Al’ajabi Part 3 Hausa Novel

Al'ajabi Part 3 Hausa Novel

**** AL’AJABI PART 3****

BAYAN WATA BIYU DA KAMMALA MAKARANTARMU

 Ranar wata juma‘a da bazan manta ta ba tun misalin 4:30pm dana kwanta a dakina na kishingida kaina bisa lallausar katifar gadona sanyin A-C na ratsani ta ko‘ina daga na‘urorin sanyaya dakin, fuskata fresh ba wani abu dake damuna musayar sakwannin soyayya kawai muke yi ni da faruk. Murmushi ne kawai ke tashi daga fuskata a wasu lktn ma nayi dariya har da samba2na ni kadai, FARUK nada barkwanci sosai abune mawuyaci kuyi magana ta min2na dashi b saka dariya ba. 2nda muka fara hirar ba wanda ya gajiya a cknmu sai da aka kira sallar magariba sannan mukai sallama a hakan ma ba‘a son ranmu ba, Na tashi nayo alwala na fito falo momi na zaune har ta ida da tata sallar na jawo darduma nima, kiran sunan da tayi yasa na dago kai tace “wai lfy naji ki kina samba2 harda dariya ke kadai?? Na danyi kasa da kaina nace sambatu kuma?? Ah momi da Fa..ruk… muke hira….“ Nakai karshen maganar a kunyace. Tadan harareni ckn murmushi tace “OK hira ce ta dadi ko??“ Na danyi dariya kawai na tayar da sallah ta. Bayan na idar baifi da min2na biyar ba daddy ya shigo da sallamarsa duk muka amsa masa, zamansa keda wuya muka zarce da hira ckn nishadi da walwala. Zuwa can daddy ya kwantar da kansa bisa kujerar da yake kai ya dubeni sosai yayi murmushi yace “My daughter yanzu ne lkc yayi da yakamata ace kin samu mijin aure domin mutane sun dade sun cece-kuce akanki amma na toshe kunnuwa na, Alhamdulillahi kin samu duk kulawa daga garemu da kuma gata lkc kuma yayi da dole muma zamu aurar dake domin ke macece babu wani gata na karshe daya rage muyi miki kamar aure. Momi tayi murmushi ta dubeni tace “gskyne musamman da yake takai munzalin da ba abnd y rage mata sai aure. hmm..

Kwanci tashi kenan ba wuya yau daddy d kansa na zancen ya aurar dani, a raina sai naji wani dadi domin damar da nake jira kenan gata tazo burina na daf da cika. daddy ya gyara zama yace “akwai babban abkn kuma aminina wanda tsohon shugaban kasar nan ne to yana da dansa me suna tijjani. bansan a inda ya ganki ba to dai yasa uban ya fada min wai yana sonki kuma harma mun tsayar da rana gobe zai zo ku tattauna ko Allah zaisa ku fahimci juna. Kirjina ya buga da karfi na dago kai na dubi dadd kawai nama kasa cewa komai har ya tashi izuwa dakinsa, na koma kan kujera na zauna na tabe baki nace “Momi me yasa ba zaki gaya masa ba? In gaya masa me??? Ta tambaya tana dubana. Nace “amma kuma kinsan ni ina da wanda nake s ta yaya…..“ Ta harareni tace “rufa mana baki mara kunya da akai ki tashi kije ki fada masa mana, ko ni kin tab fada min kina son wani?? Na kara mirgina kai nace “amma dai nasan kin gane ai don Allah ki fada masa kinji“. Momi ta mike tace “KE! nifa a wannan harkar taku ba ruwana kinji.“ Ta wuce tabar falôn, nabi ta da kallo kawai na zamar da kaina na kwanta bisa kujerar da nake kai, to ma wai meye zaisa na dami kaina?? Nasan dai daddy ba yadda za‘ai yayi min auren dole. Na dauko tantsamemiyar wayata kirar blackberry, zuwa can na kauda wayar daga idona a abinda daddy ya fada ya dawo min, nayi y‘ar gajeriyar dariya. hmm… tab! wai dan tsohon shugaban kasa, to ai ni ko dan shugaban kasa me ci yanzu bai isheni kll ba. Na lalubi lambar FARUK muka dora daga inda muka tsaya. **Washe gari 2n misalin karfe 11:30 na safe jerin gwanon motocin alfarma har kusan guda goma suka shigo harabar gdnmu kowacce na takewa y‘ar uwarta baya, a dai-dai lkcn ina can sashin saman bene sbd inda na saba hawa kenan duk sanda nake bukatar kadaici a gdn namu. Na bude labulen tagar dakin da nake ciki na hang fitowar wanda na tbbtr shine tijjanin sai wani shan kamshi yake yake yana hura hanci cabinets na take masa baya, bansan sanda na zabga masa harara ba 2n daga nan inda nake alamar fara jin haushi da tsanarsa 2n yanzu kenan. Na mayar labulen na koma kan katafaren gadon dake madaidaicin dakin na kwanta Allah-Allah nak kawai barci ya daukeni. Jim kadan wata y‘ar aikin gdnmu ta hawo izuwa inda nake ta karaso tare da cewa “Ranki ya dade momi ce tace a gaya miki bakon ki yazo.“ ji nayi kmr na bigeta don haushi. Inda a dah ne da tasha tsawa da fada intayi wasa ma harda mari amma da yake yanzu na canja dag kwance nace “salama kyaleni kinji, je kice mata kawai barci nake.“ Ba wata gardama kuwa ta juya. Na jawo filo tare da gyara kwanciyata a raina nace ‘indai nice ya hada kansa da wahala‘, ko 2nanin na fito ma bana yi. Sai bayan akalla min2na 30 dan ni har na fara barci ma naji momi na kiran sunana.

Na dago kai na dubeta a jikin kofar dakin ta tsaya hannunta a kugunta ta hade rai zuwa can tace “baki san tijjani yazo fiye da min2na talatin yana jiranki ba?? ko ban aiko a fada miki ba?? wato sb wulakanci shine kinsan da zuwansa kikayi kwanciyarki ko?? To ki tashi maza ki sauka kasa yana falo ke yake jira.“ Momi nifa….. Zaki fito ko zaki fito ba?? ta katseni tare da tsareni da ido. Dole tasa na mike na sakko daga kan gadon na wuce ta gbnta kai tsaye dakina na dosa maimako nayi wata kwalliyar kirki saina dakko katon hijabin wanda mafi yawa sai zanyi sallah nake sashi nasa har jan kasa yake ina ma ina da nikab wlh sai nas haka dai na fito falon fuskata ba wani annuri nayi kicin-kicin, shi kuwa yana ganina sai ya wani bud baki wai murmushi yayi yace “sannunki da fitowa uwar kyawawa, ai ance min kina shiryawa ne nac a barki ki gama a nutse.“ Na girgiza kai nace “Ba wani shiri da nake yi kaw yanzu nayi niyyar fitowa ne.“ Ya dan daga kai tare da cewa “hakan ma ya birgeni, Ah kamar yadda nasan an gaya miki sunana TIJJANI nazo ne domin na sanar dake irin son da nake miki ina fatan zaki karbi syyta hannu bibbiyu. hmm.. soyayya! na fada tare da dubansa sosai nace “kaga mallam tijjani ba wani boye-boye ko bata lkc da zamu tsaya yi, indai don wannan ne t ba zaka taba samu ba ka ngd da zumunci a matsayinka na dan aminin mahaifina ka tashi ka tafi kawai.“ Nakai karshen maganar tare da kauda kai. Da alama yayi ma2kar mamakin maganar ya bini da kallo kawai zuwa can yace “Ah humaira ni kuma sai nake ganin duk duniya idan ta fuskar dace ne nafi kowa dacewa dake.“ Na dan saki murmushin rainin hankali nace “hm.. a hakan??“ of course!! ya fada tare da dorawa. “Idan kika duba dukkanmu y‘ay‘an masu hali ne, mahaifina tsohon shugaban kasa ne kuma yanzu haka yana wakiltar kasar nan a zaman koli na majalissar dinkin duniya, ke kuma mahaifinki shahararren dan kasuwa ne aduk fadin afrika. Kinga kuwa ko tanan mun dace da juna.

Na dan jinjina kai nace “Ok! dama sbd dukiya zamu so junanmu kenan daga ranar da dukiyar ta kare mun rabu kenan??“ Na rufawa tambayar baya da harararsa. Abin ya kulad dashi sosai ya dago kai sosai yace “yakamata ki sani nifa babban mu2m ne a kasar nan me dimbin dukiya ya zama dole ki girmama ni.“ Dukiya?? Na tambayeshi tare da dorawa da cewa “da motoci goma ka shigo nan a matsayinka ma na dan wanda dukiyar al‘umma ya rike, idan ka fit ka tambaya ina ma‘ajin gdnnan ya baka mukullin ma‘ajiyar motoci ka debi 100 idan kana so wadanda da zunzuru2n kudin halak ma aka siye su.“ Idanunsa suka zaro waje yace “kina nufin ni mahaifina barawo ne??“ Na kara gyara zama nace “maganar mu2nci kuwa babu 2nda aka wanko kafa aka taho barar abinda ba za‘a samu ba sbd alfarma ba zata samar dashi ba gashi kuma kudi basa iya siyanshi shine SOYAYYAR HUMAIRA.“ ya danyi shiru jim kadan yace “yakamata muyi magana ta fahimta pls karki manta daga nesa naz duk domin ke.“ Nesa?? sai ka koma ka fadawa nesa da yan nesa abnd kaje nema baka samu ba, na mike na dora da cewa “bata lkcn ya isa haka zan shiga daga ciki“. Ya dan marairaice yace “bai kamata kiyi min haka ba yakamata ki bani dogon lkc muyi magana ko dôn kasancewar nayo doguwar tfy. Na juya tare da cewa “yanzu ma ai ba korarka na ba, ga T.V nan kayi kllnka son ranka amma idan k gama karka kashe can an jima zan kalli wani program. Na wuce kai tsaye na doshi dakina kan ma nabar falon shima ransa a bace ya mike ya fice, na juya na kyalkyale da dariya KORA DA KALAMAI kenan na tbbr bazai taba yin marmarin dawowa ba, dam ba SON gsky ya kawoshi ba kalarshi ma tafi kama data munafukai don duk abinda yake fada babu alamun har zuciyarsa hakane. Na wuce dakina ban kara komata takansa ba ** Misalin karfe 8:00 na dare ina zaune bisa dardumata byn na idar da sallar isha‘i, kwala min kiran da naji ana yi kuma yasa na saurara dakyau Bisa mamaki daddy ne abinda bai taba faruwa ba kenan sai yau na jefa dardumar kan gado na tare da nufo falon, daddy na tsaye ckn fusata ya hade hannunsa biyu ta baya. Na zauna tare da cewa “daddy barka da dawo….

Tun kafin na karasa Ya katseni da cewa “Menene dalilin da mu2m zai taso 2n daga katsina domin ke, kuma na gaya miki matsayinsa da kuma ko waye shi amma maimakon ki karramashi saima ki wulakantashi?? Me kika fishi?? Anji ma bakya sonsa ki mu2ntatashi mana idan nazo sai ki fada min baiyi miki ba insan yadda zanyi na sanarwa mahaifinsa amma sai ki bishi d bakaken maganganu?? Shekararmu 40 da mahaifinsa ke baki isa ki shiga tsakaninmu ba.“ Na danja da baya a kujerar da nake zaune nace “kayi hakuri idan hakan ya bata maka rai gsky bana sonshi ne ina da wanda nake so kuma shim ai da laifinsa don me zai……“ Tsawa daddy yayi min a karona farko a rayuwata da fadin “Ki rufa mana baki, ki shirya TIJJANI ne mijinki nan bada dadewa ba za‘a saka ranar aurenku. Sbd girgiza bansan sanda na mike tsaye ba kaina yayi wata juyawa sau daya, na maimaita abnd daddy ya fada “TIJJANI ne mijina??“ Kwarai!! daddy ya fada. Nace “koda hakan na nufin bakin cikina da tbbt a takaici na har abada?? Daddy ya amsa da “koda hakan na nufin mutuwarki da tbbt a kabari na har abada.“ Duk da matsananciyar damuwa data bayyana a fuskata, idanuna suka fito waje kamar zasu fado. ba AL‘AJABIN mgngnunsa kawai nake ba, amma yadda idonsa ya rufe yake zazzaga min ruwan bala‘i ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba. Ya kara da fadin “da bakinsa yake fada min kince masa MUMMUNA, BANZA, DABBA!! kmrsa ki fada irin wadannan maganganun?? Kawai ji nayi kmr an sare min gwiwoyi, lallai TIJJANI munafuki ne lamba daya abin nasa harda kage da sharri kenan?? Wasu hawayen takaici irinsu na farko a rayuwata suka gangaro min, Na gyada kai nace “ eh na fad masa haka sbd ya cncnci fiye da haka ma kuma zan kara gaya masa haka duk inda muka hadu, ckn sheshshekar kuka nace “daddy karka manta k bani ilmi me yawa wanda yasa nayi wayewar da nafi karfin ayi min auren dole. Bana sonsa!! Bana sonsa!! Ina da wanda nake so kuma shi zan aura bana jin akwai wanda zai hana ni don addini ma ya bani dama. Kuka na ya karasa fitowa na juya izuwa dakina, in zuwa a hankali na zauna a gefen gadona na hada kaina da gwiwa naci gaba da ku kan da nake yi. Tijjani ne mijinki…

Koda hakan na nufin mu2warki da tbbt a kabari n HAR ABADA. Kalaman dake kara yawo a zuciyata kenan, ashe har akwai ranar da daddy zai fada min maganar d zata sani damuwa? Akwai ranar da zai aje dunbin son da yake yimin a gefe ya fada min bakaken maganganun da zasu sani kuka?? Na dade a zaune a haka har zuwa sanda naji an dafa ni, nayi saurin dagowa muka hada ido da momi. Na kwantar da kaina bisa cinyoyinta ckn kuka nace “momi daddy ya daina sona yanzu,“ T dago fuskata muka fuskanci juna tayi saurin grgz kai tace “ba haka bane ransa ne ya baci kuma kema da laifinki bai kamata ki yiwa TIJJANI haka ba“. Wlh momi abnd yace na fada masa duk karya yak yi ban fada ba. momi tabi ni da kll tace “amma me yasa kika cew daddynki kin fada??“ na goge hawayena nace “Sb ya tbbr bana son TIJJANI.“ momi ta jinjina kai tace “yanzu dai kiyi shiru ki share hwynki, dadynki ba wanda yake so a duniya kmr KE duk abnd ya fada nasan bazai taba aiwata dasu ba.“ Na karasa goge dukkan hawayen dake idona nace “ba lallai ya saurareni yanzu ba momi“. Tayi murmushi tace “nafi kowa sanin halinsa bas da wuyar sakkowa duk irin fushin da yayi jeki kinji??“ Na bita da kallo kawai a hankali na mike na doshi dakinsa gwiwata a sanyaye, Zaune na tarar dashi tsakyr dakin bisa dardumarsa ya idar da sallah, n karasa inda yake na zauna a gbnsa tare da sunkuyar da kaina kasa ckn sanyin murya nace “Daddy don Allah kayi hakuri nasan ban kyauta ba kuma na bata maka rai dana……“ Nayi shiru sakamakon daga min hannu da yayi yace “Ya isa haka my daughter koda baki roka ba ya zama dole na yafe miki kan KUSKURE DAYA TAK!!.“ Nagode my dad na fada dai-dai sanda nayi yunkurin mikewa. Ya dakatar dani da cewa “wanene wanda kike so din? kuma yaushe kuka hadu? Ya akai bansanshi ba kuma??“ Na danyi shiru kmr bazan ce komai ba zuwa can nace “sunansa FARUK, A makarantar koyon kwamfuta muka hadu dashi kuma har gdnnan yan zuwa momi ma tasanshi tfyr da kayi ce ta tsawon watanni yasa baka sanshi ba.“ Ya kada kai yace “Wajibi nane na baki wanda kike so amma ki sani mafi girman gatan da zanyi miki a yanzu shine na tbbr na zaba miki miji nagari idan har na samu wani matsala game dashi bazan amince dashi ba.“ Na gyada kai tare da cewa “Insha-Allahu zaka sameshi duk yadda kake so,“ Shikenan kice masa yazo ina nemansa“. Na amsa da fadin “To, Sai da safe my dad.“ Kai tsaye na fice daga dakin nasa na koma nawa, har yanzu momi na zaune bata tafi ba na zauna gaf da ita na saki murmushi tare da dakko hannunta na hada ckn nata nace “Momi kinsan me?? yace in fadawa FARUK yazo yana nemansa“ Tayi murmushi tace “Humaira kina son faruk da yawa fa!! kina barci ma fa kiran sunansa kike yi.“ Na danyi dariya nace “Ah haba momi a barci kuma??“ kiyi ta fadin FARUK! FARUK!! FARUK!!!“ Na kyalkyale da dariya, momi ta mike tare da cew “idan zaki kwanta ki rinka kashe kwan nan haskensa yayi yawa.“ Ok gud night my mum. Na fada ta juya ta fice.

Na karasa kwanciya kan gadon sosai na zaro wayata na nemi lambar faruk. Mun dade muna hira dashi har sai da dare ya tsal sannan mukai sllma dashi byn na sanar dashi sakon daddy. ***FARUK bai zo gdnmu ba sai byn kwanaki biyu misalin 5:00 na yamma, daddy na gd a lkcn da kaina na fita na yi masa jagora izuwa falo inda daddy ke zaune bisa kujera. ya amsa sallamar da mukai sai dai daga shigowarmu na lura da wani kllo da naga daddy na yiwa faruk anya kuwa…. Ya zauna a kasa daga jkn kujerar dake fuskantar daddy, ni kuwa mikewa nayi nabar falon har na shiga dakina hankalina ya gaza kwanciya na dawo da baya don jin hirar da zata gudana tsakanin FARUK da DADDY. daga inda na tsaya ina hangensu tare da jin abnd suke fada. *dai-dai sanda na tsaya faruk ne ke cewa “…cikakken sunana Umar faruk jibrin, mahaifina mllm jibrin dalhatu da mahaifiyata hajiya Hauwa‘u sun rasu 2n ina karami hakan…. Daddy yace “sunan mahaifinka mallam sunan mahaifinta Alhaji banbanci na (1) kenan, mahaifanka sun mu2 nata nada rai banbanci na ( kenan, ina sauraronka.“ Ba tare da wani damuwa ba faruk yace “na sami yin kara2 kurewarsa shine degree dana samu ana bayero university… Daddy ya gyara zaman hularsa yace “Ita kuma masters gareta a OXFORD UNIVERSITY england, another deference kenan.“ Faruk dai bai kula ba ya karasa da fadin yanzu haka ina aikin banki nakai matsayin activities- director.

Daddy ya kwantar da kansa ckn kasaita bisa kujerar da yake kai yace “Akwai banbanci me yaw tsakaninka da y‘ata wanda ya wuce a misalta, kasan ko danbe ake akwai wanda kll daya zaka masa kasan yafi krfnka!! Don haka……… Jirin da naji yana neman dibata ne yasa nayi saurin dafe kaina nabi fuskar masoyina faruk da k kawai na juya da sauri na shige dakina domin kunnuwana ba zasu jure jin maganganun da dadd ke fada ba, don na riga na gane inda suka sa gaba. Ina shiga kofar na mayar na rufe nabi jikin kofar daga sama har kasa hawaye suka gangaro min, wai me daddy ke nufi ne?

Nima tan bayana kenan ga masu karatu..! Medaddy kenune..?¿ Allah sa kuna fahinta..!

Tambayar dana fara yiwa kaina kenan tambayoyin suka cgb da yawo a zuciyata. wai me yasa daddy ke yimin haka ne?? Sai yanzu a lkcn da yakamata ya samar min farin ciki fiye dana ko yaushe yake kokarin dakile hakan?? Na dade a haka zan2kan na karo da juna a ckn kwakwalwata, dakyar na rarrafa izuwa kan gadona na kwanta kawai idona a bude karrr amma 2nanin dana tafi yana kama da ace barci nake yi, ni kaina bansan yadda zan kwatanta ynyin da na shiga a wannan lkcn ba. Allah sarki faruk kawai nake 2nawa wanda ban tab ganin mu2m irinsa ba, hakurinsa kawai ya isa yas na kara kaunarsa dubi yadda daddy ke fada masa bakaken maganganu amma ko kadan ba saima ya zamana kmr kara masa karfin gwiwa yake yi. Ni dai duk ranar ban ma koda yi sha‘awar fitowa daga dakina ba. washe gari kuwa da wani azababben ciwon kai na tashi wanda ina tsammanin ban taba yin kmrsa ba, sai duk da wuyar da yake bani ban damu ba don ba shine a raina ba abinda ya dame ni daban, momi cema ta rude ta takura min akan lallai mu tafi asibiti amm naki don ni nasan meye dalilin ciwon.

 Can misalin karfe uku na rana ina kwance abin duniya ya isheni ina son na kira faruk amma na kasa, ringin da wayata ta dauka yasa na dago kaina na mika hannu na jawota ina me runtse ido sbd yadda kaina ke sarawa. hmm.. DAN HALAK na fada a zcyt sanda nabi secreen din wayar da kll a hankali na daga tare d kaita kunnana sautin muryarsa ya ratsa jikina na kwantar da kaina bisa gadon na amsa sllmr da fadin “W salam farin wata sha kallo.“ Nayi saurin zarcewa da fadin “Don Allah ya kuka karke da daddyna jiya??“ Ya danyi dariya yace “kina so kiji na jiraki 30minutes koki dan rakoni, na kira wayarki har sa uku baki daga ba?? sannan baki kokarin kirana ba a tsawon awannin da aka shafe da faruwar abin?? Na dan kauda wayar daga kunnena dama a jiyan ya kirani?? Lallai na shiga wani yanayi da yawa. N mayar da ita tare da cewa “uhm! faruk kayi hakuri da wannan, amma dai don Allah ka fada min ya akai??“ Yayi murmushi tare da cewa to kin shirya?? Da sauri harda gyada kai nace “EH“.

Ya fara zano min hirar 2n daga farko duk yadda n jita haka yake fada sai da yazo kan gabar da nake so nayi saurin mikewa zaune duk da karuwar da sarawar da kaina keyi amma na jure duk don naji abnd banji ba, ya karasa daga dai-dai inda na tsaya da ji da fadin: “…..don haka bawai zan yarda ka auri humaira don kun dace bane ta bangaren dukiya ko alfarma ba sai dai don kun dace da son junanku, dôn hak lallai ka 2romin magabatanka ckn kwanaki uku rak!! domin muyi magana.“ Idona yayi saurin budewa kaina dake mummunar sarawa ya daina, bugawar da zuciyata keyi na fargabar abnd zanji ya daina, Nayi saurin gyara zamana nace “Faruk da gaske??“ “Kwarai“ ya amsa tare da fadin “kina mamakin daddy ya bani ke ko da kina tsammanin zai hana wanda kike so??“ Wani yalwataccen murmushi ya fadada a fuskata farin ciki sabo ya ziyarci zucita na koma kan gadon na kwanta tare da cewa “Baka san yadda akai bane!!“ Sai dai idan kin fada min, yace. Na kada kai nace “To ai ni jiya labewa nayi ina sauraron hirarku farkonta kawai naji hankalina ya tashi 2n jiya ba‘a dai-dai nake ba wlh. Faruk yayi dariya yace “To banda ke wa yake hukunci da farkon abu ba tare da yaji karshensa ba?? Ashe ni ban sani bama tauraruwata bata ckn walwala?? Nifa duk nayi 2nanin farin ciki ne yayi miki yawa.“ Na gyara kwanciya nace “INA!! ban taba yin barci harda mafarki alhalin idona yana a bude ba sai jiy Ga wani ciwon kai da nayi me taba kwakwalwa.“ Ya sake yin gajeriyar dariya yace “TO!! amma ina fatan kin warke??“ Na gyada kai nace “Eh mana kana fada min lbrnnan naji na warke.“ Dukkanmu mukai dariya.

 Kina sona da yawa fa!! Ya fada. Na dan zunburo baki nace “kai kuma fa??“ Yace “Ni? hm.. bawai SO kawai ba akwai KAUNA da SHAKUWA da BEGE gareki a koda yaushe gam da ALKAWARI wanda bazai canja ba duk rintsi duk wuya ba wani dalili na rabuwa har mu2wa. Na lumshe idona kawai muka cgb da hira ckn frn ciki da walwala na tsawon lkc sannan mukai sllm Sai sannan naji wata YUNWA ta taso min domin duk yinin yau dama banci komai ba. lallai na dawo hyycn na fada sanda na mike na wuce izuwa kitchen. *duk da cewa ina da shakka akan daddy amma lk guda duk wani bakin ciki ya fita daga zuciyata nac gaba da harkokina ckn walwala, 2nanin zan iya rabuwa da faruk kawai na sawa in kwanta rashin lfy ina kuma ga an rabamu din?? Shine kawai abn na tbbtr bazan iya jurewa ba. ** Kamar yadda daddy ya nemi faruk ya 2ro haka kuwa akai bayan kwanaki uku da daddare suka zo ina dakina na kishingida bisa tafkeken gadona fuskata fresh ba kyalkyali kawai take tana walkiya, zuciyata tayi fari, wayata nakan WHATSAPP messenger muna hira da faruk. Ina jin alamun hirarsu sama-sama sai bana iya fahimtar abinda suke cewa, har sanda suka gama tattaunawarsu suka tafi. Farin ciki kmr ya kasheni idan na 2no gaf muke d fara sabuwar rayuwa wadda nake hangowa 2n dag yanzu, farin ckn nawa bai yanke ba sai washe gar da naji abinda ya wakana tsakanin daddy da iyayen faruk. Faruk ne ke fada min ta waya, 2n da naji yana cewa in nutsu kada hankalina ya tashi nasan da matsala, ashe daddy rufe ido yayi ya zabgawa iyayen faruk rashin mu2nci hade da bakaken maganganu tare da yin alkawarin yarsa tafi karfin tozarcin auren talaka kamar dansu (FARUK).

 Tunda ya fara fada min maganar na mike tsaye, sanda yakai karshen lbrn kuwa zcyt ta gama harzuka, kwakwalwata ta dimauce, idanuna suka kada sukai jajir duk a ckn kasa da sakanni 30. Wayar ta subuce daga hannuna izuwa kasa ta tarwatse komai nata ya rabu da jikinta amma ban kula ba. Abin kuma harda yaudara?? Wato daddy na ganin idan ya biyo ta haka iyayen faruk su zasu fara tilastawa ya rabu dani. Nayi dawurwura a guri daya na juya da karfi na bangaji kofar dakin ta bude na fito da gudu na izuwa falon momi na tarar a zaune bisa kujera ta saurin dago kai tace “Lfyrki kuwa??“ Na tsaya a gbnta nace “wai momi me yasa daddy keyi mana haka ne?? Koda yana son rabamu ne bai kamata yaci mu2ncin iyayen FARUK ba!! Ashe daddy na falon rufewar da idona yayi ne yas na gaza ganinsa. Yace “kaji shashasha talaka har yana da wani mu2nci ne??? Nayi turus kawai nabi daddy da kallo wani takaici da bakin ciki suka rufeni, wlh badon dai ubana bane a wannan lkcn Allah ne kadai yasan abnd zanyi. Na dawo da baya a hankali izuwa tsakiyar falon duk da cewa ckn fushi nake ma2ka amma nayi kokarin sanyaya zuciyata na saita harshena ckn salo na marairaicewa nace “amma daddy bai kamata ka gyyto mutane da kanka kuma ka tozart su ba, idan har kasan haka zakayi 2n farko gara ace FARUK din ka fadawa amma ba iyayensa ba.“ Daddy ya matso da hularsa gbn goshinsa yace “Ok! kina nufin muyi sulhu dashi kenan na bashi hakuri ko??

 Ai hakan da nayi shine kawai abnd yafi a gareni domin iyayensa sunji zafin wutar maganganun dana watsa musu dole ma su tilasta masa ya rab dake.“ RABUWA!!! kalma mafi daci a gareni kenan har sai da takai n kauda kaina kadan lkc guda na dawo da fuskata gareshi nace “daddy talauci, arziki ko wata daukaka duk na Allah ne shike bada su ga wanda ya gadama a sanda yake so kuma ba abnd ke tbb face kudirar ubangiji muma arzikin da muke takama dashi Allah ne ya bamu kuma badon munf kowa bane.“ Daddy ya kwantar da kansa jikin kujerar da yake kai yace “EH!! nafi ki sanin wannan ai.“ Na dan matso gaba kadan nace “Ashe kenan ba wata hujj da za‘a ce yar me kudi ba zata zauri dan talakaw ba? tunda duk Allah ya haliccesu ya…..“ Kaji shashanci banza!! Daddy ya katseni tare da cewa “har akwai wata alaka tsakanin mai arziki da talaka da har zata kai ga aure?? Ai a doka ma hanyar jirgi daban ta mota daban b yadda za‘ai na siyar da akuya ta dawo tana cimin danga ba.“ Na danyi yaken takaici nace “Indai don wannan ne to karka damu domin dai-dai gwargwado FARUK nada rufin asiri zai iya sauke duk wani nauyi na dake wuyansa kuma koma ba wannan ba ni faruk ko kasa ya kawo min zan dafa mana mu ci.“ Bawai daddy ba har momi sai data dago kai a firgice, daddy yayi saurin duban momi yace “wai yarinyar nan da hankalinta kuwa?? Anya talakawan nan ba asirceta sukai ba??“ Na girgiza kai nace “bawai asiri bane hakan na nuna zunzuru2n SON da nakewa faruk. na durkushe bisa gwiwoyina na canja izuwa ynyn da dole a tausaya min nace “Daddy don grmn Allah ka taimaki rayuwata wlh faruk nake so domi ina da tbbs akansa kayi min komai 2n daga kuruciya har izuwa girmana wannan shine abu na karshe da zaka samar min wanda zan cgb da rayuwa ckn farin ciki har abada, FARUK bashi da wani aibu na yarda kayi duk binciken da kake so akanshi indai ka samu aibu tare dashi nayi alkwrn zan hakura.“ Daddy ya gyara zaman bakin glass din dake idonsa yace “bincike??“ yayi nuni da hannunsa da cewa “Talaka har yana bukatar wata ne?? Halin talaucin da yake ciki kad ya isheshi hujja, Bansan sanda kika lalace haka b kika manta ko y‘ar waye ke!! to idan ke baki da hankali ni bazan biye miki ba. Ranar auren y‘ata ina saran shugaban kasa da kansa zai halarta, gwamnoni, sanatoci, yan majalissu uwa-uba manyan y‘an kasuwa a kasarnan zasu halarta kawai sai ace ina ango aga wani talaka ya shawo kwana?? Kema kinsan bazai yiwu ba akwai masu sonki da yawa y‘ay‘an gata ki zabi wanda kike so a cknsu amma dole ki hakura da wannan FARUK din.“

Ban taba sanin daddy haka yake ba sai yanzu, a wannan lkcn ji nake duk duniya ba wanda yakaish rashin imani, zuciyata tayi harzukar dana kasa dannewa na mike kawai nace “ni kuma bazan rab dashi ba kuma bazan auri wani ba face shi ma2ka dai ina numfashi a dorôn kasa, hakki nane a barni na auri wanda nake so tunda bashi da wani aibu, hawayen idona ya karasa zubowa ckn sheshsheka kuka nace “wlh ko a kotu saina kwaci hakkina ba wanda ya isa yayi min auren dole!!!!“ Na juya nabar falon, daddy yabini da kll tare da mikewa, momi da bata tsoma mana baki ba tace “amma Alhaji….“ Ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu yace “tace ba wanda ya isa ko? ya kada kai yace To zata ga isar tawa.“ Ya gyara babbar rigarsa ya wuce dakinsa. *Daga ranar komai ya sake sakwarkwacewa dady ya shiga amfani da damarsa da krfnsa wajen rabani da faruk. sai da takai ya hana faruk zuwa gdnmu, kullin da yayi na cin mu2ncin iyayen faruk yasa shima suk masa lamba akan lallai sai ya rabu dani. Soyayyarmu na karuwa kalubale na daduwa, takaicin safe daban na rana daban na dare daban. Soyayya nada koguna da yawa nikam na ruwan zafi na fada, ga tarko ya rike min kafa hagu da dama na rasa yadda zanyi na kwance, sama da sati daya ko a waya na daina samun FARUK haka ya gigitani ma2ka har sai da takai abinci ma ya gagareni ci duk na rame tamkar bani ba, rayuwar da ban taba zaton zata juya min ba. Cikin bakin ciki kmr yadda na saba nake zaune a yau ma, zaune nake ni kadai a tafkeken kayatacce falon gdnmu wanda yanzu ya zame min tamkar kurkuku na zauna bisa doguwar kujera dan karamin filo na dora bisa cinyoyina tare da dafash sbd 2nani idona ma baya kiftawa hankalina 100% baya jikina. Dafa nin da momi tayi yasa nayi firgigit tamkar wacce ta farka daga barci nabi momi da kallo da jajayen idanuna tamkar gauta, nasan danniya kaw takeyi ita kanta amma abin ya dameta. Ta zauna tace “Humaira me yasa kike hakane?? Kefa ba karamar yarinya bace da zaki mayar da kuka mafi tasiri akan komai naki. wannan 2nanin da kike yawan yi baki san babbar illane a gareki ba??

 Akan hakan gara kiyi addu‘ar Allah ya zaba miki abnd yafi alheri. Momi in auri faruk kawai shine alheri. Tabini da kll tace “FARUK!! FARUK!!! FARUK!!!! Kllm maganarki kenan??? Uhmmm nima allah ban wadda xatasoni kaman haka..koda wata tacemin she love me morther dt bet amma bataso wai asan tana sona agidansu..it a true love..?

Duk maganar da za‘ai dake sai kinyi kokarin dangantata da FARUK?? zaifi yi miki kyau ki hakura da soyayyarsa… Fuskar momi ta canja ma2ka irin yanayin da ban taba gani ba tace “amma Alhaji rashin tausayin d rashin imanin yayi yawa wlh, a ina aka taba….“ DAKATA!! ya fada sanda canja fuska, yace “ince dai y‘ata ce ko?? nina haifeta??“ Auren dole fa kake shirin yi mata!! Haka na gadama. Daddy yayi saurin mayar da martani. Nabi daddy da kll wasu hawaye masu zafi tamkar tafashashshen ruwa suka gangaro bisa kuma2na, na mike muryata na rawa nace “Kayi zabinka da kake ganin yayi maka, amma hkn ba lallai ya zam zabin ubangiji ba wanda zabinsa shine mafificin zabi don haka har yanzu banji a jkna na rabu da FARUK ba. Na taka a hnkl izuwa dakina. Momi Ta kada kai tare da cewa “wannan matakin naka Ba komai kake sonyi ba face cutar da ita wl ta tashi 2n daga kuruciya bata san meye takaici b bata san meye damuwa ba lkc guda kana kkrn tusa mata su toka sani idan humaira ta haukace karka zargi kowa face kanka,“ Ya hade rai yabita da kll kawai ya doka tsaki ya koma kan kujera ya zauna ya zaro jaridarsa ya fara karantawa. *A kwana a tashi kwanaki sai kara matsowa suke, Abu kmr wasa yana nema ya zama gaske, ckn kankanin lkc zance ya karade ko‘ina cewar bikina saura y‘an kwanaki ai kuwa duniya ta dauka kmr guguwar yaki. Ban kara tbbtrwa abin gaske bane sai da ya rage sati daya, wasu akwatina dana iske sunyiwa falonmu tsinke da ni kaina bansan adadinsu ba ak ce wai kayan lefe nane, hakan ya girgizani ma2ka lallai daddy da gaske yake. Kmr a mafarki haka nake ganin abin gashi kuma yana nema ya tbbt gaske, kuka 2n hawaye na zub har sun daina ma zuwa. Ba komai nake hangowa ba sai rayuwar da zata z min a gaba ta shekaru masu yawa da zanyi ckn takaici da damuwa watakila na har abada, abinda na dauka shine aure shine last distination na duniya a wurin mace walau ta dace da rayuwar farin ciki ko takaici na har abada. Illolin mace ta auri wanda bata so sun wuce a misaltasu, a yadda nake jin tsanar TIJJANI wlh a duniya ma bana son ganinsa yana rayuwa ina kuma ga ace mu zauna har abada???

 Wadanda ke waje basu san meke faruwa ba gani suke ai hadin ya dace har tayani murna akeyi ta waya, ciki harda wadanda bansansu bama abnd k kara min takaicin kenan. Wasu ma ganin da suke yi ni na juyawa faruk bay sbd dan uwana me kudi yazo, dadai sauran zan2k ire-iren wadannan. ba wanda yasan gskyr abinda ke faruwa sbd ba wanda na sanarwa, abune da nake zaton cewa naf karfinsa yazo yafi karfina, abnd nake ganin bazai yiwu ba yake nema ya yiwu. Lkcn daya rage saura kwanaki uku sai ya zamana duk gdn T.V ko radio daka kamo ba sai ka samu ana sanarwar DAURIN AURENMU, jaridu da mujall duk an baza gari ya dauka auren y‘ar gata AISHA HUMAIRA ISMA‘IL yazo, harabar gdnmu har ta far cika da mutane anata kafa runfunan alfarma na manyan baki da kanana. a dai-dai sanda ya rage saura kwanaki biyu da safe ina kwance nayi nisa a duniyar 2nanin dana saba ban sani ba ashe mufida tazo ta shigo har dakina kuma ta zauna ban sani ba, ta dade tana kllna sannan ta tabani da cewa “KE“. Na kakalo yake wanda yafi kuka ciwo nace “Ah mufida yaushe kika zo??“ Ta bini da kll kawai tace “HUMAIRA 2nanin me kikeyi haka??“ Nayî kasa da kaina kawai zuwa ca na girgiza kai tare da cewa “ba komai“. Karyane wlh, ta fada tare da dorawa da fadin “Naji sanarwar aurenki rana tsaka, kuma abin mamakin da wani me suna tijjani ina faruk din kuma?? nidai a sanina shi kike so.“ Nayi kokarin hana hawayen da suka taho zuba amma na kasa, “bakisan abnd ya faru ba??“ na tambayeta. Tayi saurin mayar min da amsar “Na sani amma zatona ke kika canja ra‘ayi da kanki don banyi zaton duk duniya akwai me tilastaki ba.“ Na girgiza kai nace “Daa kenan amma yanzu ta canja daddy ya daina kaunata ya tsaneni yafi son mu2 da bakin ciki akan na rayu…..“

Tayi saurin rufemin baki tare da rike hannuna ckn nata tana me grgz kai tace “karki ce haka, may b a ganinsa gata yake sonyi miki, addu‘a yakamata kiyita yi kawai a yanzu amma ba kuka ba sbd ba maganin dazaiyi miki a ynzu.“ taci gaba da tsara kalamanta wasu na gane inda t dosa wasu ma na kasa ganewa har dai mukaî sallama. y‘an min2na wayata tadau ringing Na jawota a hankali nayi arba da sunan TIJJANI!! me kuma ya bugo ya fada min?? kmr bazan daga ba amma Na daga tare da kaita kunnena, dariyar da yayi ce ta fara dukan kunnuw na, yanzu fa kin hakura ko har yanzu kina da ja?? abnd ya rage dai bai fi awanni 48hrs ki tbbt amaryata“. Duk yadda naso na danne kuka na sai daya fito, tijjani yayi dariya yace “irin dan kukan nan na al‘ada a gurin amare ba sbn abu bane“. Amma kai mugu ne wlh ba tausayi ko imani a zcyrka ko kadan, Ya kara fashewa da dariya na saki wayar ta fado bisa katifar makeken gadon da nake kai, nayi ruf da ciki kawai na rufe idona sautin kukan ma baya fitowa. Tsawon lkc na kwashe a haka har sai da wayar dake kusa dani ta sake daukan sabuwar kara, Nay wata irin dagowa a fusace na warto wayar a zaton tijjani ne sai kuma fuskata ta canja. Faruk ne nayi saurin dagawa tare da kaita kunnen sautin sheshshekane kawai ke kaiwa da komowa, dakyar nace “faruk shikenan mun rabu ko?? ki jirani zanzo har gdnku yanzu.“ A firgice na dago kirjina ya buga da karfi, gdn suwa?? karka zo zasu cutar dakai fa!! FARUK!! sai dai ina! tuni ya kashe wayar.

Ina ckn frgbr ne kasa da min2na ashrn naji hayaniya na tashi a hrbr gdnmu, na tbbtr shine bansan sanda na zabura da gudu na fita daga dakin ba maimakon na nufi wajen rikicin amma b dama kai tsaye saman bene na nufa na tsaya gaf da farfajiyar saman ina hangen abnd ke faruwa. Turewa, hantara harma da dukan da daka-dakan samari majiya karfin suka farmasa ne yasa na daf bangon dake kusa dani ina me miko hannu haway na kwarara daga idona, Tausayinsa yai bala‘in kamani. Faruk me yasa kazo?? Nayi tambayar badon a ban amsa ba. Da yake umarnin da aka basu kenan a knknn lkc sukayi masa lilis!! Wani layi da naga yana yi ne ya kara rikitani karfa su kasheshi, zuciyata ta fada min. nayi wata irin juyawa da gudu na biyo hanyar da zata sadani izuwa inda abin ke faruwa sai dai bis tsautsayi dora kafata bisa matattalar benen keda wuya na zame tare da rikitowa 2n daga kololuwar saman benen zuwa kasa……Zamewar ce tasa ba shiri na rikito gadan-gadan izuwa kasa, a maimakon na mirgino ta matattakalar sai jikina ya zamo nayo kasa kacokan. Tazarar dake tsakanin kasa da sama nada yawa na kwarara uban ihu wanda shine iya abinda na sani ban kara bude id ba sai a gadon asibiti. Awanni masu yawa ne suka shude ina ckn yny na suma, lktci sunyi nasarar ceto rayuwata daga halaka bayan tsawon lkcne kuma na farfado. A hankali idanuna suka bude tamkar wadda ta farka daga barci ni kaina abinda ya fara fado min kenan barci nayi, nayi saurin karasa bude idanun nawa a sanda na tbbtr nan ba inda na sani bane ina nake meya faru dani?? Nayi yunkurin tashi naji an danneni a sannan ne nabi inda nake da yanayin da nake lkc guda duk abinda ya faru ya fado min, Na dubi kafafuna dake mike a dai-dai gwuwoyina ansa wani kurunbon roba daban san ko meye ba. Sai fuskata dake kunshe da ciwuka na kujewa dama sauran sassan jikina, Na daga kaina mukai ido hudu da momi sai kuma MUFIDA dake zaune gefena. bana jin bakina zai iya furta komai hakan yasa banma yi yunkurin cewa komai ba, naci gaba da jujjuya idanuna ina kallon faffadan dakin asibitin. A wane hali faruk ke ciki kada dai ace sun kasheshi?? Abinda yayi saurin fado min kenan, Wasu hawaye suka gangaro min. budewar da kofar dakin tayi da saurine yasa muk kalli hanyar shigowar daddy ya fado a firgice, nayi saurin dauke kaina daga kllnsa. Ya karaso inda nake yana ganin yanayin da nake ciki ya dafe kai tare da doka salati ya juya ga momi a rude yace “wane hali ake ciki?? me likitan yace muku?? momi ta girgiza kai tace “Ba abinda ya fada mana yadai ce kawai idan kazo yana son ganinka.“ Inna lillahi wa inna ilaihir-raji‘un. Daddy ya sake nanatawa ya gyara zaman babbar rigarsa tare da juyawa ya wuce izuwa ofis din babban likitan dak kula da sashen.

 Zaune lukutin bakin mu2min yake yasa faffadan tebirin dake gabansa a gaba sai rubuce-rubuce yake, shigowar da yaji tasa ya dago kai. Sannu da zuwa Alhaji ya fada tare da mikewa don girmamawa. Doctor wane hali yata ke ciki?? meya sameta?? fuskar likitan tayi saurin canjawa ckn nuni yace “bismillah Alhaji zauna“ Ya fada dai-dai sanda shima ya zauna. Koda daddy baiso ba dole tasa ya zauna a kujera dake fuskantar likitan ckn tsananin zakuwa da so jin abinda zai fada masa. Likitan ya gyara zama yace “Alhaji kasan ita fadowa daga sama irin wannan na zuwa da abubuwa daban-daban wani lkcn a sami karaya, rauni koma a rasa rai dungurungum. Anyi sa‘a bata rasa ranta ba ba kuma a samu karaya ko daya ba, hakan ya farune sbd sanda tazo kasa da gwiwa tazo shine yasa….“ Shine yasa me….. Daddy yayi saurin tambaya a firgice. Likitan ya gyara zaman farin gilas din dake idonsa yace “ Kasan a yadda gwiwa take ita ke daukar dawainiyar iya taka kafa gaba daya ko kuma iya karyata a zauna daidai sauransu. Magana da gsky kokon gwiwarta dukkansu sun sami matsala munyi kokari mun dai-daitasu daga gocewar da sukai amma sunyi sanyi ma2ka sbd buguwar ba y‘ar kadan bace hakan yasa zata dau dogon lkc bata iya taka kafarta kamar yadda kowa yake yi ba. Doc..tor me kake…nufi ne?? Daddy yayi saurin tambayar. Abinda nake nufi shine a yanzu kafafunta basu da maraba dana karamin yaro don haka za‘a dau lkc bata iya taka su ba.“ Ckn kallo me kama da harara daddy yace “kada dai kace min ta zama gurguwa??“ Kayi hakuri alhaji amma ta zama, sai dai kawai na wani dan lkcne zata dawo taci gaba da tafiya kmr kowa. Daddy baisan sanda ya cire hular dake kansa ba ya sake doka salati tare da goge gumin dake kwaranyo masa ya matso gbn kujerar tare da dafa tebirin dake tsknnsa da likitan yace “doctor yanzu ba yadda za‘ai?? kasan kudi ba matsalata bane k nawa ne zan iya biya kada ta zama nakasashshiy doctor.“ Wannan ba magana bace ta kudi 2nda kokai nasa baka taba jin inda akai dashen gwiwa ba, dole sai dai ayi hakuri ba abnd za‘a iya yi kuma duk inda kaje ina da tbbcin haka abin yake. Kuma da yake ynyn larurar tata ba wadda dole jinyarta sai a asibiti bane nan da wasu y‘an awanni idan komai ya dai-daita muna iya sllmrku ku koma gida aci gaba da kula da ita a kula kada ku sake tayi yunkuri na taka kafar sbd a yanzu kafarta tamkar ta jariri take. Daddy ya dago tare da dafe kai yace “ynz shikena ckn y‘an awanni y‘ata ta zama gurguwa???“ Sai dai hakuri. Likitan ya fada.

A sanyaye daddy ya dawo dakin da muke, ina kwance nabi fuskarsa da kll har izuwa sanda ya zauna yaune karon farko da naga hawaye a idonsa. Kmr yadda likitan ya fada haka kuwa akai domin ranar aka sllmemu, abnd yafi bani mamaki shine nidai bana jin wani ciwo a kafata sai dai kawai ji da nake tamkar kafafuwan ba ajikina suke ba. Ko kadan bazan iya motsa su ba, KADDARA kena idan tazo babu me iya canjata kasa da awa 12 na zama gurguwa. Rayuwa ta kara juye min bangare mafi baki da muni, na shiga kangi na bala‘i da masifa da ko a mafarki ban taba 2nanin zan shigesu ba. WASHE GARI tijjani yazo har gdnmu ko dakina inda nake bai karaso ba a falo ya zauna anan daddy yazo ya tarar dashi ya zauna tare da cewa “TIJJANI kaga abnd ya faru ko??“ Wlh naji Alhaji. Ya fada fuskarsa a daure, babu alamun walwala tare dashi. Daddy ya gyara zama yace “amma KADDARA baki iya zuwa ba, um-u-um!! yanzu ya za‘ai tijjani??“. Game da me fa?? Ah game da harkokin bikin nan mana kasan duniy ta gama sanin gobe ne ga manyan baki sun hallar an gama shirya komai bai kamata ace anji kunya ba.“ Ban gane ba Alhaji. Tijjani ya fada. Daddy ya gyara zama tare da matsowa gab da kujerar ckn kasa da murya yace “a bari a daura auren nan idan yaso koda tarewar ne sai a daga y zama dai an fita kunya…“ Allah ya kiyaye!! Tijjani ya fada tare da dorawa da fadin “wani zancen aure gsky a barshi Alhaji me za‘ai da HUMAIRA bayan ta zama NAKASASHSHIYA?????“

 uhmm allah hadamu damasoyanmu nagaskiya badon wani abu namuba..!

Tijjani yacigaba da cewa Ina dai jajanta maka na abnd ya samu y‘arka amma ba2n aure babu gsky ba yadda za‘ai kamar ni ace na auri gurguwa, da harkokina zanji ko kuma da jiyyanta? Kafin na taho munyi magana da dad dina kuma y fadawa da duk wadanda a bangarenmu muka gayyata cewan an fasa bikin nan. An fasa?? Daddy ya tambaya ckn kaduwa. kwarai na hakura da ita don bazan iya zaman KADDARA ba, daddy ya kara sanyaya murya yace “haba TIJJANI abin fa ba wani me muni bane likit ya tbbtr min zata dawo normal ckn y‘an lkt kankani.“ Tijjani ya mike tare da cewa “Alhaji kaga tafiyata, na isar maka da sakon daya kawoni.“ Ya gyara zaman suite din jikinsa ya juya ya nufi hanyar ficewa duk da kiran da daddy ke masa TIJJANI!! TIJJANI!!!. Amma ina! ko alamun waiwayowa baiyi ba dai-da lkcnne nida momi muka fito ina zaune bisa keken guragu irin na zamani a hankali momi ke 2rani h muka karaso tsakiyar falon momi tabi kofar fitar d kll ta dawo da kllnta ga daddy tace “Tayaya kake tsammanin zai dawo?? Bayan dama ba don Allah yake sonta ba?? Koda ma ace anyi auren idan kaddara irin wannan ta sameta juya mata baya zaiyi! Amma abin tambayar me yasa shi mahaifinsa ya tilasta masa ya aureta a haka?? Shi ya manta amincin dake tsakaninku?? Na tbbtr yana sane amma zai iya danne wannan y nunawa dansa syy abnd kai ka kasa yi kuma ka kasa ganewa kenan.“ daddy ya 2nbuke hular kansa ya jefata kan kujera gaba daya ya rikice dakyar ya karasa kujerar da tafi kusa dashi ya zauna ya dago kamar ya fashe da kuka yace “kinga shugaban kasar CHAD yanzu haka ya sauka a hotel kuma don daurin auren nan yazo, banda wadanda suka 2ro wakilansu, ga sanatoci ga gwamnoni banda abokaina manyan y‘an kasuwa na duniya duk sun hallara abin kunyane na 2nkaresu da maganar an fasa bikin nan, inna-lillahi wa inna-ilaihir raji‘un….“ Yakai maganar dakyar. Hmm..

Zaune kawai nake ina binsa da kallo bam ta tawa yake ba ta yadda zaiyi ya fita kunya kawai yake, ba a wanne hali nake ciki ba. Hankalinsa ya tashi ma2ka fîye da ko yaushe sbd abnd baiyi zaton zai faru ba ya faru, Amma ni a wurina hkn yafi yaimin don gara na tbbt a yanayi da nake ciki da na auri tijjani. o-o-ooo!! Ina zansaka raina??? Daddy ya sake fada kamar zai rushe da kuka don takaici. Budewar da kofar tayi da karfi yasa duk hankalinmu ya koma gareta, kamar daga sama FARUK ya fado da saurinsa caraf muka hada ido dashi duk da a yadda yake ba‘a farin ciki yake ba amma bai hana annuri tashi daga fuskarsa ba. Yanayin tfyrsa ya canja ya fara takowa a hankali muna klln juna. Nayi saurin cewa “FARUK meya kawoka?? me kaz yi?? Kayiwa Allah ka juya ka tafi karka yarda ka kara kusanto inda nake sbd ni yanzu bani kadai bace tafe nake da rakiyar KADDARA, yayinda BALA‘I da MASIFA ke take min baya. Yayi saurin girgiza kai yace “Ba wata kaddara da zata iya sawa na gudu na barki, karki manta Alkawarinmu na kasancewa a tare duk tsanani du wuya. Da ace ba wata masifa da zata iya riskar dan ada toda har abada ba za‘a taba iya gane masoyi na hakika ba, sai kaddara ta afku ne kawai ake iya gane soyayya ta zahiri da kuma ta karya don hak yanzu ne yafi ko yaushe cncnta na nuna miki soyayya.“ Na daga kaina sama wasu sanyayan hawaye suka gangaro min, ya tako izuwa inda nake ya durkusa ya dafa keken da nake kai yace “Sannan idan zaki 2na na taba gaya miki cewa ba ina sonki don wa abu naki bane ko don moruwar wani abu daga gareki, ina sonki ne a matsayinki na humaira ku zanci gaba da sonki har abada.“ Ya mike tare da duban daddy yace “Idan har ka amince ni zan auri HUMAIRA a haka, zan zauna d ita domin bazan taba guje mata ba har abada. Babu bukatar duniya tasan abnd ya faru da ita bar makiyanmu su sami bakin yi mana dariya. Fuskar daddy tayi saurîn washewa, wani sbn annuri ya saukar mata ya mike tare da cewa “Lall faruk ba‘a banza ba humaira ta yarda da kai yau na gani da idanuna don nayi imanin ko ni ban fik son humaira ba, laifi nane da nayi yunkurin hana abnd Allah ya kadarta.

 Nagode da kayi yunkurin rufa min asiri da kuma masoyiyarka. Lallai samun masoyi kamarka za‘a dade ana tonawa.“ Faruk ya gyara tsayuwa yace “Don na rufawa HUMAIRA asiri ba wata bajinta nayi ba domin kain nayiwa.“ Daddy ya gyara babbar rigarsa yace “idan kuwa har kayi min haka nayi Alkawarin baka dukiya me tarin yawa kuma zan dauki nauyinku kai da ita ba abnd zaku nema ku rasa.“ Faruk ya girgiza kai yace “bana bukatar komai daga gareka indai akan HUMAIRA ne sbd daga ranar da na samu humaira hakkin kula da ita da samar mata da farin ciki akaina yake kuma dole n saukeshi.“ Daddy yayi saurin cewa “uhm!! kaji masoyin gask masoyi na hakika yanzu kai kana ganin a shirye kake??“ Faruk ya gyada kai yace “kwarai kuwa!! abinda kawai nake so a dauke daurin auren daga gobe a matsar zuwa jibi idan zai yiwu.“ Ah! kwarai kuwa sosai ma!! Don dai kwana daya kawai?? Faruk ya kada kansa tare da juyowa muka kurawa juna ido, ni kaina ya bani mafi girman mamaki a yau, domin duk yadda nake hango HALACCIN faru ya wuce nan. DAN HALAK farar fuska farar zuciya. Har yanzu hawaye ke kwararowa daga idanuna ha na fara hango yadda sabuwar rayuwarmu zata kasance duk da cewa bata zo mana a yadda muk so ba. Ya goge hawayen dake idonsa har ya taka izuwa bakin kofa sai ya juyo yace “kayi hakuri amma Sa kasa an kwashe wadancan gardawan banzan daka tara a bakin gate izuwa asibiti sbd ta karfin tsiya na bigesu na shigo nan.“ daddy yayi saurin gyada kai yace “KARKA DAMU KAYI DAI-DAI.“ Ya juya tare da yimin klln karshe ta wani irin salo kmr zaiyi magana amma sai ya fice, nabi daddy d kll na durkusar da kaina na fashe da kuka kmr raina zai fita. Kukan na abubuwa da yawa ne da suka cunkushe zuciyata, ko yunkurin rarrashina ma ba wanda yay zuwa jimawa MUFIDA tazo a lkcn ina daki ta zaun a falo momi ta zayyane mata duk abnd tijjani ya fada da tsananin mamaki ta dago kai tace “amma TIJJANI anyi tsinannen mu2m mara mu2nci da bashi da imani a zcyrsa, ynz momi shikenan komai ya rushe??? Ta girgiza kai tace “FARUK yazo kuma yace yaji y gani ya amince ba abnd za‘a fasa, sai dai nifa ina jin tsoron al‘amarin nan sosai.“ MUFIDA tadan yi gun2n murmushi tare da girgiza kai tace “babu abin tsoro momi, 2nda nake ban taba ganin soyayya irin ta HUMAIRA da FARUK ba, wlh momi yadda kika san da son junansu aka haliccesu 2n fil‘azal. A kyalesu kawai tbbs da abinda Allah yake nufi a tryyrsu.“ Momi ta kauda kanta kawai ba tare data sake cew komai ba, mufida ta mike ta nufo dakina. Kwance nake na kishingida akan makeken gadona na zubawa kafafuna ido hawaye na zuba daga idanuna, mufida tadan rufe min ido tare da bina d kll tace “haba HUMAIRA meye haka?? kuka bashi da wani muhimmanci a gareki sbd bai isa ya dawo miki da abnd kika rasa ba, a zatona farin ciki zan tarar kinayi Allah ya kadarta abnd ki buri.“ ckn sheshsheka nace “Dole nayi kuka sbd shi kadai ne abnd zan iya yi a yanzu, ba haka naso rywr aurenmu tazo mana ba.“ Shi kuma Allah hak yaso. Tayi saurin fada tare da dorawa “Allah na tsara abubuwansa ne yadda yaso ba wanda ya isa ya canjasu, amma dai na tbbtr ko a yayane zakiyi dauwamammen farin ckn zama da faruk wannan kawai ya wadatar.“ Haka dai kalamai irin nata na RARRASHI tayi ta jerowa.

 *Faruk kuwa isarsa gida keda wuya ya fadawa wadda take uwa da ubansa kudirinsa da kuma taimakon da yake so tayi masa, duk da cewa bata fiya fushi ba amma a wannan karon sai data canj Tabishi da kll tace “A zatona kana da hankali amma ka canja. HUMAIRA ce kadai mace a duniya?? ka manta abnd suka yi maka kenan?? sai yanzu da suka shiga wani yanayi sun kada gabas da yamma basu da me rufa musu asiri shine suka taho wurinka kai sbd kafi kowa wauta ka yarda ko?? kai wannan bai zama abin kunya bama a gareka? Mutumin nan bakai kawai ya wulakanta ba harda iyayenka wadanda su zasuyi maka wakilci su ku dame zaka 2nkaresu da yarda su dawo su shige maka gaba?? 2n wuri ka cire wannan daga ranka don bame yiwauwa bane. Fuskarsa ta canja kmr ya fashe da kuka yace “amma ummi mahaifinta ne yayi mana laifi ba humaira ba, ni kuma yanzu humaira nace zan aur ba mahaifinta ba laifin wani yana shafar wani ne?? Ta dan zaro masa ido tace “EH yana shafa! indai ina na isa na fada ka dauka to ka rabu dasu da y‘arsu idan a jibin kake son auren ni ina da wadd zan baka gasu nan da yawa ma.“ Faruk yayi saurin girgiza kai yace “ni HUMAIRA nake so ita zan aura kota yaya ni naji na gani 2nda ni zan zauna da ita.“ Ta daga kai sama tace “TO!! tashi daga kasa ka dawo kan kujera muyi magana 2nda ka zama abokina.“ Ummi ba haka nake nufi ba amma… Ta katseshi da fadin “wai Yaushe ka koyi musu d gardama irin wannan to bani da lkcn musayar zance akan maganar banza tashi ka tafi.“ Dole tasa ya mike ckn nuni da hannu yace “don Allah ummi ki…..“ Ka bacemin nace ko?? Ta katseshi. Ya saki hannunsa kawai ya bita da kallo kawai. “Allah ya wuci zcyrki.“ Ya fada sanda ya wuce izuwa sashinsa, bangaren me zaman kansa da falo guda gefe guda kuma ga dakinsa gdn nasu dai-dai gwargwado na rufin asi ne. Ya zauna jim kadan ya zaro wayarsa ya lalubi lambar bbn abokinsa NAZIR yana dagawa yace “kazo gida don Allah yanzu ina son ganinka, ………..

Ah lfy kadai zo yanzu. ……………. OK sai kazo. Ya mike ya wuce dakinsa min2na kadan yaji motsin zuwan nazir yana fitowa nazir wanda 2ni y dare kujera yace “HUMAIRA!! HUMAIRA!!! kllm zancenka kenan wai da gaske kai ahaka zaka aureta…? Faruk yadan tsaya a hankali ya tako tare da bata rai yace “Eh a hkn ko zaka hana nine??“ Yayi tambayar sanda ya wuce izuwa karshen falo ya dauko lemon juice da kofi ya juyo izuwa inda nazir ke zaune yace “idan munafuncin daya kawoka kenan ka tashi ka tafi.“ Nazir ya warto kofin da faruk ya dora a dan karamin tebirin dake gbnsa ya zuke lemon cknsa yace “haka akeyi? ka gyyceni kuma ka koreni?? kawai dai nayi mamakin yadda kayi haka anya baka nuna rashinzuciya ba??“ Faruk ya grgza kai yace “Nazir ba haka bane ni HUMAIRA bata taba yimin laifi ba, bada yawunta, sonta ko yardarta abubuwan da suka faru suka far ba hasalima jajircewa tayi sai ni sbd tana da yaki akaina, don haka idan na juya mata baya yanzu it nayiwa ba wani ba.“ nazir ya jinjina kai yace “kazo da zance kaima, yn dai me kake so ayi??“ Faruk ya gyara zama yace “So nake pls ka sanar da kowa jibi daurin aurena kowa ya shirya ba, nasanka da zafin nama a shirya komai ckn lkc nasan zai yiwu??“ Ah! kwarai me zai hana?? ai ko gobene bazamu kasa kintsawa ba bare jibi. Faruk ya dago yace “Na sani, zan 2ra maka isassun kudi a account dinka yanzu so nake komai ya kintsu ckn kwana biyu kmr anyi shkr biyu ana shiri, ga mukullin nan (ya jefa masa) na gdna ne nasan kasanshi shima a gyarashi gyara bana wasa ba a shiryashi a kintsashi kada ya ras komai da ake bukata.“ Nazir ya mike tare da sarawa yace “an gama ‘leader‘ yayi kasa da murya yace “amma dai UM fa dole…“ faruk yace “karka damu shawo kanta a guna bam wuya bane kai dai ka zartar da aikinka ka barni d nawa ka hanzarta kaga dare ya taho yi .“ Nazir ya taka kmr zai fita sai kuma ya juyo ya rik baki yace “um!! gskyne gaf kake da kafa record fa saurayin daya zama ango ckn kwana biyu.“ kana gaf da zama MAI GIDA….

Faruk ya nunashi yace “kai! bana son iskanci, na…. yayi kmr zai bishi.“ Nazir ya kyalkyale da dariya ya fice da sauri. Faruk ya koma dknsa. *WASHE GARI da safe faruk ya fito byn ya gama duk abnd zaiyi a falo ya tarar da ita zaune a kujer ya gaisheta ta amsa sama-sama. Faruk ya gyara zamansa yace “Ummi gameda maganar nan ne ta jiya ina so….“ Kace game da maganar banzan nan ce ta jiya, ta mike tare da juyawa zata bar falon, faruk yayi saurin mikewa ya tsaya a gbnta ya saki hawayens data fi tsanar gani fiye da komai ya durkushe bisa gwiwoyinsa yace “Don girman Allah ummi ki taimakeni ki fahimceni, kin sani ban isa na aiwata da komai ba sai da izininki kuma bazan taba bijirewa umarninki ba domin kece komai nawa. Ina so nayi wani abu ne guda daya dazai gyara abubuwa da yawa kuma ya samar da alkhairai da yawa, ciki harda ladan taimakon wanda yake bukatar a taimaka masa wanda kin dade kina kwadaitar dani akan haka, kinsha fada min na zama me juriya da yafiya a koda yaushe. Humaira batayi mana laifin komai ba hasalima keda kanki yabonta kike kuma itama bata so akai mana haka ba idan na gujeta a yanzu ba wani nayiwa ba ita nayiwa, na tbbtr idan na barta zata shiga kangi da takura fiye da ko yaushe a rywrta nasan kuma kema ba zaki so a gujeni don wata kaddara ta fada min ba!!“ Jin tayi shiru yasa ya kara tausasa lafazi yace “2n ba yanzu ba kin dade kina fada min yadda karshe rayuwar masu HALACCI, CIKA ALKAWARI da RIKE AMANA take yin kyau ki taimakeni na zama daya daga cksu don Allah.“ Ta bishi da kll da alama kalamansa sun ratsata ma2ka, da dawo da baya izuwa kan kujerar jim kadan tace “kai yanzu wane shiri kayi?? Shirina bame wuya bane umarninki kawai nake jira. Ina ka shirya kaita to byn auren?? Ta sake tambayarsa. Ya bata amsa da fadin “Gidan da kika fada min cewa shima nawa ne dana gada a wurin mahaifin kuma kika bani mukullinsa da komai nashi da hnnki can zan kata mu zauna idan kin amince.“ Shikenan ya zanyi da yin Allah?? Na amince Allah yasa hkn shi yafi alkhairi. Fuskar faruk tayi gaggawar washewa yayi saurin mikewa ya dawo gbnta ya zauna tare da cewa “Abinda nake so ki fada kenan ummi nasan kuma zaki amince shi yasa nake godewa Allah daya ban ke NA GODE sosai ummina, amma kina ganin su kawu zasu amince kuwa??“ Ba dole ba?? Tayi saurin fada. Kaifa maraya ne kowa so yake yayi maka abnd zaisa kayi farin ciki ko don ya sami lada ka bari zamuyi magana dasu kaje kawai. ckn farin ciki faruk ya fita daga gdn.

 Hakika abnd Allah ya kadarta faruwarsa babu abinda ko wanda ya isa ya dakatar dashi. Da ana SO da ba‘a SO, Ana kuka ko ana dariya, dole aka daura aurena da faruk a ranar da lokacin a kuma inda aka shirya. Ranar da bazan manta da ita ba a rayuwata, daga waje biki yayi armashi ma2ka sbd ba wanda yasa halin da ake ciki, kai ko a gdn wadanda ya zama dole su sani ne kawai suka sani. A gdnmu kam naira jknta ya gaya mata, daddy masu sakin famfon kudi haka kawai ma bare da dalili. Kowa yayi mamakin faruk da irin abubuwan da ya a sannan ne daddy ya tbbtr faruk ba irin talakan da yake tsammani bane!! Washe gari byn komai ya lafa dare nayi aka kaini gdn faruk, gdn sabuwar rayuwa, gdn farin ciki, gd jin dadi da walwala. Ba wasu mutane masu yawa bane suka rakoni hakan yasa ba jimawa kuwa kowa ya watse ya zamana daga ni sai MUFIDA, ina zaune bisa shimfideden gadon da a yanzu nake jinshi fiye dana sarauta ma daya zarce na alfarma. Mufida na zaune sai zuba take ta inda ta shiga ba tanan take fita ba, da yake uztaziyya ce a nasihar tata harda ayoyi da hadisai, maganganun nata na ckn ratsani naji tayi shiru jim kadan ta mike tare da jawo mayafinta da jakarta zata fice, nayi gaggawar dago kai na damko hannunta wasu hawaye sukayi saurin gangaro min nace “MUFIDA kema tafiya zakiyi ki barni ni kadai??“ Ta bini da kallo tausayina ya bayyana karara fuskarta, ta dawo ta zauna gaf dani tace “dole zan tafi sbd nan gdnki ne ba namu ba, gasu can a waje ni kadai suke jira mu tafi FARUK yananan taf KIYI HAKURI.“ Ta banbare hannunta daga nawa ta fice tana waigena. Daga nan sai naji ni a wani irin yanayi, ba wanda zai zauna?? Wace irin rayuwa na shigo kenan?? Kodai basa sona shi yasa kowa ya tafi?? Tunanin da yayi ta yawo a zcyt a wancan lokacin. Hmm da kina tunanin xasutayaki xamane..

 Ina nan zaune ni kadai bisa tsakiyar makeken gadon da nake kai, jikina na sanye da kaya na alfarma kaina na kasa kirjina na dukan uku-uku n rashin sabo. Sallamarsa da naji tasa naji wata nutsuwa tazo mi sautin muryar tasa ya daki kunnuwana kai tsaye y fara zagaye a kwakwalwata, ban dago kai ba shi kuma baiyi magana ba ya zauna ta salo na fuskantar juna ya kura min ido kawai. Na dan dago kai a hankali na dubeshi nayi saurin mayar da kaina, yayi murmushi tare da cewa “yes dago mana ya kika fasa my AMARYA!! kodai tsorona kike ji?? Na girgiza kai nace “Koda ace za‘a wayi gari kow ya zama abin tsoro a gareni na tbbt banda kai.“ To ki dago kanki. Na yace mayafin dake kaina tare da dago kai fuskata wadda hawaye ya gama jikata sharkaf ta bayyana. FARUK yadan yi baya da kansa kmr yaga abin tsoro yace “Kuka kuma??

 Maimakon murna da farin ciki??“ Na girgiza kai ckn sheshsheka nace “ni nafi cncnt nayi kuka fiye da kowa, mafi yawan amare nayin kuka amma na munafunci ne ni kuwa nawa kukan na dolene sbd rayuwa bata zo mana a yadda yakamata ba, laifin me mukaiwa duniya da tayi mana wannan horon FARUK…?? ya kauda kansa tare da cewa “ki daina fadan haka HUMAIRA ba muka iya da yadda Allah ya kaddara, Ai dai gamu a tare matsayin MA‘AURATA wannan shine bbn abu mafi jin dadi daya kamata ki rinka 2nawa. Na kara kasa da murya nace “ma‘auratan mu amma ba kmr saura ba 2nda mu muna da nakasu ta bangarori da yawa kowacce amarya takan zauna ne a tankwashe amma ni kafuna kag a mike suke daga sama har kasa ba wani motsi d zasu iya yi, kaga kenan ni nakasashshiya ba wani amfani da zanyi a garek……“ .
Yadan zaro min ido tare da katseni yace “HUMAIRA!!“. yabini da kallo ya dora da fadin “do Allah ki daina fadar haka, idan baki manta ba a baya na taba sanar dake cewa ba ina sonki ne do bukatuwar samun wani abu daga gareki ba, ina sonki ne a mtsynki na humaira gnnki a kusa dani kawai ya wadatar dani. Kuma ai larurarki ta iya wani lkc ce ba‘a ce ta har abada ba don haka zaki warke kuma muyi rywa kmr sauran MA‘AURATA. Tarayyarmu bata wani dan lkc kankani bace ta har abada ce, babu wani dalili dazai rabamu har abad Ki rinka 2na wannan a koda yaushe.“ Ckn sheshsheka nace “a baya na dade ina hango yadda rayuwar aurenmu zata kasance ckn farin ci walwala da jin dadi sai gashi tazo mana akasin haka, tazo da babban nakasu.“ faruk yace “ki daina kawowa zamanmu babu farin ciki sbd kawai kina da larura, duk inda HUMAIRA da FARUK suka kasance tare akwai tbbcin farin ci a wajen a kowanne irin yanayi ne.“ nadan bishi da kallo nace “Me yasa ka hana a bamu y‘ar aiki da zata taimaka mana, alhalin sani kanka ne ba abnd zan iya yi. Yayi saurin girgiza kai yace “babu bukatar wani ya shigo ckn rayuwarmu ya taimaka mana mu zamu taimaki rayuwarmu da kanmu kuma mu tafiyar da ita yadda muke so, zamuyi zama irin wanda ba‘a taba yin irinsa ba. Na tbbt Allah daya haliccemu zai taimakemu.“ “girki, goge-goge, share-share, wanke-wanke duk waye zaiyi wadannan ayyukan?? Na tambaya ina dubansa. ya mayar min da amsa da cewa “duk nine.“ Idanuna sukayi saurin tafiya yawo sbd AL‘AJABI!!!! kai kuma??

 Naka aikin kuma fa ko shikenan a gida zakayita zama?? “A‘A! aikina yana nan amma bazai shafi wannan ba.“ Wasu sababbin hawaye FIL suka sulalo min. Lallai bana jin za‘a samu mu2m irinka duk duniya!! ka sarayar da hakkinka da duk wani ango ke buri idan yayi aure sannan ka dauki alhakin ai mafi girma akanka duk sbd ni. Ina rokon Allah ya kawo sababin da nima zan nu maka HALACCIN da kayimin duk da nasan zaiyi wuya nayi maka irin abnd kayi min sai dai na kwatanta.“ Na kwantar da kaina bisa cinyoyinsa n fashe da kuka. Mun dau tsawon lkc a haka dakyar faruk ya rarrashe ni na iya yin shiru, da kansa ya tashi ya zubo min abnc ya tilasta min sai da naci sosai. Ya dauke plask din da sauran kayan ya mayar dasu wajensu ya tako a hankali yace “To kinga yanzu lkcn kuka ya wuce ki kwanta kiyi barci isashshe kada kiji komai a gdn masoyinki FARUK kike.. yakai karshen maganar dai-dai sanda ya zauna a dan karamin tebirin dake gefen gadon, nabishi da kallo har yanzu hawayen idona basu kafe ba saim kara gudu da sukeyi. Na dubeshi nace “amma wannan rana tazo mana ba yadda yakamata tazo ba, me yasa ma haka zat faru??…“

Faruk ya dan kauda kai ya dawo ya dubeni yace “ bari!! zakiyi sabo fa! idan kika ce me yasa, kai tsaye Allah kenan fa kike tambaya. Haka Allah ya kadarta mana koda a haka zamu taf har mu2wa ni bani da kaico, kada ki karya zuciyarki da yawa duk wanda yasanki yasanki aka dakakkiyar zuciya me zai hana ki dawo ki cgb da zama a haka??“ Na girgiza kaina nace “zaiyi wuya koda zai yiwu badai a ynz ba.“ Ya bini da dogon kll yadan zunburo baki yace “Zamu bata idan baki daina kuka ba.“ Na goge hawayen idanuna. Yace “yauwa ko kefa?? Sai ki kwanta kiyi barci ki samu isashshen hutu kinji?? Na gyada kai kawai nabi gadon na kwanta nace “kai kuma ina zaka??“ Zanyo alwala nazo nayita sallah na godiya ga ubangijina daya bani ke. Zan bika muyi tare. Na fada ina dubansa. Ya girgiza kai yace “A‘A my amarya aike kina da lalura barci shine mafi dacewa a gareki a yanzu.“ Ka daina kirana da amarya sbd lalura ta hana na amsa wannan sunan, ban kuma san sanda zata barni na warke harna amsa sunan ba. Na fada. Yayi saurin cewa “manta da wannan“ ya jawo bargo ya lullubeni har zuwa wuyana yace “kiyi nutsatstsen barci da safe zaki fada min kalar mafarkin da kikai.“ Yakai maganar murmushi na tashi daga fskrsa, fuskata ta fadada da murmushi nima na gyada kai kawai. Ya juya ya dauro alwala akan idona ya fara sallah sautin kara2n da yake yi yana ratsa kunnuwana har barci ya kwashe ni. *WASHE GARI da asuba faruk ya tasheni nayi sallah a zaune kmr yadda na saba yi barci na koma sbd akwai shi a idona sosai. Misalin 8:15 na safe faruk ya tasheni a karo na biyu, cak ya daukeni ya dôrani bisa kekena ya set kafafuna a matokarar keken dake kasa ya 2rani a hankali muna hira kai tsaye muka fito falo ya wuc dani gefe falon inda aka tanadi wani faffadan tebiri cin abinci zagaye kujeru ya 2rani har izuwa gbn kayataccen tebirin ina zaune bisa keken da aka halitta sbd irinmu. faruk yace “yauwa kinga ke y‘ar baiwa ce ba ruwanki da kujera, ni kuwa bin tebirin kawai nake da kll zagaye yake da abinci kala-kala irinna breakfast kuma dafawar yanzu sai tiriri suke kana gani kasan yanzu aka hada su. ckn AL‘AJABI nace “waye ya dafa duk wannan abubuwan??“

 Yayi murmushi yace “Nine!! kina mamakine??“ Ya fada dai-dai sanda ya ajiye kofin tea a gefena tare da cewa “bismillah! sai ki fara da duk wanda kike so.“ A ido kawai nasan duk abinda ya dafa zasuyi dadi ma2ka sanda nakai bakina dazan hadiye har wani lumshe ido nayi, na bishi da kll nace “a jami‘o‘in koyon girki wacce kayi??“ Yayi dariya yace “A jami‘ar ummina mana, 2n ina yaro tare muke yin komai gashi kuma yanzu haka ya fara amfani.“ Haka dai muka cgb da cin abincin ckn nishadi muna hira har muka gama, faruk ya fara shiga da loko da sakon na gidan. *Haka dai muka cgb da rayuwa har hu2n faruk ya kare ya koma wajen aiki sai ya zamana kafin ya tafi duk abinda zan bukata ya aje minshi bisa faffadan tebirin dake gaf da makeken gadona. Abinci, ruwa, magungunana da komai suna kusa dani sai kuma uwa-uba wayata wadda da ita muk tare a ko yaushe. kllm sai ya dawo ya koma, da la‘asar tayi kuma y dawo gida ya shiga kitchen da kansa ya dafa man abinci.

 A wasu lktn tare muke shiga ina zaune bisa dan kekena muna hira har mu gama hada abnd muke so, rayuwarmu abin sha‘awa ckn sauki muke gudanar da ita cike da walwala da aminci wanda hakan ya samu ne ta silar tsantsar SOYAYYA ta gsky. Anya kuwa..

zata daure..

Mu hadu a kashi na hudu Al’ajabi Part 4.

Leave A Reply

Your email address will not be published.