Al’ajabi Part 4 Hausa Novel

Alajabi part 4 Hausa novel

***** AL’AJABI PART 4 ****

 A wasu lktn idan na dubi a yadda rayuwarmu ke tafiya sai naga kmr a mafarki don ban taba zaton zan tsinci kaina a hali kwatankwacin haka ba, da ace shekaru biyu kacal da suka wuce wani zai fad min cewa haka zata faru koda zai nutse a kasa do rantsuwa bzn yarda ba. Amma gashi na tsinci kaina a wata irin rayuwa daba haka nayi zato ba, sai dai ko ba komai was darussa ne na koya na rayuwa da bazasu taba gushewa daga kwakwalwata ba. *da yake zancen duniya baya buya a ckn dan kankanin lkc maganganu suka fara zagaye gari, nan fa kasuwar gulma da tsegumi ta bude masu mamaki da rike baki nayi masu salati da sallallam nayi, masu jinjinawa faruk nayi masu tausaya mas nayi. A fahimtar wasu kuskure ya tafka babba dazaiyi dana sani a gaba, wasu kuma na kllnsa wanda kuruciya tayiwa yawa. Amma ko kadan bai kula da hkn ba saima kwarin gwuiwa da yake kara samu na kyautata min da nuna min soyayya iyakar iyawarsa, hkn yaba mutane mamaki ma2ka da gaske. Wato ni kaina idan na kalli faruk ina mamakinsa musamman yanzu dana kara kusanta dashi banyi kuskure ba idan nace ba kmr kowa yake ba tbbs shi daban n wanda samun mu2m kmrsa zaiyi wuya.

A kwana a tashi kwanaki sai kara garawa suke zaman mu na kara daukan lkc, syy da kulawa, kauna da shakuwa na daduwa. Mu kadai muke gudanar da rayuwarmu kmr yadda faruk yace haka yake so mu kasance, ko ziyara b wanda ke kawo mana harta da momina sai dai kawai muna yin waya wasu lktn, ba‘a zancen daddy dama amma banga laifinsu ba da wane ido zasu kll faruk?? Wanda suka batawa da mummunan sharri ya sak musu da mafi kyawun alkhairi. hmmm… Abin da kunya ai. **kmr kllm yauma zaune nake bisa gadona na kishingida misalin karfe 4:45 na yammaci tsammanin dawowar faruk kawai nake nama yi mamakin yadda yau bai dawo da wuri ba don maf yawa ana kiran sallar la‘asar yake dawowa, a hakan har barci ya kwasheni. ban jima da tafiya nahiyar baccin ba faruk ya shig da sllmrsa yayi shiru sanda ya tbbtr ba yadda zanyi na amsa don bansan yana yi ba. ya dan tsaya ya bini da kallo kawai murmushi ya tashi daga fuskarsa ya rankwafo tare da sumbatar goshina ya dago yace “ohh!! my lovely wife Allah ya kara miki lfy.“ bai tasheni ba Ya juya ya wuce izuwa bathroom. Byn wasu y‘an min2na na farka, na dubi agogo 5:05 lallai yau faruk ya dade bai dawo ba na fada zuciyata, ta yiwu wani muhimmin abu ne ya tsaya dashi. Nayi saurin bawa kaina tbbs akan haka domin bis al‘ada baya kaiwa haka don wasu lktn ma ana kiran la‘asar yake shigowa. Kmr na kirashi sai kuma na fasa, da yake da wata kishirwa na farka matsowa nayi bakin gadon na jawo ruwan SWAN dake ajiye bisa dogon tebirin dake gefen gadon gaf da fuskar gadon wanda ke dauke da abubuwa da yawa.

Irin daukowar gaggawar da na yiwa robar ruwan yasa ta subuce ta fadi kasa tare da gangarawa nesa sosai da gadon, gashi ina bukatar ruwa sos hakan yasa na matso bakin gadon tare da kwantawa na mika hannuna don dauko robar, sai dai ina!! hannuna ya gaza kaiwa inda take. Nayi iya kokarina na mika hannuna iyakar mikawa amma ya gaza kaiwa, 2nanin dana fara yi shine wai yau nice ga abu ina so amma na gaza iya daukarsa kuma ba wanda zai bani. Musamman idan na 2na rywr baya yadda zan hantara inyi tsawa a aikata min koda ba‘a so sai gashi yau wanda zan yiwa magiya yayi min ma babu shi a kusa. Nayi wani spring ta gefe na koma zaune hawaye wadanda suka zama sabo na suka gangaro min, na zuba tagumi na rasa abnd kemin dadi a duniya. Dai-dai lkcn ne FARUK ya dawo daga inda ya shiga izuwa dakin fuskarsa tayi saurin canjawa ya bini da kallo, jimawa kadan yace “HUMAIRA!!“ firgigit nayi kmr wadda ta farka daga barci muka hada ido, kll daya nayi masa nasan ba yanzu ya dawo ba nayi saurin goge idanuna nace “Uhum!! dama ka dawo??“ Lfy?? meye ya faru kuma?? ya tambaya yana dubana. na girgiza kai nace “uhm..uhm ba komai meka gani??“ Ya tako a hankali yace “koda banga hawaye a idonki ba kll daya zanyi miki nasan da wani abu, abin mamakin min2na 15 da suka wuce ma dana shigo barci kike yi ko kinyi wani mummunan mafarki ne??“ Na girgiza kai alamar a‘a. Ko don ban dawo da wuri ba?? Sake tambaya yana dubana. Nayi saurin sake girgiza kai a karo na biyu. ya bini da kll da fadin “meye ya faru to??“. na dan kauda kaina a hankali nace “ba komai.“ na fada idona nakan robar ruwan data fadi 2n dazu, faruk yabi inda idona yake da kll idonsa yakai ga inda take ya kalleni ya kalli robar tare da takawa ya daukota, ya dawo inda nake da fadin “mu2m najin kishirwa yana ganin ruwa ya gaza samu abin da ciwo kam. Ya zauna a tebirin dake gaf da gadon muka yadda zamu fuskanci juna sosai ya juya ya dauko kofi y tsiyaya min ruwan tare da miko min, ba gardama kuwa na amsa tare dakai kofin bakina na zuke ruwan. yace “abinda yasa ya fada kasa wai yanayi miki nuni da cewa na shigo ne, wanda yakamata ya baki da hannunsa ya shigo don me zaki wahalar da kanki don Allah ki bari faruk ya baki da hannunsa. abinda naji robar na fada kenan yanzu dana daukota.

Duk da gun2n hawayen dake idona saida nayi murmushi har dariya ta kwace min. hmm… me kwantar da hankali yayinda ya tashi kenan. Ya gyara zama yace “idan kina kuka ko sai in rink ganin kamar ba humairar dana sani a baya bace, HUMAIRA y‘ar kwalisa me jin kai da girma da martaba komai nata da isa take yinsa, ga taurin zuciya da juriya komai na kasaita ne. Bata taba karaya bare har tayi kuka hawayenta su zuba, me yasa kika canja???? Na bishi da kll kawai nace “rayuwa ce ta canja ni sbd naga abubuwan AL‘JABI masu yawa da suka koya min darasi a rayuwa wanda indai zan rinka 2nasu hawayena ba zasu daina zuba ba har abada.“ Zasu daina mana. Ya fada tare da cewa “Dole sai kin manta abinda ya wuce zaki samu nutsuwar fuskantar abnd zai z a gaba, kefa daban ce kuma babba ce, mahaifinki babban dan kasuwa me arziki ma2ka, ke kuma kina da baiwar ilmi, fahimta da alfarma me yawa. Na kada kai nace “OK na zaci girman ta bangaren hikima, hazaka, tausayi, alkawari da amana kake nufi dasai ince sai dai kai!! Domin kai sai bayan shekaru ashirin ake sake haihuwar irinka a duniya.(hmm anya kuwa koni abdool aina fishi.) Ya dan daga gira kadan tare da mikewa yadan taka, nace “ina zuwa??“ Ya juyo tare da cewa “zan shiga kitchen baki ga nayi dress din girki.“ nabi y‘ar karamar rigar dake jknsa da kll hade da wando wanda da kadan ya wuce gwiwa, irin kaya nan ne masu yanayin jersey da basu da nauyi sai P-CAP dake sanye akansa 2n daga sama har kas duk launin yellow ne dasu nayi murmushi nace “To a fito lfy amma ka tbbtr ka kula da wuka sbd tana da kaifi, snn ka kula da wuta sbd tana da zafi.“ Ke kuma ki kula da ruwanki sbd kada ya kara fadowa. Ya fada tare da juyawa. Nabishi da kll kawai nadan kada kaina dariya ta kwace min. Ya yaje bakin kofa sai kuma ya juyo tare da takowa yace “my queen me kike sha‘awar ci ne yau??“ kmr bazan ce komai ba sai kuma nace “Fried rice idan ka iya.“ Yadan kara takowa a hankali tare da maimaitawa “fried rice! fried rice!! kai gsky….

“ Rabu dashi kawai kayi koma meye. Nayi saurin fada. Ya girgiza kai tare da cewa “ba za‘ai haka ba 2nda shi kike so to sai mun cishi yau, abnd za‘ai ba dake zamu je kitchen idan ni ban iya ai ke kin iya, sai zama director kina zaune a kekenki na sarauta kina bada umarni. Daga yau kinga nima sai na kara ilmi ko?? Ya karasa fada sanda ya karasa inda kekena yake ya 2roshi dai-dai bakin gadon. Haka kuwa akai a hankali ya 2rani bisa keken izuwa kitchen muka fara aiki. Ina daga zaune ina yi masa nunin abubuwan daz hada don yin fried rice ckn nutsuwa, idan bai gan bama 2rani yake har inda abin yake nayishi da kaina. A haka har muka gama hadawa tare muka dawo izuwa falonmu. Irin wannan shine taimakon kanmu da kanmu da mukeyi kuma muyiwa kanmu komai ba wanda yakeyi mana. Kwanaki nata zuwa suna shudewa sannu a hanka kulawa daga faruk babu alamun raguwa saima karuwa a koda yaushe. **BAYAN SHEKARA DAYA** zai yiwu bazai yiwu ba, zamu jure ba zamu jure b zai iya faruwa ko bazai iya ba da wasu keta cece- kuce duk sai yazo ba yadda da yawan mutane suka zata ba. sai da muka shafe tsawon shekara daya cif a hak yadda muke. Abin sha‘awar babu korafi ko canjin yanayi a tare damu sai ma karin karfin gwiwa da muke samu da kuma tbbs soyayyarmu da tbbs na rayuwa tare ha abada. Wato mun riga mun zama daya na zama faruk ya zama ni domin idan na fahimta dai-dai ko a fusk kamanninmu sun juye sun zama daya. dangane da larura ta A kllm jina nake akwai alam sauki a tattare dani sai dai bana yarda da hakan, yanzu ina jin cewa akwai kafafu a jikina sabanin baya. A kllm kuma sai nake jin suna kara karfi har nakanyi 2nanin me zai hana na gwada mikewa amma idan na 2no da gargadin likita acan baya s na hakura. Abinda na tbbtr shine akwai ranar da zata zo zan mike na tafi akan kafata don na dade da fara jin alamun haka. *Kamar kllm yadda ya saba fita misalin karfe 10:0 na safe ina zaune bisa kekena faruk na tsaye jakarsa na hannuna ya gama shirinsa tsaf zai fita na bishi da kll nace “you look very fresh my life, amma zaman hularka da gyara.

Ya tsugunno dai-dai da fuskata tare da cewa “gyara min dai-dai da yadda kike so.“ Na cire hular a hankali tare da gyara karinta na mayar kansa tare da daidaita zamanta naja hannuna baya tare da lankwasa dan yatsana alam jinjina. Ya mike na mika masa jakarsa da fadin “fatan alkhari, sa‘a, da nasara a gareka mijina.“ Ya karba tare daja da baya yana kllna yace “amee matata, zadai ki iya tuka kanki ki koma daki ko??? Na gyada kai nace “Eh kasan ai keken na zamani ne wanda yake kaima zai iya sarrafashi nayi sa‘a ni gurguwar zamani ce bata daa ba.“ Kidai bi a hankali kinsan KARFEN NASARA….“ Ya fada yana me nuno ni da dan yatsa. Nayi dariya nace “nafa yi karfi yanzu nayi kwari sosai don ni a yanzu ji nake kmr ma zan iya mikewa nayi tfy da kafata.“ FARUK ya girgiza kai yace “habawa!! da saura kad ma kice zaki jaraba don bazai yiwu ba, ko kuma kima gwada 2n yanzu a gabana don ki tbbtr baza iya ba kada ma in tafi ki gwada hakan.“ Na bishi da kll nace “kaban izinin hakan??“ Ya gyada kai tare da matsowa wai kozan fadi ya taroni. Na jinjina kai nadan runtse idona tare da yin bismilla na yunkura a karo na farko na tashi tsay ni kaina bude idona kawai nayi na ganni a tsaye kyam!! Kmr daga sama lkc guda naji karfi ya shiga ckn kafafuna ko don dama rashin motsasu na sawa bana jin karfinsu?? Nan fa fuskar faruk ta fara canjawa yana kllna kawai ckn mamaki. Ni kuwa kawai sai na motsa na daga kafata tare dayin tafiya nayi taku uku akan kasa sannan ne tbbtr da abinda nake zato, tbbs kafafuna sun dade da dawowa dai-dai nice kawai ban sani ba. Sbd AL‘AJABI idanun faruk zarowa sukayi waje kamar zasu fado sai kllna da yake yi ya kasa magana, na dubeshi nace “faruk na warke fa.“

Kara takawa mu gani!! Na daga kafata na taka nayi tfyr dani kaina banyi zato ba naji ni damurmur akan kasa ko alamar la banayi bare na fadi, jina nayi a yanzu tamkar ban taba samun wata matsala ba. Faruk yayi wurgi da jakar hnnsa izuwa kan kujera ya tako izuwa gabana a hnkl bakinsa ya furta sunana “HUMAIRA!!!“ muka rungume juna sbd farin ciki da murna, wasu sanyayan hawaye suka gangaro bisa kuma2na. muka fuskanci juna sautin dariyar farin cknmu me hade da hawaye ta fara tashi, faruk ya goge hawayen kuma2na da hannunsa ya girgiza kai yace “ba lkcn kuka ne yanzu ba, asibiti zamu tafi yanzu don mu sami tbbs daga bakin doctor shiry maza. Faruk har wata y‘ar karamar rudewa yayi, kayan jikinsa ma canjasu yayi yasa wasu. Muna fitowa motarsa muka hau wanda ke kula da gate din gdn ne yake jan motar sbd murna ba zat barshi yayi 2ki ba, da mun hada ido murmushi ke tashi daga fuskokinmu. Ban taba tsintar kaina a farin ciki kmr na yau ba, sai da takai magana ma bama yiwa junanmu sai murmushi sai dariya har muka iso makeken asibitin da shekara daya kenan rabona dashi. Duk inda na kalla a cknsa baya nake 2nowa. salih Ka dan jiramu zamu fito bada jimawa ba, faruk ya fadawa wanda ya jawo motar. To ranka ya dade. Salih ya fada ckn ladabi. Muka juya izuwa ckn asibitin kai tsaye.

 Shekara daya kenan banga wajennan ba, duk inda na baya kawai nake 2nawa sanda aka kawoni magashiyan na rikito daga bene yau kuma gani n dawo da kafata. kai tsaye bangaren da aka kwanta dani shekara daya data wuce sanda larura ta sameni muka wuce, muna isa kuwa aka taremu nan fa wasu likitoci mata su biyu suka sani a daki aka fara gwaje-gwaje da aune-aunen kafata 2n daga sama har kasa, na jima kafin daga bisani su kammala. babban lktn ya umarcemu muje ofis dinsa mu jirashi, haka kuwa akai muka shiga ofis din tare d zama a kujeru biyun dake fuskantarr ta kujerar likitan. Addu‘o‘i kawai nake mai-maitawa a raina Allah yasa karshen matsalarmu yazo gaba daya, Allah yasa muji tbbcin komai ya dai-daita kmr yadda muke da yakini. Bayan tsawon lkcn da muka kwashe a zaune likitan ya shigo da saurinsa tare da yi mana sallama, muka amsa faruk ya mike suka gaisa ckn girmamawa suka zauna a tare. Likitan ya dubemu tare dayin murmushi yace “FARUK*HUMAIRA ko??“ muka gyada kai kawai mudai abnd ya kawo mu kawai muke son ji. ya kada kai tare da zaro wata sabuwar takarda daga gaban aljihunsa ya dubemu ya sake yin murmushi yace “humaira sannu fa, kinsha wahala amma gskyr hausawa da suka ce komai yai farko zaiyi karshe, Allah me magani.“ Muka dubi juna fuskarmu tadan kara saki. Likitan ya gyara zama ya mayar da idanunsa ga faruk yace “a baya kmr yadda mukayi maganar da mahaifinta akan larurar data sameta idan ban manta ba na sanar dashi cewa matsalar data sam bata din-din-din bace lkc zaizo da zata warke kwata-kwata sai dai babu yakinin ko yaushe ne.

Ah wato duk yadda nake da yakini akan cewa zata warke amma ban taba 2nanin abune da zaizo da sauki koda wuri ba. Yadan dakata tare da rike baki kadan yace “Abin y bani mamaki da AL‘AJABI ma2ka da gaske ni kaina ban taba 2nanin zata warke a dan kankanin lkc haka ba, Allah ya nuna ikonsa!! Ina me tayaku murnar kin warke babu wani kafark ta dawo kamar ta kowa kina da damar takata zuw duk inda kike so ba wani sauran ciwo a tare da it Mukayi gaggawar duban juna nida faruk ido cikin ido a hankali murmushi ya fadada a fuskokinmu, faruk ya matso gaban kujerar da yake kai tare da fadin “ina me bakin cikin kasa yi maka komai a matsayinka na wanda ya bani albishir mafi dadi a rayuwata, hakika da ace ni me tarin dukiya ne da kudi yau sai ka gaji da cewa a barsu haka, sai na cika maka harabar gdnka da motoci, na gina mak manyan gdje na gani na fada, kana duk shekara sai kaje aikin hajji da umara. Doctor yayi dariya tare da cewa “faruk kenan da abin dariya kake, yin Allah kenan a kiyasce shekara biyu na daukarwa al‘amarinnan gashi Allah yayi ckn shekara daya kacal.“ yakai karshen maganar yana dubanmu. Faruk ya dubeni mukayi farr da ido a tare muka zarce da yalwataccen murmushi tamkar zamu 2ntsire da dariya. Mun dade munayi masa godiya kafin mu fito. Tare muka jero muna fitowa na ciro wayata na far kiran mufida na sanar mata, jinta kawai nayi amm nasan bata taba farin ckn da tayi yau ba. Muka karasa jkn mota faruk ya dubeni yace “hmm… lallai kina ji da kawarki irin wannan lbrn ba‘a fara sanar da momi ko daddy ba sai ita??? suma duk zasu ji ai lambarta ce ta fara zuwar min a farko. Na fada kawai amma a zuciyata nasan dalili, mufida tayi min halacci duk abnd ya faru baisa ta watsar dani ba tafi kowa kula dani idan ka cire faruk. Tsayar da dan tasi din da faruk yayi ne ya bani mamaki nace “a mota muka zo fa koka manta??“ Ya grgz kai yace “Ina sane kuje gd a wannan motar zan tafi a tasin nan zuwa wajen aiki akwai wani documents da suke nema ni kadai nasan ind yake kinga sun yimin text yafi guda ashirin. Amma faruk…. Ya katseni da fadin “karki damu!! ko awa daya bazan kai ba na dawo gdn, ya juya ga salih yace “ku koma gd nima ina tafe, amma wlh kabi min sarauniyata a hankali. salih yayi murmushi kawai ya amsa da TO.

Bari nayi sauri inje ko?? Ya fada. Na gyada kai kawai na bishi da kallo har yayi gab sai kuma ya dawo ganin kallon da nake masa. Yadai?? menene?? Ya tambaya. Na dan gîrgiza kai nace “ba komai.“ Nayi saurin fada. To jeki ku tafi sai nazo. Ya juya ya shige tasin suka tafi nayi ta kallon motar har sai data bace min. Na juya na shiga motar da muka zo da ita salih y juyata muka bar wajen. Wani iri naji da faruk ya fadi zai je inda ya tafi, amma ai na saba jin haka duk sanda zamu rabu da faruk. hakan yasa na share kawai. Bayan mun iso gd ina isowa dan karamin falonm wani tsallen farin ciki nayi na fada kan kujera. (akwai masu cewa basuga wani part ba da mukawuce me buqata se ya shiga wannan pagedi (y) ßADI ßA RAI. dan samu complete) Rayuwa sabuwa yau akwai shagali, dawowar faruk kawai nake jira. Na tashi na shiga nan na fita nan nayi ta kewaya gidan sai yanzu na kara gane gdn, da yawa sai yanzu naga wasu abubuwan. Na shiga bathroom nayi wanka na fito na caba kwalliya irin wadda na manta rabo na da nayi irinta, jina nake kawai na dawo wata sabuwa. Na wuce kitchen kuma na shirya hadadden girki na dawo falo na zauna na kurawa wani hotonmu nida faruk ido wanda aka hadashi mun yi kyau sosai. Ina nan zaune Bayan akalla min2na talatin wayata tadau ringing na dagota nayi arba da faruk nayi murmushi nace DAN HALAK ina ambatonka a rain kana kirana a waya, na daga nakaita kunnena fuskata cike da annuri. Na karasa kai wayar kunnena yalwataccen murmushi na tashi daga fuskata, sai dai tayi sauri canjawa daga annuri zuwa rashin fahimta sanda naji muryar dana tbbtr ba tashi bace. .

inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un..nafada.

 Na karasa kai wayar kunnena yalwataccen murmushi na tashi daga fuskata, sai dai tayi sauri canjawa daga annuri zuwa rashin fahimta sanda naji muryar dana tbbtr ba tashi bace. Idan har a yadda muka fahimta dai-daine Ga alam kece matar me wayar nan ko?? Ckn y‘an sakannin da yayi na maganar 2n kafin yakai karshe fuskata ta rikide daga yadda take a baya zuwa mummunan yanayin daya wuce misaltawa nayi saurin cewa “Eh…eh nice la..fiya meye ya faru??“ ka2war muryar tamkar ana buga diro dake magan tayi shiru zuwa can tace “To kiyi gaggawar zuwa asibitin SABO TAIWO HOSPITAL mijinki ya samu mummunan accident…“

Iya abnd kunnuwana suka iya jiye min kenan suka dauke dif ma‘ana suka daina jin komai, wani duh ya ziyarci idanuna na daina ganin inda nake tsaye ma bare nesa. Kaina kuwa wata irin juyawa ya far yi kwatankwacin yadda belt din inji ke juyawa sanda yake aiki, wani gumi me zafi ya fara ketowa ta ko‘ina daga jikina tamkar an watsa min ruwan zafi. (wani yasaman yacemin wai ina tsalleke..to ni ba tsallake duk wanda be gani haq qarke to se ya koma ta opera zegani har inda mu ka tsaya..)A tsaye nake na kasa gaba na kasa baya, a takaice dai gaba daya na dauke wuta, ni kaina banyi yunkurin motsawa ba don nasan faduwa ce zata biyo baya saima mika hannuna da nake yi wai ko zanji bango na dafa amma babu. Na shiga yanayi mafi muni 2nda uwata ta haifeni yau sanadin MUMMUNAN ALBISHIR!! Bansan sanda wayar ma dake hannuna ta subuce zuwa kasa ba, tana dira kuwa ta tarwatse komai nata ya rabu da dan uwansa, na dade a tsaye tamkar gunki dafe da kaina dake juyawa. Zuwa jimawa kadan dana ji dan dama-dama na yunkura da karfi daga inda nake tsaye wani jiri ya kwasheni ta gefe nayi kasa sai dai bisa sa‘a jina kawai na fado akan kujera, na dunkule kaina na fashe da kuka hawaye na zuba tamkar ruwan sama. Zaiyi wuya in ban rasa faruk ba. 2nanin da nayi kenan wanda yasa nayi gaggawar mikewa duk da ban gama dawowa dai-dai ba na jawo mayafina, takalmina da mukullin motar faruk duk na rikesu hannuna nayo waje da gudu. Banma yi yunkurin tsaida kukan da nakeyi ba don nasan bame yiwuwar tsayawa bane. ganin a yanayin dana fito yasa salih tasowa tare d tambayar “hajiya lfy?? ya na ganki haka?? me ya faru kike kuka kuma?? Na daga baki dakyar nace “Faruk ne.. sunyi accident yanzu haka suna…asibiti…“ Nakai karshen maganar dakyar. Subhanallahi!! Accident??

 shima ya fada a gigice, hankalinsa ya tashi ma2k Yayi saurin amsar mukullin dake hannuna ya bud min kofar motar, muna shiga ya juyar da ita muka fice. Duk da gudun da salih keyi iya krfnsa amma na raina gudun ji nake kmr na sauka na ruga da gudu, kuka kawai nake rusawa 2n salih na bani hakuri har ya gaji ya daina. Muna isowa harabar asibitin kukana ya karu 2n kafin ya gama tsayawa nayi ready na sauka, yana tsayawa nayi yunkurin fita yayi saurin dakatar dan da fadin “hajiya kiyi hakuri ki rage kukan nan don Allah ki samu nutsuwa ko yayane, dubi yadda kik fa!! Nabi mayafina da takalmina wadanda duk suke rik a hannuna nabi shi da kallo kawai na saki takalmi zuwa kasa na zirashi ckn kafata na yafa mayafin akan kafata kawai nayo waje nayi saurin tsayawa sakamakon motar dana gani a nesa kadan dani n ganeta motar tasin da faruk yahau ce, gaba daya tayi raga-raga lallai ba karamin accident bane. Nan fa na sake rudewa da firgici me tsananin, ‘IHHH!!!! bakina ya furta dai-dai sanda hakorana suka fara karo na sama na dukan na kasa ji kake KAF! KAF! KAF! jikina yadau tsima. nasan zaiyi wuya wanda ke ckn motar nan ya fita da rai, na juya da gudu izuwa ckn asibitin bangaren Emergency na nufa don nasan bazai wuce can ba, 2n kafin na karasa naga an fito da wani daga daki bisa irin gadon nan da ake 2rawa an lullube jikinsa alamun ya mu2. kawai ji nayi kafafuna sun dakata, SHIKENAN!! ya mutu!! kukana ya canja salo, da sauri na tari gaban wadanda ke 2ra dan siririn gadon na dire a gabansa tare da bude mayafin dake rufe da fuskarsa. Nadan yi baya a zaune KAI! ba faruk bane!! na ganeshi direban tasin ne.

Nayi wata juyawa a haka na mike tsaye da gudu na doshi dayan dakin dake kusa da wanda naga a fito da wancan. Kai tsaye na fada da yake dakin nada zurfi zarcew nayi zuwa tsakiyarsa, tfyt tayi saurin cnjw na kom tfy a hankali sabanin gudun da nake yi a baya. Har na karaso gbn gadon da yake kwance, kwanc yake idonsa a rufe tamkar meyin barci gaba daya kansa na nade da farin bandeji, hannunsa dama kafarsa. Numfashinsa na hawa da sauka a hankali, y‘ar farar kyakykyawar fuskarsa na klln sama. Na tsaya akan gadon nasa na zuba masa ido da yanayin da yake ciki, nabi pipe na ledar karin jinin dake jone a jikinsa da kallo sama inda take rataye Wasu hawaye da suka banbanta da nadaa suka zubo min, Bai mutu ba. Abinda na baiwa kaina tbbs kenan. Na cake gwiwoyina a kasa na dora kaina bisa gadon gefensa kadan na zarce da kuka me tsanan wanda duk wanda yaji sai ya tausaya min. Na jima a haka ko sau daya ban dago kai ba, ji kawai nayi an dafa bayana a hnkl na dago kai muka hada ido da wata siririyar farar nurse dake sanye da fararen kaya, tayi murmushi tace “am sorry dan matsa kadan zan cire masa wannan ledar. Na bita da kll da jajayen idanuna kawai na mike wani jiri yaja ni zan fadi nurse din ta taro ni da fadin “hankali zaki fadi fa.“ Na lallaba na zauna a kujerar dake gaf da gadons na kwantar da kaina a jkn bango hawaye suka cg da sintiri a kuma2na. Nurse din ta cire ledar jinin ta jona masa ledar karin ruwa, tadan tako kmr zata wuce sai kuma ta tsaya ta dubeni tace “kiyi hakuri kinji shi ai nashi yazo da sauki ma2ka, karki damu da yawa.“ Takai karshen maganar tare da dafa kafata ta wuce. hmm..

 wane kwantar min da hankali ma zata iya yi?? Tayaya hankalina zai kwanta da wannan bala‘in?? Daga wannan sai wannan, murna ta koma ciki kenan takaici yaci uban nadaa.

 Wannan wace irin KADDARA ce??
wane irin bala‘i ne??
 yaushene zamuyi rayuwa kmr kowa??
ire-iren 2nanin daya mamaye kwakwalwata kenan.

Tunane-tunanen nata karo a ckn kwakwalwata, a haka dai naci gaba da zama a kujerar dake gaf da faruk na zuba tagumi tare da kurawa faruk idanu, ba yanayin da yake ciki yanzu nake kll ba amma ainihinsa nake kallo. kyakykyawar dariyarsa, ingantaccen murmushinsa, da yalwatacciyar fa‘ararsa. Innalillahi wa inna ilaihir-raji‘un. Ko a lbr ban taba jin wadanda masifa ta taso su a gaba kmr mu ba, daga wannan sai wannan?? KADDARA!!! KADDARA!!! KADDARA!!! itace kawai kalmar dake min yawo a zuciyata. Domin idan tazo ba yadda aka iya sai dai ayi hakuri a rungumeta, ji nayi kawai dama banma mike nayi tafiya ba faruk ya fita yayi tafiyarsa tuntuni da duk haka bata faru ba. Amma ya muka iya??? Sai da yamma ta farayi sosai sannan ma nayi wan tunanin sanar da wani halin da ake ciki, sai sanna na 2na inda na jefar da wayata can a gida lkcn dana rude sanda lbrn abnd ya faru ga faruk ya isarmin. Wayar wannan nurse din wadda itace keta zarya akan faruk na ara na kira mufida da nazir bbn abokin faruk da yake umminsa ta tafi umara banyi yunkurin kiranta ba, sai kuma momi dana kira daga karshe. Momi naji ta rafka salati tare da tambayar “subhanallahi!! Wane asibitin??“ muna SABO TAIWO HOSPITAL!! da dan AL‘AJABI ta tambayeni “waye ya daukeki y kaiki can??“ Bata san halin da ake ciki ba, bata san cewa na dawo dai-dai ba zatonta har yanzu ni gurguwa ce Bata samu wata amsa ba saima rushewa dana sake yi da kuka na janye wayar daga kunnena a hnkl, ji nake kmr kaina zai fashe sbd zafi da yayi min.

Mufida ce ta fara zuwa kusan karfe biyar na yammaci lkcn, hankalinta ya tashi ma2ka amma d yake tana da nutsuwa a dan lkc ta fara rarrashina da kalamai masu dadi da saka nutsuwa sai dai ina!! bata sami kaina ba saima wani kuka daya kara turnuke ni. Mufida ta rasa yadda zatai dani tadan rike kafadun tare da cewa “HUMAIRA!! wai me kike so ki zama ne?? Ke ba zaki iya jurar kaddara ba kenan?? Ko kina zaton Haka kawai Allah zai bar bawansa b jarraba ba. kuma gsky ta fada fa 2nda faruk dai ba mutuwa yayi ba amma yakamata tasan ba yadda za‘ai kod ciwon kai ya sami faruk hankalina ya kwanta bare hali irin wannan. daga karshe dai na roketa alfarma da taje gd ta dauko mana wasu abubuwan da zamu bukata, tak mike tare da tambayata ina mukullayen gdn?? Na dan kauda kaina kawai a raina nace gsky wannan ta samu matsala, a ina na sami nutsuwar daukar wani mukulli?? Zuwa jimawa na dubeta da shakakkiyar muryata nace “kije kawai komai a bude yake.“ Ta dan bini da kll kawai tare da girgiza kai cike d tausayawa ta juya ta fice. Naja kujerata izuwa fuskantar faruk nayi tagumi kawai, ji nake inama nice a kwance bashi ba!! Ina ma ni masifa ta riska bashi ba!! ina ma nice hakan ta faru dani bashi ba!! Sai byn wasu lkt mufida ta dawo, nazir da abkn faruk su uku suka zo, momi ma ba shiri ta bazamo. Likitan dake kula da faruk ma yayi bayani gamsashshe daya kwantar min da hankali ma2ka, a cewarsa ‘faruk bai sami wata matsala ba sabod kaf ilahirin jikinsa kalau yake iya kansa ne kawai yadan sami buguwa da karfen motar da sukai hatsari akanta shine ma dalilin saka bandejin dak kansa sbd suna tsammanin ko akwai inda ya fash kuma babu ma hkn yasa bayan wani lokaci suka cire, akwai yiwuwar farfadowarsa nan da wayewar gari.‘ Hakan yasa nadan ji sanyi a raina sosai, tbbs abin yazo da sauki sosai nima na yarda da hakan. Gefe guda momi dasu nazir AL‘AJABI ya ma2kar turnikesu ganin yadda nake taka kafata tamkar ba ba, na fahimci momi nason tambayata shiru dai kawai tayi. Sanda dare ya tsala sannan ne duk suka tafi ya rage ni da faruk kawai sai kayayyakinmu daga gef guda kuma y‘ar hayaniya na tasowa daga waje da yake dakin da muke na musamman ne ba kowa a cknsa sai kuma nurses dake ta kaiwa da komowa don ganin komai ya tafi dai-dai. Na koma daga can gefen gadonsa na shimfida darduma na fara sallolin nafil-fili da addu‘o‘in samun sauki ga abin alfaharina guda daya tak a duniya, Allah yasa yadda muke tsammani ya zam haka ne. Addu‘ar dana kwana inayi kenan don ban iya runtsawa ba a daren.

*WASHE GARI*

misalin karfe 10:00 na safiyar ina zaune a kasa bisa shimfidar da nayi nayi tagumi kawai kusan hankalina baya jikina na tafi duniyar 2nani, gwauron numfashin da aka kawo yasa ni dawowa hayyacina na dago kai da sauri na dubi inda sauti ya fito. FARUK ya farfado!! abnd na fara fada a zuciyata kenan, nayi zumbur na mike na zauna a gefensa. fuskata tadan fara saki sanda na tbbtr da abnd nake zato, a hnkl idanunsa suka bude sosai ya yunkura ya mike zaune wani murmushi hade da hawaye suka ziyarceni nadan kawo gwauron numfashi tare da hada hannuna ckn nasa. Yace “HUMAIRA“ na amsa da “na‘am FARUK!!“

Meya faru dani haka ne?? A ina nake?? kina ina ne ba fitila a inda muke ne?? Nayi saurin sakin hannunsa kirjina ya buga da karfi, kaina ya sara tamkar kwakwalwata zata rushe. Ba kaganni bane?? gani a gabanka. Ya mitstsike idanunsa ya rufesu tare da budewa y grgz kai yace “wallahi bana ganin komai sai duhu, meya faru dani ne haka?? Ya fada yana murza idanunsa. Caraf naji hannuna biyu a kaina sbd tashin hankal na dubeshi sosai idanunsa fa a bude suke garau ba wani ciwo a tare dasu tayaya ma za‘a ce baya ganin komai?? Na fadawa kaina. Faruk da gaske kake?? Ya kara kikkifta yace “na daina gani fa humaira!!“ Ya koma ta baya ya zauna ya dafe kai tare da fadi “YA SALAM!!“ Na daki tsakiyar kaina da karfi na fashe da kuka, wani irin tashi nayo waje da gudu izuwa inda na hakikance nan ne ofis din babban likitan dake kul da wajen, dakyar kuka ya barni na fada masa abn ke faruwa. Da hanzari kuwa ya taso muka dawo dakin ya far jerowa faruk tambayoyi jimawa kadan ya zare glass din dake idonsa yace “innalillahi wa înna ilaihir raji‘un“, ya shafi gashin kansa. Ni kuwa kara kaina nayi a jkn bango kawai naci gaba da dankarar kukana, dai-dai lkcnne momi d daddy suka shigo da sllmrsu. A hankali suka karaso a sanyaye abin mamakine garesu ganin faruk ya mike harma yana a zaune amma ina kuka maimakon murna, lfy meye ya faru?? Daddy yayi saurin fada. Na kasa cewa komai don bakina bazai iya mgn a yanzu ba. Ckn girgiza kai na jimami lktn yace “akwai matsal zancen nan da muke daku patient dinku idanunsa basa iya gani ko kadan, sbd firgita ledar dake hannun momi subucewa tayi. daddy kansa har wani ja baya yayi tare da fadin what?????? Ya daina gani?? To tayaya??? Ka sameni a ofis. likitan ya fada tare da wucewa, jikin daddy yayi sanyi ma2ka musamman daya dubeni ya kuma dubi faruk wanda ke zaune bisa gado, a hankali tamkar wanda kaza ta fashewa a ciki daddy yabi bayan likitan momi kuwa zama kawai tayi a zuba tagumi. *doctor tayaya idanun mu2m zasu daina gani alhalin suna a bude lfy ba abinda ya samesu??

 Tambayar da daddy ya fara jefawa likitan kenan. ya gyara zama tare da cewa “wato Alhaji gani bawai ya ta‘allaka akan ido ne kawai ba amma kwakwalwa ita ke taka rawa wajen tbbtr da ganin…“ Tayaya?? Daddy yayi saurin katseshi. likitan ya dora da fadin “ta hanyar jijiyar dake sanar mata cewa ido yaga wani abu sannan ta tantance me aka gani din, ba ido kawai ba harta kunne idan magana ta shigeshi sai an sanarwa da kwakwalwa cewa anji wata magana ta tantance abnd aka ji snn a gane anji maganar. Duk sanda aka ce jijiyar dake sanarwa kwakwalwa wani abu da aka gani ta sami matsala to tbbs makanta ta samu kmr yadda nake da tbbcin abind ya faru gareshi kenan ta silar buguwar da yayi akai. daddy ya kauda kai ckn mamaki da fadin “buguw akai matsala a ido.“ Kwarai kuwa “sbd abin ya taba mahadar idanun d kwakwalwa ne. Daddy ya dan dafa tebirin dake gbnsa yace “kaga doctor yaron nan mijin y‘ata ne a shirye nake na biya ko nawa ne akansa, abinyi??“ farin siririn likitan ya grgz kai tare da cewa “ba wani abinyi Alhaji sbd shi sha‘anin kwakwalwa ba yadda aka iya sai dai a tsaya aga ikon Allah kawa Allah me yadda yaso wai a kasa da 24hrs me gan ya zama makaho. A snyyn da naga daddy ya dawo ne yasa ni matsowa izuwa inda yake nasha gbnsa tare da fadin “Shikenan ya makance ko?? ya daina gani har abada?? Ya zama…. Na kasa karasa maganar ta sarke min, lkc guda wata bugawa da kaina yayi yasa na sulale kasa sumammiya.

 ******* Nan fa hankalin kowa ya kara tashi komai ya kara rikicewa, sai dana shafe tsawon lkc bansan a inda kaina yake ba. A cinyar momi na farfado mufida na tsaye a kaina tana yimin fifita, na cilla idanuna sashe zuwa sas lkc guda na dago kaina izuwa mikewa zaune na zarce da kuka. Momi ta jawoni jikinta ta fara rarrashina, daddy da sauran mutane na zazzaune kowa ya zuba tagumi suma suka shiga bani baki ciki akan kaddara idan tazo ba yadda aka iya da ita. *Kwanaki biyu kacal muka shafe aka sallame mu muka bar asibitin muka koma gida, daga nan ne kuma wata sabuwar dagulalliyar rayuwa ta fara, abubuwa da yawa suka sauya izuwa bai-bai ba yadda suke tafiya a baya ba. Aikin da faruk keyi dole tasa ya hakura domin bazai yiwu babu idanu ba kuma gashi ba kmr aiki gwamnati ba aikine da idan zaka iya ayi dakai ida ba zaka iya ba shikenan an ajeka babu saran samun komai, gashi kuma ummin faruk bata nan kuma duk wasu kadarori da dan abinda faruk ked shi suna hannunta. Hakan yasa a dan kankanin lkc muka fara shiga matsanancin yanayi sai da takai wani lkcn abinci ma dakyar muke ci, wani lkcn sai dai abokan faru su taimaka mana. Ina son na sanar da daddy don ya taimaka mana amma faruk yace Na bari kawai mu kara hakuri umminsa na gaf da dawowa komai zaizo karshe, kuma dai nima din bana son sanar musu sbd ina tsoron abnd ka iya biyo baya. Kamar yadda na saba ina ckn kitchen ina sarrafa dan abnd zamu ci na tsaye nake na dafa wani tabl dake gabana na tafi duniyar dana saba zuwa wato TUNANI, gaba daya hankalina ba‘a kan girkin ma da nakeyi yake ba. alamun zamewa data faduwar da naji yasa na dawo hayyacina tare dayo waje d sauri izuwa falon, abnd kuwa nake zatone faruk n sai dai baije kasa duka ba. Nayi saurin rike hannunsa nace “sannu! baka ji ciwo badai??“

Ya danyi murmushi tare da fadin “Ah ba abnd naji karki damu.“ Ya mike tsaye. Na jawo yar karamar bakar sandarsa na makala a hannunsa muka tsaya a haka nace “kayi hakuri laifinane danayi nisa ban dawo da wuri ba. Harka gaji da zaman kadaici kayi yunkurin fitowa. Ya grgz kai tare da yin murmushin da koda yaushe kuma a ko wane yanayi ya saba yi yace “baki da laifi nine da karambani.“ Nayi masa jagora izuwa kan kujera na dubeshi nace “bari naje kitchen ko?? mintu biyu kawai. Ya gyada kai kawai, Na mike na koma. Bayan na gama ne na zubo abincin wani dan plat na dawo falon. Zaune muke faruk nacin abncn muna hira ckn nutsuwa, mun fuskanci juna ina lura da yadda ya kai abncn bakinsa. Ya dago kai yace “da alama fa ba cin abncn nan kike ba??“ uhm! so nake kai dai ka gama tukunna.“ yayi shiru zuwa can ya grgz kai yace “HUMAIRA ina tausayinki gsky kina shan wahala ba karama ba…“ Nayi saurin katseshi nace “ka daina fadan haka don Allah, abnd nake yima ne zai zama wahala?? Ban taba klln abinda zanyi maka a matsayin me wahala ba koyaya yake kuwa sbd ka cncnci fiye d haka, Zanci gaba kuma da yima iya iyawata har abada.“ Yayi murmushi kawai kmr zai ce wani abu sai na kautar da maganar da wani zancen. Bayan ya gama ne na jawo jarida sabuwa na fara karanta masa halin da duniya ke ciki, idan muka zo kan wani lbrn na ban dariya muyi tare. Sallamar da muka ji ce ta dawo da hankalinmu, gabana ya fadi da naga momi ta tsaya tana yi mana wani kallo ta tako a hankali izuwa ciki. Sannu da zuwa momi!! Na fada dai-dai sanda faruk yayi saurin sakin fusk da fadin “Ah! momi ce sannu da zuwa.“ A ynyn fuskarta nasan da matsala, sama-sama suka gaisa da faruk na tashi nayi masa jagora izuwa daki na dawo falon na zauna. KE HUMAIRA!!!!! momi ta fada sanda ta gyara zamanta a kjrr da take zaune tare da dubana sosai. Na dago kai nace “Na‘am“. Momi tace “Wai baki da lafiyane naga duk kin wa rame kin kanjame kin lalace??“ Na dan dubi jikina nace “rama kuma?? lfyta kalau momi ba abnd ke damuna.“ Ah karya kike akwai, idan ba rashin lfy ba to yunwa ko wahala akwai daya.“ hmm… Na gama gane inda ta dosa, na grgz kai nace “ni dai-dai nake kuma ina ckn farin ciki sosai.“ Karya kike akwai wani abu, kodai baki da lfy ko kuma akwai yunwa a tare dake ko kuma wahala tsanani. Na bita da kll kawai, ta dora da cewa “tsakaninki da Allah kina cin abinci sau uku a rana??“ Kina samun cikakken hutu koda na awa biyu ne a rana?? Kina samun wani farin ciki a irin wannan zaman?? Nadan yi baya da kaina nace “To momi meya kawo wadannan tambayoyin kuma?? Koda ina samu ko bana samu nan fa gdn mijina n ina da inda yafi nan ne??“ Kina dashi.

 Tayi saurin cewa ta zarce da fadin “Duk zaman dazai zama da kwarar juna irin wannan to bashi d wani amfani don haka dole a samu mafita akan haka don ba zamu zuba ido wahala na neman kasheki a banza ba.“ Wani takaici ya rufeni na dauke kaina nace “Banyi zaton jin haka daga gareki ba ko kadan, a zatona kwarin gwiwa zaki bani akan kula da faruk amma ba wadannan maganganun ba. Haba momi faruk fa!! Eh naji faruk sai me?? Ta fada tana dubana. Na grgz kai nace “Toni bana daga ckn butulu masu manta alheri a dan kankanin lkc, nidai naji na gani kuma na gamsu zan iya koda kuwa zan mu2 ne akan haka. Momi tace “ke yarinyace da kike da kuruciyarki sosai kula da makaho a gurinki ba karamar masif bace da zata iya sawa ki tsufa 2n kina yarinya kada ki cuci kanki munyi magana da daddynki dole ma asan abinyi. Idanuna suka zaro waje kmr zasu fado, abnd na dade ina tsoro kenan nasan zaiyi wuya hakan bat faru ba. Na sauka daga kan kujerar da nake na sauka kas na kwantar da muryata nace “Momi kada kuyi hak don Allah, ki 2na abinda faruk yayi mana bai kamata muyi masa haka ba, ni zan jure koma menene. Momi ta mike tace “kinga ana auna me zai zo ne gaba ba abnd ya wuce ba, ba wanda zai yarda yabar y‘arsa me gata gaba da baya a yanayin da kike ciki da sake.“ Momi ki tsaya ki fahimceni. Na fahimceki mana amma kiyi fatan daddynki ya fahimceki idan ya ganki a wannan yanayin. Ta fada tare da juyawa ta fice. Na koma da baya na jingina da kujerar dake bayana, tunane-tunane suka fara kaiwa da komow a zucita. Abu daya dana sani duk rintsi ba wani dalili dazaisa na rabu da faruk. (Hmm za’ai butulci kenan) Abin ya ma2kar dauremin kai, banyi tsammanin ji haka daga momi a dan kankanin lkc haka ba. Na dade a zaune nayi tagumi kawai abin duniya y isheni, dakyar na iya mikewa na koma daki, faruk na kishingide akan gado idonsa dake sanye da bakin glass na klln sama. Na zauna gaf dashi, meye kike kuka?? Ya tambaya. Nima nayi saurin tambayarsa da cewa “kuka kuma??“ Na shafa kuma2na, yes gsky ya fada akwai haway na grgz kai nace “ba kuka nake ba.“ Ya za‘ai momi tazo da magana me zafi, daci da ciwo irin wannan kice ba zakiyi kuka ba?? ya sake jefo min tambaya. Na kauda kaina a zcyt nace “dama yaji abnd ya faru??“ Ya sauke kansa kasa yace “Watakila shikenan lkcn rabuwarmu yazo, duk ginin da mukai a baya ya rushe!!

 Sababbin hawaye sukayi saurin gangaromin, na kwantar da murya nace “Faruk idan kana fadan haka sai nayi zaton ko baka da kwarin gwiwa akaina ne, ina so ka yarda ba abnd zai rabamu har abada. Ka yarda da haka. muka danyi shiru na wani lkc y gyada kai tare da cewa “Na dade da yarda amma akwai tarin kalubale akan yiwuwar hakan. Sautin kukana ya sake fitowa na kwantar da kaina kawai. *BAYAN KWANAKI UKU* Misalin karfe takwas na dare bayan mun gama komai faruk ya dubeni yace “kyau kije ki kwanta k huta duk yau fa baki samu wani hu2 ba, na kada kai nace “badai ina tare da kai ba?? Shine morewar tawa ai.“ Duk da haka dai hutu ma wani abu ne. ya fada. duk da bana son tashi amma sai da ya lallabeni n mike na tafi daki, da yake a gajiye nake sosai ina kwanciya barci ya kwasheni. Faruk na zaune jim kadan da tashi na kamar daga sama daddy ya fado da zazzafar sallamarsa data sanya faruk saurin dagowa bai iya amsawa ba har sai da daddy ya zauna. Sannu da zuwa Alhaji. Ya gyara zama sosai akan kujera ckn gadara yace “Yauwa“. Shiru ya gudana tsakaninsu nadan lkc zuwa can faruk yadanyi kmr zai mike tare da cewa “bari na taso humairan tana ciki. A‘A yayi saurin dakatar dashi kana yace “Wajenka nazo ba ita ba.“ A hnkl faruk ya koma ya zauna tare da cewa Allah yasa dai lfy? Ka taba ganina a gdnku?? daddy ya tambaya ya dora da fadin “To 2nda ka ganni yau ka hakikance dole da dalili.“ Yadanyi shiru yabi da komai da komai na falon d kallo a wulakance yace “Ah duk halin da ake ciki lbr yazo kunnena kuma banyi mamaki ba don nasan dole haka zata faru. Sanin kanka ne yanzu ka zama misaki, nakasashshe kuma makaho ba abinda kake iya yiwa kanka bare kayiwa wani ba. Hakan yasa ba zaka iya rike humaira ba a halin d kake ciki kuma kai kanka kasan haka, Naso ace k zauna na har abada sbd yadda kuke son junanku musamman irin halaccin da kayi mata to amma magana ta gsky hakan ba zata samu ba. A matsayinmu na iyayenta ba zamu zuba ido mun gani y‘armu ta kaskance ta lalace karshe ta mu2 wahale ba. Don haka ina me umartarka da lallai ka sawwakew humaira ba tare da bata lkc ko jinkiri ba.“ sbd grgz a firgice faruk ya dago kai duk da ba iya ganin komai yake ba amma sai daya mayar da fuskarsa zuwa inda yake 2nanin cewa anan daddy ke zaune, fuskarsa ta canja ma2ka bakinsa na raw yace “Alhaji! wannan maganar da kazo min da ita ta ma2kar gigitani!! Don girman Allah ka taimakeni kada ka rabani da humaira, duk duniya Allah ne gatana humaira ce gatana ita kadai ke taimako na don Allah….“

Wannan ba wani abin damuwa bane, akwai kudi dazan baka wadanda sun isheka ka auri mata hud ma idan kana so su kula dakai nidai bukatata ka sakar min y‘ata ban haifeta don irin wannan wahalar ba. daddy ya fada. Faruk ya grgz kai yace “kome zaka bani kuma komai yawansa baikai muhimmanci da kimar humaira a idona ba kuma idan ina dashi zan iya sadaukar dashi akanta, ka rike koma meye nidai k barmu tare don Allah.“ daddy ya kara bata rai yace “bawai nazo ne muyi wani doguwar muhawara dakai ba so nake yadda kazo gida na dauki y‘ata na baka to ka dawo min da y‘ata gida.“ faruk ya grgz kai yace “To kuwa bazan taba iya yi abnd kake so ba.“ Da sauri daddy ya dubi faruk ya maimaita abnd ya fada ckn salona tambaya, kace ba zaka iya ba?? daddy ya mike tare da cewa “kuskure mafi grm d zakai a rywrk shine kaki sakar min y‘ata.Dama ca ba tsararka bace na amince ka auretane kawai sb irin larurar data shiga amma kaima kasani badon ka cancanta ka aureta bane. Na baka 24hrs kacal lallai ka dawo min da y‘ata gida ko kuma kaga abnd zanyi maka. Idan kunne yaji……“ Ya juya ya fice. Faruk ya dafe kai ckn tsananin takaici innalillahi…… bakinsa yama gaza kai karshen addu‘ar daya faro. Yadau tsawon lkc a zaune bayan tsawon min2na ne kuma ya lalubi sandarsa tare da mikewa ya taho a hankali ya shigo daki, takun tafiyarsa ne ya tasheni daga barcin da nake, nayi saurin tashi na bishi da kll, duk da yadda yake so ya boye damuwar dake ransa sai data fito. Yana zama na fara da tambayarsa “meye ya faru kuma??“ Yadanyi yake da cewa “kinga wani abune??“ Na gyada kai nace “tbbs akwai damuwa.“ Ya dan gyara zama yace “daddynki ne yazo!!“ Nayi saurin zabura, daddy?? me yace?? Ya kukai dashi?? faruk ya grgz kai yace “bai kamata kiji ba sbd bashi da dadin ji.“ Na sani abu me dadi bazai kawo daddy ckn gdn nan ba amma duk da haka zanso ji, don Allah me yace?? Kmr bazai ce komai ba zuwa can yace “Ya bani wa‘adin awanni 24 lallai na….“ 2n kafin ya karasa na katseshi da cewa “awanni 24??“ hmm..

Tayaya yake zaton zama na har abada za‘a kawo karshensa ckn awa 24?? Kayi hakuri mijina wannan tatsuniyace kawai.“ Duk da yadda naso na nuna ba wani damuwa amma ni kaina a zuciyata nasan karya nake, bansan yadda zanyi da wannan kalar masifar data sake tinkaromu. *** Sai byn kwanaki biyu da yammaci muna zaun da faruk muna hira, kamar dirar mikiya daddy ya fado, juyowa daya nayi muka hada ido naja da baya a tsorace tare da cewa “Innalillahi!!“ Meye?? waye?? faruk ya tambaya. Ubankane!!!!! Daddy yayi saurin fada 2n kafin nace komai. Me nace maka?? Yaya mukai dakai?? ya tambayi faruk yana dubansa a fusace, ya dora da fadin “to yau ko kana so ko baka so sai y‘ata ta dawo gida tare muke da yan sanda na shigar d kararka sai munyi shari‘a dakai. ya juyo gareni ckn tsawa yace “uban me kike yi anan?? wuce mu tafi.“ wayyo faruq kadebo ruwan dafa kanka..!

 A maimakon na iya cika umarnin da daddy ke bani sai na tsaya ina binshi da kallo kawai, idan na dubeshi sai kuma na juya na dubi faruk dake tsaye ya kasa cewa komai na tbbtr kunnuwansa a bude suke yaji abnd zan iya yi. Alkawarin dana daukarwa kaina na kasancewa da faruk a duk yanayin da yake ciki yasa duk wani tsoro yakau daga zcyta, ni ban wuce na tafi kmr yadda daddy ke cewa ba kuma bance komai ba har sai daya kara buga min tsawa a karona biyu. “Ki wuce mu tafi nace“. Maganar ta daki kwakwalwata, yaune karon farko da daddy ke daka min tsawa kai tsaye haka amma maimakon na firgita sai na kara gyara tsayuwa ma na tsaya kyam nace “daddy! ka dubi grmn Allah da manzonsa karkayiwa faruk haka, ka 2na sanda ya taimakemu ya rufa maka asiri kai kanka dani daduk danginmu, me yasa yanzu mu kuma ba zamu saka masa ba?? Idan wai don ni kakeyi don ka samar min da farin ciki ka rabani da wahala, to ka barni kawai sbd ni farin cikina anan gdn yake, faruk mijina ne har gobe kuma zan iya zama dashi a kowanne yanayi.“

 Daddy ya zaromin ido yace “gsky na yarda baki da hankali, banda haukanki ina ke ina zama da nakasashshe makaho?? Abin kunyane ma ace kmr ni y‘ata mijinta makaho ne, abnd yayi mana a baya ya wuce mu gaba muke hange idan ke baki da 2nani mu muna dashi kuma bazamu bari wahala ta kasheki a banza ba, ki wuce nace!!“ Fuskata ta canja ma2ka naja da baya nace “Ina me baka hakurin cewa wlh ba inda zanje ba yadda za‘ai na tafi nabar gdn mijina wanda yaso ni sanda kowa ya gujeni yake kyamatata, kuma ba akan wani dalili ba.“ Cikin tsananin AL‘AJABI daddy ya bini da kallo yace “Ni kike gayawa haka??“ Ba tare da tsoro ba nace “Kayi hakuri amma ya zama dole in fadi hakan sbd kokoluwar butulci ne abnd kake so kuma banyi halacci ba idan nayi haka, na zabi na zauna anan har mu2wa tazo ta riskeni.“ Kin zabi wannan makahon akan mu iyayenki?? Daddy ya fada yana me nuno ni. Na gyada kai nace “Eh! haka nake nufi sbd mijina ne ko a wajen Allah hakkinsa a yanzu yafi naku. Hakanan dady yajuya yatafi tare da gargadin bani basu.

faruk ne xaune abakin gado yana tatunanin dani kaina bansan me yake tunawaba.. Gyaran murya yayi alamun yanason yace wani abu naisaurin dago dakaina..yace HUMAIRAH.!! Nace na’am yace kishirya gobe zamuje gidanku.”! Yinme? natan bayeshi..zamuje muba dady haquri akan abin daya faru.. Da SAFE WAJEN KARFE 10;00 ranar asabr….. Tsawon min2na talatin muka dauka sannan muka gama shirye-shiryen tafiya, abinda ya bani mamaki yadda faruk keyi tamkar zamu inda ba zamu dawo ba. Bayan mun gama kuma yace na rufe duk wasu kofofin gidan na ko‘ina, cikin rashin fahimta nace “wai faruk ina zamu ne?? Ina tsammanin cewa kayi gdnmu zamu mu dawo?? Meye kuma na sai mun garkame kofofi?? Faruk yadan hade fuska yace “ba gdnku zamu ba siyar dake zanje inyi.“ Duk da yanayin da nake ciki sai da nayi dariya na kada kai tare da cewa “Ba haka nake nufi ba faruk abin ne kawai ke bani mamaki,“Na dan taka daga gbnsa izuwa kan kujerar da hijabina yake, na kara yin dariya a karona biyu nace “wai ka siyar dani, ashema zaka iya siyar da kanka kenan??“ Naja sandarsa muka wuce kai tsaye izuwa waje tare da cgb da hira har muka fito izuwa harabar gdn muka zarce izuwa inda motar faruk take, na budewa faruk kofar ya shiga na mayar na rufe tare da zagayawa na shiga na tuka motar muka tafi.

Ckn nishadi muke tafiya ina sanar dashi duk wani wuri da muka gifta ko wani abu daya faru dai-dai sanda zamu gifta, a haka har muka iso tsaleliyar katafariyar unguwar, SARAUNIYA STREET!! makeken Allon dake kafe yayi mana maraba. 2n daga nan fuskata ta fara canjawa shekara daya curr kenan rabona da mahaifata na fara tuno rayuwar data faru dani a baya, na fara 2no lokutan baya sanda a wannan hanyar ake tukani a tsaleliyar mota, sanda nake takama ina fankama, nake ji da kaina. Ba yanzu da rayuwa ta canja ni ta karfin tsiya ba. A hankali muka cgb da ratsa kyawawan gine-ginen dake hamshakiyar unguwar da duk wanda ka gani a cknta to ya wuce raini, har muka iso tsalelen gdn namu. hmm… birki naci kawai a gbn gidan ina kallonsa, da ace wani zaizo wucewa yaga motar danake cknta da yadda na koma idan zanyi rantsuwa nan gdnmu ne bazai yarda ba. A hankali na danna worn har sau uku a hankali karamar kofar ta bude me bude gate din yabi motarmu da wani wulakantaccen kallo naji sanda kasa-kasa yake cewa “Bafa kowanne talaka ke shiga gdn nan ba.“ Waye ne?? Ya tambaya. Na sauke glass din motar a hnkl na leko da kaina waje, 2n kafin nace komai yaja da baya adan tsorace ‘ranki ya dade!!‘ Ya juya da sauri ya koma, jim kadan tafkeken gate din ya fara budewa. Naja motar izuwa harabar gdn nayi parking tare da fitowa ina me bin harabar gdn da kll sashe zuwa sashe. Abubuwa da yawa suka fara dawo min, duk inda na kalla sai wani abu ya fado min wanda faru a dai-dai wajen. Idona ya ciko da kwalla. Dai-dai lkcn ne faruk ya fito daga ckn motar wanda hakan ya dawo da hankalina gareshi na tako naja sandarsa muka nufi ckn gdn. Ma‘aikatan gdn kuwa sunyi dandazo sai gaisheni suke duk wanda na gifta ta kusa dashi, wasu ma harna fara manta sunansu. Da sallamarmu muka shigo tafkeken kayataccen falon, ba kowa sai hafsa y‘ar aiki tsaye a gbn plasma dake kafe tana y‘an goge-goge. Ta amsa sllmr tare da juyowa muna hada ido ta dafe kirji, LAH! aunty humaira!.

Hajiya! Hajiya!! Ga humaira tazo. Da sauri momi tare da daddy suka fito, momi ta dubeta tace “meye??“ hafsa tayi nuni damu. Dukkansu sukai turus suna kllnmu, momi ta dubi hafsa tace “To na gansu jeki.“ Hafsa ta ajiye duster dake hannunta ta juya tare dan dago min hannu tana murmushi, na gyada mata kai kawai ta fice. Daddy wanda ya kllmu ya dauke kai yaci gaba da gyara maballin rigarsa lkc guda ya dago kai ckn tsawa yace “uban me kuka zo yimin a gd?? Meya kawo ku??“ Na dan kara matsawa gaf da faruk nace “ka fada masa abnd kace kazo ka sanar masa kawai mu tafi.“ Faruk ya gyara tsayuwa yace “Zuwa nayi don na sanar dakai abnd nasan dole sai kayi dariya, abnd nasan shi kake so kaji kuma shi kake so ya faru. Insha-Allahu daga yau ka daina tsanata kuma komai yazo karshe.“ Faruk yaja hannuna izuwa kan kujera muka zauna. Momi da daddy ma suka zauna kunnuwanmu duk a bude so muke kawai muji me faruk zai fada. faruk yace “Alhaji na sani duk duniya ba wanda kake so kamar y‘arka guda daya wato humaira, sannan kuma ba wanda ka tsana kmr ni faruk sbd dalilai da yawa, musamman yanzu da dalili me karfi ya karu akan nada. Banga laifinka ba don kana son kwatowa y‘arka yanci donta rayu ckn rayuwa me dadi da nayi 2nani ma sai naga hakika kafini gsky. Nayi iya nazarin da zanyi na gano cewa zamana da humaira babu komai a ciki face takaici da damuwa….“ Na katseshi da karfi nace “FARUK!!“ ya daga min hannu da fadin ‘ HUMAIRA! minti daya.‘ ya dora da cewa “akwai cutarwa kwarai kmr yadda kake fada idan naci gaba da zama da humaira a haka kuma nima bazan so ta rayu har ta mu2 da bakin ciki ba don haka gata na dawo maka da ita har gida kmr yadda ka nema kuma zan tafi na…..“

 Nayi saurin mikewa tsaye nayi dawurwura a guri daya naja da baya da sauri na fizgo wata sharbebiyar wuka na dan yanki hannuna kadan jini yayi tsartuwa kai tsaye na wuce da ita wuyana. daddy da momi suka mike da sauri tare da zaro ido, momi tadanyi kara da fadin “iohhh!!!!! humai…“ Faruk ya mike tare da cewa “humaira me kika dauka??“ Ba tare da tsoro ba nace “WUKA!! wuka ce faruk! kuma zan kashe kaina idan har ka tafi ka barni.“ Ya tako izuwa inda yake jin motsina ya tsaya cak a gabana yace “Karkiyi haka!! duk tsananin tashin hankali da ukuba kada kiyi yunkurin kashe kanki domin tashin hankalin da zaki tarar yafi wannan, zaifi ki nemi wata mafitar amma ba wannan ba. Ya miko hannunsa tare da cewa “bani wukar.“ Nabi fuskarsa da kallo wadda keda tasirin saurin sani ko hanani da kallo na saki wuka kasa na rike hannunsa nace “Karkayimin haka?? Nice fa humaira koka manta ne?? Kace ba zaka tafi ba don Allah kaji?? Kace da wasa kake faruk!! Ya banbare hannuna daga nasa yaja da baya yace “bakin alkalami ya bushe ba yadda muka iya, don kin rabu dani ba yana nufin shikenan ba. Kece dai humairar nan ta baya zaki samu wanda yafini kiyi rayuwar farin ciki. Ki manta da ba2na kawai ki dauka baki sanni ba a rywrki ki shimfida sbwr ryw, nina tafi.“ Ya kai karshen maganar ya juya ya nufi hanyar fita..

Natausayama faruq..!

Daddy yace “Yayi kyau faruk kuma ka birgeni akwai kudin da nayi maka alkawari zan baka ka tsaya ka karbi cheque din.“ Faruk ya juyo hawaye suka kwararo ta kasan glass din dake sanye a idonsa yace “ka rike kudinka bana bukata.“ Ya sake binmu da kallo wanda ya kara rikitani ya juya ya fice. Innalillahi wa inna ilaihir-raji‘un. Abin da AL‘AJABI sai kace almara!! Faruk da kansa ke furta rabuwa dani?? Da kafarsa zai fita daga inda nake?? Idona yakai ga fuskar daddy wanda keta murmushi yana annashuwa. Da sauri na nufi hanyar fita inda faruk yabi nabi bynsa duk da kiran dasu momi keyi min baisa na dakata ba. A guje na karaso inda yake tuni har ya fito harabar gdn duk da cewa da ma‘aikata masu yawa suna ta kaiwa da komowa bai hanani tarar gbnsa ba, na rike sandar dake hannunsa zafafan hawaye suka kwararo da idanuna ckn sheshshekar kuka nace “Faruk kana nema rana ka cnz min daga hakikanin yadda nasanka izuwa wani daban, ko a mafarki ban zaci haka daga gareka ba.

 Yanzu ma a haka tayaya zaka tafi?? Faruk ya grgz kai yace “indai don ta tfy ne karki damu na tbbtr salih yazo?? Yayi nuni da inda motar da muka zo take. Na juya na kll inda ya nuna, kwarai yazo kuwa. zcyt ta fada min. Ya dora da fadin “Na gaya masa dama ya biyo bynmu zai daukeni ban bari kin sani bane sbd kada ki gane akwai wani abu.“ Na kara gyara tsayuwa nace “amma faruk yakamata ka tausaya rywta a karona biyu ka sani idan ka tafi ba lallai na dauki dogon lkc ba zan bakin ciki da takaici zasu kasheni, idan ma wani wuri kake so kaje na yarda zan bika muje ko ina ne kuma duk rintsi da wahalarsa zan iya jurewa….“ Ba inda zaki bini humaira kuma baki isa ki fita daga ckn gdnnan tare dani ba, na hakura dake na hakura da tarayyarmu 2nda ba wahayi akayi mana dole sai mun zauna tare ba. Ya fada yana me daga murya. Bakina yadau rawa na dan taka kadan izuwa gfnsa nace “faruk!! nice fa!! ni kake gayawa haka?? Anya kuwa kasan abnd kake fada??“ Ya gyada kai tare da cewa “kwarai!! da hnklna kuma duk abnd nake fada shine abnd nake nufi har ckn zcyt.“ Tfyr hawayena ta canja izuwa kara sauri nace “A takaice kana so kace duk irin kaunar da kake yimin a baya yanzu babu ita?? Duk yadda alkawuran da mukai zaka karya su?? kenan soyayyar da muka dade muna raina ta mu2, yanzu babu ita 2nda har zaka iya tafiya ka barni…“

Yayi saurin juyowa yace “EH! babu ita na dade da kankareshi daga zuciyata wanda shine ya bani krfn rabuwa dake. Dai-dai lkcnne daddy da momi suka karaso. Na dubeshi nace “idan ka tafi kai da kanka sai kayi dana-sani me girma…“ dana-sani?? Ya tambaya yana dubana ya dora da cewa “Ai na gama dana-sani 2nda na yarda na aureki, wannan shine kuskuren da nayi mafi girma a rywt.“ Kaina ya sara da karfi Bansan sanda nace “karya kake faruk!! Ni nasan baka isa ka tafi ka barni har abada ba ko ka daina so na ba.“ Ya juyo yace “Kece makaryaciya humaira amma ni duk abnd na fada gskyne, zan tafi na barki kuma bazan taba dawowa ba har abada.“ Ya yunkura zai tafi nayi saurin rike rigarsa ya juyo muka dubi juna nace “Ka daina zaton ni kmr kowa ce a gareka, nasan maganar da zaka fada ta gaske da wadda bata gaske ba. Nasan abinda zai yiwu a wurinka da wanda bamai yiwuwa bane, abnd kake fada yanzu har abada bazai yiwu ba. Nasan kana fadan hakane sbd kawai kana son na kyaleka ka tafi, idan kuma har da gaske kake ka juyo ka rantse min da Allah Ka daina sona kuma zaka iya tfy ka manta dani har abada!!“ Ya tsaya kawai ya kasa motsawa. Na katse shirun ckn daga murya da cewa “Ka fada mana idan zaka iya“. jimawa kadan ya juyo a hnkl tare da grgz kai yace “humaira kinsanni ma2ka fiye da kowa a duniya, kinsan abnd zan iya yi da wanda bzn iya ba. Nayi karya idan nace “Zan iya cire sonki daga zcyt kona manta dake a tsawon rayuwata.“ Yayi kasa da murya yace “Amma ina so ki fahimta yau ba zabi bane a garemu, dole ne mu rabu. Bashi da wani alfanu cgb da zama a yadda muke sbd kowa baya son zamanmu tare kuma ba wnd keda shirin taimaka mana, duk daren dadewa dole wataran zamu gaza watakila sanda lkc ya kure mana.

RABUWA itace kawai maslaha a garemu koda bama so amma dole mu hakura. Kin sani bazan taba son mu rabu haka kawai ba, dalilaina nada ma2kar karfi wanda suka sa ni kaina naji na gamsu mu hakura da juna ba sonki nayi ba idan na barki kika bata da iyayenki akaina, na dawo dake garesu shine Kokoluwar son da zanyi miki sbd koda yaushe ryw aunata ake akan mizani, dole na fada nayi kuskure tun farko dana yarda na bata da kowa akan SOYAYYA kuma bazan so abnd nayi kema ki maimaita irinsa ba. Kiyi hakuri ki fahimceni humaira don Allah.“ Na jinjina kai sanda sautin kukana ya kara fitowa nace “yanzu meye madogara a gareka ina zaka??“ yace “Allah ne kawai madogara ta gareshi na mika al‘amurana na tbbt bazan taba tozarta ba.“ Ya juya inda ya tbbtr anan su daddy ke tsaye yace “Alhaji yau mun rabu da y‘arka kmr yadda ka nema, ni kuma na tafi kmr yadda kake so, amma ka sani idan wai kayi hakan don ka samu farin ciki to ina me bkn ckn sanar dakai kayi bnkwn dashi har abada. Na tbbt GUGUWAR KADDARA dake binmu tana gaf da zuwa kanka. Alkhairi nayi amma ban tsira ba bare kai daka shuka mana sharri, ba fata nake maka ba amma kaji tsoron taka UKUBAR don dole sai tazo.“ Daddy murmushin keta kawai yayi don wasa ma ya dauki zancen. faruk ya juyo gareni yace “Kada ki manta idan kika so nan da dan lkc kina da damar kîyi wani auren ba takunkumi akanki ya jinjina kai ya juya da fadin “ Na tafi humaira!! Sai wata rana idan muna da rabon saduwa.“ Bani da ikon hanashi a yanzu dole tasa nabishi da kallo har izuwa sanda motarsu ta fice daga ckn harabar gdnmu, a hankali kuma idanuna suka fara duhu kwakwalwata ta rikice, idanuna suka fara lumshewa a hankali ban ankara ba na sulale kasa sumammiya…

 Ahmad dake karanta lbrn yayi saurin juyo shafin da yake karantawa sakamakon zuwa karshe da yayi, yayi saurin bin faffadan littafin dake hannunsa da kallo. Iyakar inda aka tsaya da rubuta labarin kenan, zuciyarsa ta fada masa. Ya saki lttfn tare da kauda kai kmr ya fashe da kuka amma ai ba shikenan ba da saura sai meye kuma ya faru daga nan?? Ya tambayi kansa, ya shafi fuskarsa sannan ne yaji hawayen daya dade yana yi ashema kuka yake yi bai sani ba. Tunda yake bai taba jin lbr na abin al‘ajabi da tausayi kmr wannan ba yayi saurin sake jawo lttfn ya bude farkonsa ya kurawa hotunan dake manne a farkon littafin ido, hoton musamman hoton faruk din dake gefen na humaira, Allah sarki!! Ga kyau ga haiba ga annuri na tashi a fuskarsa, dukkansu farare sol tamkar larabawa sun dace ma2ka. Ya dubi dan zanen da akai a tsakiyar ho2nan, hoton alamar LOVE mashi ya shiga ta tsakiya kasa kadan an rubuta: littafin ya subuce daga hannunsa ya dafe kai kawai. Allah sarki!! Ashe ba banza ba humaira ta kasance koda yaushe ckn damuwa, shine dalilin da yasa ta zama wata iri harma ya kasa gane kanta. Ahmad ya daga kai ya kalli agogon dake manne a dakin nasa karfe 3:12 na dare, safiyar ma da saura kenan!! Ya fada. sbd yadda yake ji kmr ya jawo safiyar tazo, so yake kawai ya ganshi a gbn humaira sbd akwai tambayoyi masu dimbin yawa da yake son yi mata. Dukan kofar dakin nasa da akeyi a hankali yasashi dawowa hayyacinsa ya mike tare da takawa izuwa bakin kofar.

 Waye?? Ya tambaya ba tare daya bude ba. Nice.. Fatima ce. Ya bude kofar a hankali ya dubeta tare da cewa “Menene ya faru??“ Tadan dafa bakin kofar tare da cewa “Yaya lafiyarka kuwa?? Ina kwance a daki 2n dazu nake jiyoka kana surutai kai kadai fa.“ Kai!! zancen zucin da nake dama a fili nake yinsa kenan?? Ya tambayi kansa a zcyrsa. Ya juyo tare da cewa “a‘a.. kin… Waya nake yi ne da wasu abokan business dinmu muna magana ne akan yiwuwar wata yarjejeniya mu da su, bawai….wani abu bane…“ Waya har karfe 3:30 na dare?? Ta tambaya tare da cewa “gari na wayewa kuma karfe 8:00 ka fita, Allah yaya mutanen nan fa idan ka biye tasu zasu haukata ka!! HAUKA???? yayî saurin tambaya. Ya dora da fadin “kawai daga ina ayyukana sai hauka ko kuwa an gaya miki kwakwalwar mu maza irin taku ce??“ fatima Tayi dariya tare da cewa “To! Yanzu dai duk ba lkcn wannan bane don Allah ka kwanta kayi barci ka huta, ka kyale mutanen nan gobe sai ku karasa.“ Ya gyada kaî tare da cewa “To!! dama mun gama.“ Taja da baya da fadin “Sai da safe.“ OK!! ya fada sanda ya mayar da kofar ya rufe tare da takawa ya dawo kan gadonsa ya kwanta amma barcinma gagararsa yayi, 2nani kawai yake ta yadda zaiyi ya iya shawo kan humaira ta karasa masa lbrn nan. Sai byn tsawon lkc barci ya daukeshi ba kuma wani dadewa yayi ba aka kira sallar Asuba. *Tunda ya tashi bashi da wani 2nani sai asibitin da humaira take, 2ni ya mayar da komai ckn jakar tata kmr yadda take badon-badon ba da 2ni ya fice da sassafe amma dole tasa ya hakura.

Misalin 8:30 na safe suna zaune bisa kujeru su uku sunsa faffadan tebirin cin abinci a gbnsu wanda ke dauke da abinci kala-kala akansa, Ahmad da sauri yake kai abncn bakinsa burinsa kawai yaga ya kammala ya fita, Fatima ta kofin tea dake hannunta ta dubeshi tace “Yaya don Allah kaci a hankali, Mum jibi wani cin abnc da yake yi don Allah.“ Ya bîta da kll tare da cewa “Ina ruwanki?? Kin ganki…“ Mum din tace “gsky ta fada ai irin wannan cin abinci kmr zaka tashi sama??“ Ya dan daga kansa yace “wlh mum akwai abnd nake so naje nayi ne da gaggawa..“ Aiki ko?? Ta tambaya ba tare data dubeshi ba. fatima tayi saurin cewa “Shine mana mum ai kllm zancensa kenan.“ To!! Fadi ba‘a tambayeki ba. Ya ture kwanon dake gbnsa ya mike tare da cewa “Mum daga daki wucewa zanyi sai na dawo.“ A dawo lfy Allah ya bada sa‘a. Mum ta fada ahmad ya amsa da ameen tare da takawa. Fatima tace “A dawo lfy yayana na kaina.“ Ya waigo tare da cewa “Allah yasa kanwata ta goshina.“ Fatima ta kyalkyale da dariya. Mum kanta sai data murmusa tare da cewa “kudai abin dariyarku yawa gareshi.“ ahmad da sauri-sauri ya dauki abubuwan daya saba dauka hade da jakar ta humaira da key din motarsa ya fice daga gdn. Tafiyar da yakeyi akan kwalta kanta ba irin ta kllm bace hakan yasa a y‘an kalilan min2na ya iso asibitin, ya karasa da motar tasa inda aka tanada yayi parking kai tsaye ya wuce ciki. Allah yasa ta farfado ta dawo hayyacinta, Allah yasa ta yarda ta taimakeshi da abnd yake son ji. A hnkl ya 2ra kofar dakin wanda ya kasance na musamman a asibitin ya shiga, Ido hudu sukai da ita yayi saurin canja tafiya. Alhmdllhi! ya fada a ransa ganin yadda ta dawo tamkar ba ita ya bari a wani hali jiya ba. Ya karaso a hankali tare dayi mata sallama sanda ya iso gaf da ita ya zarce ga kwantaccen tsukakken tebirin dake jikin gadon da take ya jingina zuwa can yace “Sannu humaira, ina fatan saukin jikinkinki ya wuce yadda nake gani a zahiri Sannan da fatan zaki yi hakuri da abnd ya faru nasan nine na jawo miki.

Ya zanyi? dole na hakura mana, na hakura rabin jiki na ma ya tafi nake zaune da rabi!! bare wannan. Ta fada tare da yi masa nuni daya bata jakarta dake hannunsa. Ya tako ya dawo yana me cewa “banga kowa ba sai ke kadai?? Momi na ce kawai dama kuma ta fita amma zata dawo yanzu. Ya mika mata jakar yana me dubanta lkc guda yace “Naji faruk ya tafi kin suma a wancan lkcn daga nan sai me kuma ya faru?? Humaira ta saki jakar dake hannunta tare da binsa da kll tace “Abnd nake gudu sai daya faru kenan?? Ina ruwanka da jakata?? Meye na bude min?? Da izinin wa kayi hakan?? Ahmad ya grgz kai tare da cewa “kiyi hakuri nasan bai kamata bude miki abin sirri ba amma Allah ya kaddara ta hakan zansan lbrnki, naga abbwn AL‘JABI da yawa a cknsa ki taimaka ki kawar da dubunnan tambayoyin dake min yawo a zuciyata. ckn fusata humaira tace “Ba za‘a fada maka ba to! Sbd banga wani dalili ba da zaisa dole sai kasan komai gameda rayuwata ba 2nda idan ma ka sani ba abnd zaka iya yi.“ ka daina taso min da tsohon ciwo ka fita ka tafi kawai. Ta nuna hanyar fita.

Mu hadu a kashi na biyar al’ajabi Part 5.

Leave A Reply

Your email address will not be published.