan na dora da cewa “ Ban taba tsammanin jin wannan kalmar daga bakinka domin wadanda suka fika komai ma ba wanda ya taba 2nkarata da wannan maganar… hakan na nuna miki irin son da nake miki kuma yana tbbtr miki ni masoyi ne gaske bana yaudara ba. ya fada kyakykyawar fuskarsa na kaina. Na ajiye littafan dake hannuna na mike da dubesh tare bata hade rai wanda ban taba yin irinsa ba nace “ kaga leader kake kowa?? wasanka yana yin yawa yakamata kasani akwai wasan da kakanni kawai ake yiwa irinsa…

Ya katseni da cewa “Wlh ba wasa nake ba idanun kadai sun isa su tbbtr miki da haka, amsa kawai nake jira daga kyakykyawan bakinki wanda ta yiw shine danbar fara sabuwar rayuwata“. Amsa kake jira?? na tambaya ina kllnsa nace “ kana tsammanin amsata zata zo a yadda kake so ne?? to kayi kuskure, babu wata maganar soyayya tsakanina dakai kayi gaggawar janye wannan maganar ko don tsira da mu2ncinka a idona. ya gyara zamansa izuwa kallo na sosai yace “ Bazan taba janye kudirina ba sai dai idan har zaki fada min shin wani mummunan hali gareni da za‘ ki sona sbd dashi?? Na girgiza kai nace “ba wani mummunan hali amma koba komai banbancin class… kuma ma kawai bana ra‘ayin soyayya yanzu.“ amma…………

Nayi saurin katse maganar tashi da tsawa nace “Bana sonka!! nace bana yi!! karka kara zuwar mi da zan2ka irin wadannan sbd nafi karfin jinsu bar na yarda dasu.“ Fuskarsa ta sauya ma2ka ckn yanayin da ban tab zaton akwai ranar dazai zama haka ba a yadda nake ganinshi, yace “ Naji na amince kuma na hakura amma zanso kiyi abinda idan na tafi baza zargeki ba sai dai na zargi kaina.“ Kamar yaya?? na tambaya ina kllnshi. Yace “ kiyi min duk irin jarabawar da kika gadama a duniyar nan da kowacce nau‘in tambaya kîka gadama idan har na fadi to shikenan na hakura kuma bazan taba zarginki ba sai dai na zargi kaina.“ Idan kuma ka amsa fa?? Nayi saurin tambayarsa. Yace “sai ki dauki kaddara ki yarda muyi soyayya Na bishi da kallo na koma inda nake a baya na zauna nace “ ba tambaya daya zanyi maka ba sai dai guda uku kuma cikin kwanaki uku a jere idan ka fadi a daya ko kayi tsallaken rana daya shikenan dole ka rabu dani.“ Na amince. Ya fada ba tare da jinkiri ba…. Na bishi da kallo ckn mamakin yadda bai tsorata da komai ba saima wani karfin gwiwa da yake da ita, ya tsareni da ido jiran irin tambayar da zanyi masa kawai yake. Allah ya sani yana ma2kar birgeni sbd ya hadu sa dai kawai ji da kai da takamata ta hanani na amince da ainihin abinda ke zuciyata, wacce tambaya ma yakamata nayi masa????? Tambayar dake ta yawo a zuciyata kenan ckn salo na nazari.

 Zuwa can na dago kai nace “tambayar yau me sauki ce ina so ka canki sunana wanda mahaifina ya rada min, sau daya kawai zaka fada idan ka fada ba dai-dai ba ka fadi.“ Yabi ni da kallo tare da gyara zama yace “ Sunanki?? Haba ranki ya dade ta ina kika taba ganin an fadi sunan mtm daga ganinsa??? SUNAY na daga abubuwan da suka fi komai yawa a duniya don haka amsa wannan tambayar is impossible a ko‘ina, a zatona zakiyi min tambayane wadda kwakwalwa zatai aiki wajen gan amsa amma ba canke-canke ba. Na danyi gun2n murmushi nace “daga farawa harka fara karaya?? wannan itace mafi sauki daga wadanda nayi maka tanadi, koka manta kai kace duk irin tambayar da nake so??“. ya kauda kai daga kallo na a hankali ya dan jima baice komai ba zuwa can yace “bari kwakwalwa tayi aiki“. Ya mike daga inda yake zaune ya fara takawa a hankali yana kaiwa da komowa hade da kallona a wasu lokutan, yanayin na nuni da zuzzurfan nazarin daya shiga, ni kuwa har wani murmushi nake yi idan na kalli halwar daya shiga, yau dai zan rabu da kaya. Abinda naketa darsawa kenan domin ina da yakini 100% bazai iya amsawa ba. y‘an min2na kalilan ya kwashe ya juyo gareni yac “A mafi yawan lkt suna nayin tasiri a kamar mu2 da yanayinsa, idan har an sami haka a kanki to in da tbbcn sunanki ba me guda daya bane irin sunan nan me guda biyu ko ince tagwaye kamar “fatima-bintu, zainab-abu, halimatus-sadiya! sai dai duk bakiyi kama da wadannan sunayen ba. Ya dan taka da kafarsa dake sanye da wani kyakykyawan farin takalmi ya juyo gareni ya kalle na dan lkc yace “AISHA HUMAIRA!!!!!!!“ Ya fada tare da sake mai-maitawa da fadin “yes nafi yarda sunanki Aisha humaira….“ ya zarce da kllna don jin abinda zan fada.

Ni kuwa 2ni idanuna sun kwalalo waje sbd AL‘JABI, ya akai kasan sunana?? tambayar dana jefa masa kenan, fuskarsa tadan fara saki yace “ kina nufin Na fada dai-dai kenan? Bansan sanda na gyada kai alamar eh ba, ya kaw gwauron numfashi hade da murmushi ya koma ya zauna tare da cewa “Step one done saura na gab ita dama SOYAYYA hadin Allah ce idan yaso koke baki da ikon hanawa kuma ina da yakini da karfin gwiwar yin nasara sbd ina ji a jikina akwai alkhair a tarayyarmu.“ Ya mike tare da ja da baya fuskarsa cike da yalwataccen murmushi yace “Nima sunan nawa me tagwayene UMAR FARUK!! sai an jima farar tauraruwa me farin haske. Ya juya ya fice. Na daki tebirin dake gabana kamar na fashe da kuka, gsky ya birgeni amma naji haushin yadda yayi kaca-kaca da tambayata mafi tsauri irin wannan domin ba canka kawai yayi ba hankalinsa ne yayi aiki a wurin. wai wannan anya kuwa mu2m ne??? dakyar na karasa abinda nazo yi na tafi class. °ranar sai ya zamana duk na zama wata iri 2nani irin zazzafar tambayar da zanyiwa faruk kawai nak wacce zata gagareshi amsawa, koda ace zan yard da soyayyar faruk amma bana so ya kureni, sai d duk tambayar data fado min sai naga kamar kwaf daya zaiyi mata° Washe gari 2nda na shiga makarantar bamu hadu dashi ba har aka tashi na fito daga class na hang driver na sai dai dole na jira mufida wacce bata fito ba har yanzu, na karasa jikin motar na bude bayanta na zauna ba tare dana rufe kofar ba saim kafafuna dana ziro waje, salon sallamar dashi kad keyi tasa nasan ya iso, na dauke kai kawai. Ya dubeni sosai yace “sorry for the late, Allah ya taimakeni baki tafi ba da shikenan na fado ina fatan dai baki manta tambayar da kika tanado min ba?? Na kalleshi nace “bana so saina kayar dakai ta karfin tsiya ka hakura kawai zaifi maka sauki daga jin tambayar da miliyoyin mutane suka gaza amsata masu ji da basirar, hikima da hazakar da tafi taka..Mai-makon kalaman yaudarar da nake amfani dasu suyi tasiri akansa saima ya kyalkyale da dariya ya dan taka kadan izuwa jikin kofar motar dana bude ya dafashi da daddadar muryars me ratsa zuciya yace “Humaira kenan kada kiyi tsammanin kautar da 2nanina akan abinda nake s kuma nake da yakinin zan sameshi, na kasance ina da baiwar yin abubuwan da miliyoyin mutane suka kasa, wannan kamar a jinina ne don haka karki damu kiyi min kawai ni abinda na dauka shine abinnan da muke yi kamar istahara ne a gareni indai tarayyarmu dake alherice to zan ams tambayoyinki koda sun kai 100, idan kuma babu alheri a ckn soyayyarmu to bazan taba iyawa ba.“ Nabishi da kallo kawai nace: *“ Akwai wata halitta a doron kasa wacce yanayint ke caccanjawa.

 Idan tana karama tana tafiyane da kafa hudu, idan ta girma kuma sai ta koma tafiya da kafa biyu, yayin da kuma ta tsufa sai ta koma tafiya da kafa uku, wacce halitta ce wannan???* Yayi saurin sakin kofar daya rike yabini da wani irin kallon da ni kaina sai dana tausaya masa, yaj da baya kadan lkc guda ya fara kaiwa da kawowa wajen hankalinsa in yayi dubu ya tashi, na saki yalwataccen murmushi nace “kaga faruk ba iya amsawa zakai ba ka…….“ Ya daga min hannu yace “ karki katseni “. Na daga ido tare da tabe baki a raina nace ‘ayi da mugani‘.“ Ya dan dakata kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya shafi gashin kansa yace “DANKARI!!“ Na kyalkyale da dariya kawai na dauke kai na fara latsa wayar dake hannuna sbd a yadda nake ji a jikina na gama dashi, sai dai ta ciki na ciki don kuwa kirjina dif-dif kawai yake don bansan yadda zamu karke dashi ba. tsawon lkc muka shafe amma babu alamun ya karaya da amsa tambayar saima dada kaimi da yake wajen 2nani da nazari, jim kadan yadan yi nuni da hannun tare da gyada kai ya saki murmushi kyansa ya kara fitowa, ya tako a hankali izuwa inda yake tsaye 2n dazu yace: “ idan har 2nanina da nazarina sun bani dai-dai- dai to ina da tbbcin ba kowacce halitta bace wannan face MUTUM wato bil‘adama.dalili kuwa mu2m sanda yana yaro da kafa hudu yake tafiya shine RARRAFE, gwiwoyi biyu hannaye biyu. Yayin kuma daya girma ya iya tafiya sai ya koma tafiya da kafa biyu kamar yadda ni dake muke tafiya yanzu. Lokacin kuma da mutum ya tsufa sai ya zamana kafa biyu ba zata iya daukarsa ba sai ya kara da sanda a matsayin kafa ta uku.“ Bansan sanda wan irin murmushi ya kwace min ba wanda shine ya nuna ainihin abinda ke zuciyata nake dannewa, yadda yake zano abubuwan tamkar me karantawa a littafi ya birgeni ma2ka. Shima yayi murmushi tare da cewa “ zan iya cew wannan murmushin tayani murnar cin nasara a karo na biyu ne??“ Na gyada kai tare da cewa “kwarai kuwa da alama gaf kake da cina da yaki faruk akan haka dole na jinjina maka domin kaine mu2m na farko daka far neman ka kureni, murmushin da kaga nayi na tayaka murna ne da kuma tausaya maka domin k kai matakin da dole kayo kasa domin gobe koda kai aljanine baka isa ka amsa tambayar da zanyi maka ba.“ Ya dago kansa ya fashe da dariya yace “kina birgeni sarauniya sbd komai naki me tsari ne ku da karfin gwiwa hakan na daga ckn abinda yasa muka dace da juna, idan wai kina tsorata nine to sai ince miki kima hutar da kanki don kuwa ma2kar ina tuna cewa soyayyarki nake nema to zanyi abinda aljani ma bazai iya yi ba. Na gyara zamana dai-dai sanda na hangi mufida tare da kokarin shigo da kafata ckn motar nace “can dai da yawarka“. Yayi dariya ya gyara doguwar jakar dake rataye a kafadarsa wadda ta hadu da dressing din jikinsa tayi masa kyau yaja da baya a hankali yace “Ki shiryawa fara sabuwar soyayya a gobe……“ Nayi saurin katseshi da cewa “ko kuma ka shiryawa bakin cikin faduwarka a gobe ba“. Ya dan dakata yace “ to shikenan zan iya cewa duk mu jira FINA din don ganin yadda zata kaya, ya dora hannunsa a gefen goshinsa ckn alamu na sarawa tamkar soja yace “sai gobe farin ganina“..

Hmmm mumadai allah yakaimu GOBEn muji wannan wata tanbayace haka..zata hada ko zata raba..?!

Mufida na isowa direban wanda har ya fara barci na daka masa tsawa ya farka ya juyar da motar muka nufi hanyar da zata sadamu da gida, Mufida ta dubeni tace “amma fa nayi mamakin yadda naga kuna hira da faruk harda dariya sai kace ba ke ba??“ Na kwantar da kaina kadan nace “manta da wancan faruk din lamarinsa sai shi.“ mufida tayi dariya tace “Ah kidai fadi gsky tbbs akwai wani abu“. Ganin yadda take kokarin kureni yasa na kautar da zancen ban bari yayi nisa ba, har na isa gida. *Abinda na kasa ganewa game dani shine: Nidai faruk na birgeni ma2ka, komai nasa naban sha‘awa, shine kawai a duniya da bana iya tozartawa ko in wulakantashi koda nayi niyya sai hakan ya gagara yiwuwa a wajena. Ga yawan 2naninsa da nake yi a koda yaushe banda son kasancewa dashi a kowanne lkc da nake yi!! Shin wannan shine SO?? tambayar dani bansan amsarta ba kenan.* Washe gari misalin karfe tara na safe tsaye nake a jikin wata faffadar bishiya dake harabar makarantarmu nesa kadan da inda dalibai ke zama, kasancewar yau an tashi da lullumi ga iska me dadi na kadawa yasa nake jin dadin wurin. Gefe guda dalibai ne group-group masu hira nayi masu kara2 nayi, Ni kuwa littafine a hannuna ina karantawa hankalina gaba daya tafi ga kara2n, jin sallamarsa yasa dole na tsagaita daga kara2n da nakeyi duk da cewa ban dago na kalleshi ba. Amincin Allah a gareki ya ma‘abociyar son kadaici da hutawa, Ya fada 2n yana nesa kadan dani. Dan kwalisan saurayi kllm kara kyau yake ya karaso inda nake tsaye yace “ina fatan dai kin shirya tambayar dazan bige a karo na karshe???

Nayi banza kmr banji abinda yace ba. Yayi murmushi yace “ Kinyi shiru kodai kin karaya ne?? Nayi yaken karfin hali nace “baka isa kasa na karaya ba, yau so nake ka fada min ranar da aka haifeni da watan da shekarar kayi jumulla ka fada min shekaruna nawa?? da wata nawa?? kuma da kwana nawa?? Nayi karatu a kasar waje ka fada min wace kasa ce kuma wacce university?? Na kumbura baki sanda nakai karshen maganar ckn gadara da takamar cewa na gama dashi. Ya kura min ido kamar baisanni ba. na kalleshi nace “yadai ka kasa cewa komai kodai ka karaya ne??“ Yayi murmushi yace “gskyrki da kika ce ko aljani yayi kadan ya amsa tambayarki tayau sbd shima baisan gaibu ba amma ina so ki sani SOYAYYA ba karya bace don haka duk abinda naji a jikina game dake to gskyne, zuciyata bata taba gaya min karya akanki ba don haka zan jaraba idan har son gsky nake miki na tbbt Allah zai bani nasara. Ya taka kadan gaba da inda yake yace: Irinku rayuwarku na tfy ne ckn tsari ba a hargitse ba don haka ina da tbbs idan nace, an saki a primary shekara shida sannan kika samu shekaru shida a ita primary din, kin secondary da shekaru 12. kika gama secondary da shekaru 18 kika wuce university kika yi shekaru 3, jumulla shekarunki ashirin da aya (21) yanzu. Tofa!! 2n daga nan idanuna suka zaro waje sbd AL‘AJABI. Ya kara gyara tsayuwa yace “idan har jikina dai- dai yake bani an haifeki 1/6/1994 kuma kinyi kara2 a OXFORD UNIVERSITY ta kasar england domin itace burin duk wani dan gata irinki.“ Hmm..

Nifa tun kafin ma yakai karshen zancen nasa bansan sanda duk abinda yake hannuna ya subuce ba naja da baya a dan tsorace, idan har faruk ba aljani bane to yana harka da aljanu. Kallo daya yayi min ya tbbr ya amsa dai-dai ya tako inda nake tare da durkusawa ya tattaro kayana da suka zube kasa ya mike muka fuskanci juna yace “karki AL‘AJABI ko mamakin abinda ya faru a maimakon haka ki yarda Allah keson tarayyarmu, nasan kina sona tun tuni don na dade da gani a idanunki amma kina dannewa abnd kika manta shine zuciya ba‘a yaudararta akan soyayya yau dai wasa ya kare zamuyi soyayya abar kwatance indai da tsawon rai. na karbi laptop dina da littafina harma da wayata daya miko min yaja da baya yace “Yes ki shirya daga yau an fara, I LOVE YOU.“ ya juya izuwa ga abokansa dake can gefe nesa sosai da inda nake, nabishi da kallo kawai na kwantar da kaina a jikin bishiyar da nake, wani murmushi ya kwace min Allah ya sani ina so kauce-kauce ne kawai irin nawa yau kuma karya ta kure. Nadan dade ina cgb da tsayuwa a wurin har zuwa sanda lkcn shiga class, ko break yau ban fito ba yau sai da aka tashi na samu naja mufida bamu bata lkc ba muka tafi, kai tsaye gd muka nufa bayan da muka sauke mufida a gdnsu. Isowata keda wuya da yake da yunwa na dawo kai tsaye kitchen na wuce na zubo abinci naci nayi sallar azahar sannan na jawo laptop dina na shîga aikina. Zaune nake bisa luntsumemiyar kujerar falon namu na tankwashe kafafuna laptop din na ajiye bisa cinyoyina gaba daya hankalina ya tafi ga laptop din sai shiga da fita nake, television dake yi ma kasheta nayi sbd karar ta dameni. Tunda na fara ba kakkautawa sai naji an kira sallar la‘asar sannan na rufe na sakko tare da shimfida darduma na jawo katon hijab dina dana tanada musamman don yin sallah nasa. Idarwa ta keda wuya momi ta fito falon ta zarce izuwa kujera ta zauna ta danna remote din dake rike a hannunta tafkekiyar T.V din dake manne a jkn bango ta dawo taci gaba dayi. Gamawata keda wuya na mike na koma kan kujera na zauna na jawo laptop dina na budeta, momi tace “aikin kenan bakya gajiya bakya daga kafa.“ Na danyi dariya nace “momi ai computer tayi, uhm don Allah momi dan rage karar t.v dinnan tana takura min, momi tace “don kina wannan shiriritar sai nabar jin abu me muhimmanci irin wanda nake kll yanzu??“ Nadan kumbura baki nace “ momi shiririta kuma??“ Eh an fada shiririta ai ni wannan makarantar taki da ita da shirme duk dayane a wurina.“

Na dan hade rai nace “ai kuwa momi ba shirme bace don kara2n computer na daya daga ckn mafiya tsada a duniya, kuma wlh yadda nake jin dadin makarantar nan ko OXFORD banji dadinta haka ba.“ Momi ta kauda kai tace “karyar banza!! yanzu dai ki tashi kije banki ki ciro min kudi zanyi baki gobe ba kudi a hannuna kinsan dadynki sai jibi zai dawo,“ Na dan cilla hannu nace “kayyyy!! momi kina gani aiki nake yi kuma…..“ Ta katseni tana kallona da cewa “OK ba zaki je ba kenan???“ Na mayar da kaina ga laptop din dake gabana nace “Zanje“ to ki tashi maza ki tafi kinga yamma nayi, na rufe laptop dina na nufi dakina kai tsaye bathroom na shiga nayi sabon wanka na wuce ma‘ajiyar kayana na saka wadanda suka dace dani a yanzu na dawo ga tafkeken madubina na zauna kujerar dake fuskantarsa zagaye dani kayan kwalliya ne bila- adadin kala-kala. Bayan dana gama shiryawa na kalli kaîna bansan sanda wani murmushi ya subuce min ba, hmmm… wato ba karya ne ba ni nakai mafi kololuwa fagen kyau bama kyau kawai ba komai nawa daban ne domin abinda kesa wasu muni ni kuma kyau yake kara min bare kuma nasa abu me kyau, Na zama kwatankwacin zarah a ckn taurari gasu da yawa amma daka daga kai ni zaka fara gani. Na fito izuwa harabar kasaitaccen ygdn namu ina takun isa, takama da gadara. Direba ya taso da gudu tare da cewa “ranki ya dade ina zuwa haka??“ Na harareshi nace “Ba ruwanka da yinda zanje bani mukullin waccan motar,“ nayi nuni da CR-V din dake nesa kadan dani. A tsorace ya miko min tare da cewa “amma…….“ Nayi saurin katseshi da tsawa nace “Yau nizan tuka kaina inda nake son zuwa ka koma kuci gaba da zaman munafuncinku, na warci mukullin daga hannunsa na shige motar na juyar da ita na fice nabi titin dazai sadani da inda zanje. Tafiyar min2na 15 nayi na iso katafaren bankin nayi parking motata a inda aka tanada na wuce ckn bankin, Al‘adata duk sanda nazo kai tsaye wajen manager nake wucewa ya 2ra a ciro min abinda nake so in juyo na fito sbd asalinsa yaron dadyna ne. Zuwana ofis din nasa dai-dai inda ya saba zama nayi turus don yau wanda nake tsammani bane ba abinda yafi kenan ba wanda ke zaunen 2n daga zamansa dress dinsa da komai nasa ma nasan ko waye. Na tsaya akansa nace “ Ah!! Ya haka kuma?? Dalibi a wani wuri ma‘aikaci a wani wuri??

Faruk ya dago kai koda ganin nice sai ya saki murmushi ya gyara zama yace “ kina mamaki ne?? Na gyada kai dai-dai sanda na zauna a kujerar dake fuskantarsa nace “yes!! dole da mamaki mana kodai faruk din biyu ne bayan wanda na sani??“ Yayi dariya yace “Nine dai wanda kika sani don ba sunana husaini ba bare kice hassan dina kika gani, dama kina zuwa nan ne?? Ba tare dana dubeshi ba nace “shi yasa ma nake mamakin ganinka don ban taba ganinka anan ba sai yau.“ Eh gsky ba zaki ganni ba sbd ba anan bangaren nake ba yau ne kawai na dawo nan as temporary time kafin me kujerar ya dawo ya karbi wurinsa, ya dago idonsa yace “cire kudi, turawa ko kuwa kawai yawon shakatawa???“ Na dan yi dariya nace “Ah haba yawon shakatawa a banki kuma?? Bama dai zaka ji abinda ya kawoni ba…… Me yasa????? Ya tambaya yana dubana. Nace “sbd ba wajen ka aka turoni ba wanda aka 2roni wajensa baya nan kaga kuwa a matsayina na y‘ar aike dole na koma na fada idan ance na dawo wajenka na dawo!!“ Yayi murmushi yace “Nima zanyi farin ciki ki koma din 2nda na tbbr idan aka tambayeki wa kika tarar zaki ce masoyinki FARUK kika gane a wajen, kinga ko tanan na fara samun shiga a wajen momi da dadynki.“ Na zaro cak a jakata da biro na dora a tebirin dake gabana na fara rubutawa nace “Tayaya kake tsammanin zan fadi haka???“ Sbd nasan ba zaki taba yin karya ba. Na tura masa cak din bayan dana gama rubutawa ya kira wani jami‘in banki ya umarceshi daya je ya ciro min kudin muka cgb da hira ckn nishadi, Na dubeshi nace “Lallai bayan kokari ma harda daukan dala ba gammo kake yi, AIKI irinna banki + KARATU irinna computer ba hu2 kenan???“ Ya kwantar da kansa jikin kujerar da yake kai yace “Aikin ne ya jawo kara2n kuma duk tare suke tafiya basu shiga lokacin hutu ba, Muna da rauni ta bangaren masu ilmin computer shine dalilin da yasa aka 2rani na karo sani akanta don cgbn wannan bankin, kinji dalili.“ Na bishi da kll nace “yanzu na gano dalilin da yasa bana ganinka in nazo, wato dan lele ne kai a bankin.“ ya daga kai yace “of course kamar yadda na zama dan lelen zuciyar humaira. Nayi saurin girgiza kai nace “Waye ya gaya maka? Baka samu wannan damar ba ba kuma zaka taba samu ba har abada sbd ni zuciyata FARUK ne kawai a cknta kuma daga shi na rufe ba wanda zan sake bawa dama ya shiga bare ma har yayi tasiri.“ Ya dan lumshe ido ya dago kai yace “ faruk na godiya hade da alkawarin rike amana bata shekaru kawai ba ta HAR ABADA.“

 Na jinjina kai nace “A wasu lktn alkawari nada saukin dauka amma saukewa nada ma2kar wahala“. Ya gyara zama yace “Ina da tbbcn duk nauyin alkawari ma2kar ke na daukowa shi to zan sauke sbd ni akan SOYAYYA….. ni kaina mamakin kaina nake yi.“ Na bishi da kallo kawai, nima na dade da yarda yana da zafin soyayya, jim kadan jami‘in nan ya dawo ya dora leda bisa tebirin dake gbnmu tare da cewa “Sir, gasu an ciro.“ Ok thank you, koma bakin aikinka. Ya 2ro minsu yace “An cika aiki.“ Na kauda kai nace “OK a takaice dai kora ta kake ko??“ Ya girgiza kai yace “Mezai sa na koreki?? Alhalin kece fitilar dake haskawa zuciyata hanyar daya kamata tabi?? Gani dai nayi kawai kin samu abinda ya kawo ki.“ Na juyar da kujerar da nake kai izuwa gefe nace “Amma ban gaji da klln faruk ba“. Yayi murmushi yace “Shima bai gaji da ganinki ba sai dai idan kuka kwantar da hankalinku wannan rabuwar ta wucin gadi ce domin zaku hadu a rayuwa ta har abada.“ Na saki murmushi kawai. Yayi saurin matsowa gaban kujerarsa yace “yauwa ni kuwa na manta ban karbi lambar sarauniyar tawa ba, na dago wayar dake hannuna kaina na kanta nace “ Ai da farko na zaci itama zaka canka ne 2nda shi yafi komai sauki a wajenka.“ Yace “Eh don dai kawai idan kika bani da kanki zata fi martaba ne a idona, amma da sai dai kawai kiji kira. Na 2ra wayata izuwa gabansa nace “ai ko ifritu ba yadda zaiyi ya canki lambarnan dai~dai.“ Yayi dariya kawai ya 2ro min wayoyi biyu na dauki tashi lambar na mike tare da rakiyarsa na fito daga bankin. Na dubeshi nace “kaga me girma manager nifa bance kayi min rakiya ba. Yayi murmushi yace “bai dace ba ace sarauniya kamarki tana tafiya babu dogari ko daya a gefenta.“ Na girgiza kai nace “A yanzu ai ba sarauniya da dogari bane ke tafiya, SARKI da SARAUNIYA ne.“ murmushi ya fadada a fuskarmu har zuwa sanda muka karasa jikin motata, ya bude kofar gaba tare da dora hannunsa a goshinsa ckn salo na sarawa tamkar wani soja yace “shiga da lfy tauraruwar taurari.“ nayi murmushi kawai na shiga na zauna ya mayar da kofar ya rufe da yake glass din a sauke ya dafa kofar da hannunsa biyu yace “murmushinki ya dace da fuskarki kwatankwacin yadda ni dake muka dace da juna, sai mun hadu next time farin ganina.“ Ya juya ya koma ckn bankin nabishi da kallo murmushi na tashi a fuskata har sanda na daina ganinshi a hankali na daga glass din motar tare da takata na nufi gd. Wannan shine tarihin asalin fara soyayyata da FARUK.

Daga ranar ne kwanci tashi alakarmu na kara karfi har takai soyayya me karfi ta shiga tsakanina da FARUK wadda tafi gaban a kwatanta, har takai mun zama ababan misali domin bawai tsakaninmu kawai ba kowa yasan alakarmu da kuma karfin syyrmu.“ Musamman a makarantarmu wanda kowa yayi mamakin ganinmu tare rana tsaka muna soyayya tamkar bani ba, daga nan ne kuma na zama ta mutane muka fara kulla abota da mutane daban- daban ta silar faruk. Ban taba jin son wani bil‘adama a duniya kmr FARUK ba kuma ban zaci zan tsinci kaina a hakan ba, takai ga bana iya yi masa musu a duk abinda ya fada, bana ganin rashin dai-dainsa a duk abinda yayi, Sa‘a daya da nayi da shima yana ma2kar sona domin idan son da yake min baifi nawa ba to nawa bazai fi nasa ba. Kasantuwar kusanci da karfin syyrmu yasa har aka fara kiranmu da sunaye daban-daban wasu suce LAILA da MAJNUN, wasu suce ANGELICA da MACIOLA dadai sauransu.**** FARUK ya kasance haifaffen garin kano kmr ni, ckkken sunansa UMAR FARUK MUHAMMAD yayi primary, secondary da university duk a garin kano, ya karanci irin abnd na karanta mathematic economics a BUK. Lbrn rayuwarsa daya bani wanda nafi tausaya masa shine kasancewarsa maraya. Ya rasa mahaifansa 2n yana karami ta silar hatsarin mota, ya taso ne a hannun kishiyar mahaifiyarsa me suna hajiya amina, yana yawan ambaton sunanta a koda yaushe domin a cewarsa itace gatansa a duniya ita zame masa uwa da uba ta rikeshi tamkar dan data haifa a cknta har izuwa yanzu. Ni kaina na yaba da halayenta da kirkinta ranar farko da faruk ya kaini gdnsu muka gaisa da ita, ba shakka yayi sa‘ar samunta matsayin wacce ta rikeshi har izuwa grmnsa. A duk ma‘aikatan gdnmu ba wanda baisan FARUK ba domin sai da takai idan direba yakai ni makaranta FARUK ne ke dawowa dani a motarsa sannan ya wuce, kai harta da momi ma tasanshi kuma tayi farin ciki da ganinsa ta yaba dashi sosai duk da ban fada mata ba amma ta fahimci abinda ke tsakaninmu. Kwanci tashi har lokacin gama makarantarmu yayi bayan tsawon lkc da muka shafe, ranar karshe ta rufe laccarmu bayan mun fito na nemi faruk banganshi ba mufida kuwa na can ckn kawaye suna irin sallamar nan tasu ta kawaye, nima nayi sallama da iya wadanda na sani da yake yunwa nake ji kai tsaye restaurant na dosa domin gani nake kmr bazan iya kaiwa gd ba, zamana keda wuya na umarci dan matashin saurayin dake jigilar kawo abinci na gaya masa abinda nake so ya kawo min.

 A hankali FARUK ya karaso tare da zama a kujerar dake fuskantata ya dubi me kawo abincin tare da cewa “kai kawo min abinci da sauri.“ Na dubeshi nace “wane irin a kawo maka abinci baka ga na riga ka bane??“ Ya dubeni ya tabe baki yace “ina ruwana ni??“ ya juya gareshi yace “ kai aje a kawo min ka taho da juice me sanyi.“ Na kara hade rai nace “baya yiwuwa wlh na riga ka don haka dole ni za‘a fara kawowa.“ Me kawo abincin ya tsaya kawai ya kasa tfy ya dubemu yace “to ai ni na rasa yadda zanyi daku ai duk kun rudani, pls daya ya hakura a fara kawowa daya mana.“ Faruk yace “kai manta da ita dallah jeka kawo mana.“ na kauda kai nace “a manta dani ko a manta dakai.“ Ya kalleni ya bata rai yace “karki ce zaki raina ni fa don bana wasa da yarinya ranki zai baci yanzu.“ Na zabga masa harara nace “sai dai naka ya baci wlh.“ Ya hade rai tare da mikewa ya nuna ni yace “KE!!“ Na mike nima na nunashi nace “KAI!!“ Muka dan dubi juna na tsawon lkc jimawa kadan muka kyalkyale da dariya yace “gsky kin iya fa sai kace gaske??“ Na zarce da dariya nace “Na iya koka iya gsky dakai actor ne zaka kwashi yan kllo“. Kai! dama ba fadan gaske kuke ba??? Me kawo abincin ya fada ckn AL‘AJABI. Faruk yace “kai dai je ka kawo mana abinci don sarauniyar tawa yunwa take ji. Har aka kawo mana abincin hira muke kafin mu gama mu tashi. Daga ranar mukai sallama da makarantar domin mun kammalata sai dai koda NI da FARUK kllm sai munyi waya ta tsawon lkc, ko mu kasance muna hira ta WHATSAPP wataran kuma har gdnmu yake zuwa. Haka muka cgb da rayuwa ckn jin dadi kafin KALUBALE ya biyo bayan soyayyarmu wanda yayi sanadin zubar hawaye na HAR ABADA. Wannan wani QALU BALENE..?

Bari in barku haka kar kuce nacika surutu.

Mu hadu a kashi na uku al’ajabi Part 3.

Leave A Reply

Your email address will not be published.