Al’ajabi Part 5 Hausa Novel

Al'ajabi Part 5 Hausa novel

**** AL‘AJABI part 5 ****

 Ahmad yabita da kallo kmr ya fashe da kuka don takaici, ba’abin da yake so a ransa kmr jin karashen lbrn daya dauko jinsa amma ya yanke amma gashi bisa alama bazai samu ba, yadan gyara tsayuwa kadan yace “Amma humaira…..“ Tayi saurin katseshi da fadin “Ahmad!! idan kana yiwa Allah ka fita ka tafi! Karka manta duk abnd ka sani ma bada izini na bane bada yarda ta ba don idan da don nice ba zaka taba sanin komai gameda dani ba har abada. Ahmad ya juya baya daga inda yake tsaye yadan taka a hnkl ya dafa kujera dake gaf dashi ya juyo yace “Shikenan humaira kina da dama da ikon bani ko hanani abnd ya zama naki ba, kuma banga laifinki ba sbd wannan abune da ba kowa za‘a budewa ya sani ba. Is ok!! Na fahimceki kuma na gane abnd kike nufi da hkn, koda akwai wadanda zasu iya sanin komai gameda ke ni bana daya daga cknsu. Na gode Allah iya abnd na sani da kuma ilmin dana samu dangane da rayuwar duniya daga lbrnki, nayi dariya a wasu wuraren nayi murmushi a wasu wuraren, naji haushi a wasu wuraren sannan nayi kuka me yawa a wurare da yawa. Ya dakata da maganar jim kadan yace “Baki so ba kuma baki ji dadin sanin lbrnki danayi ba amma kiyi hakuri, Sai anjima.“ Ya juya a hnkl tare da takawa zai fita. Humaira tabishi da kll lkc guda taji bata kyauta ba idan tayi haka, Ahmad mtm na farko daya nuna damuwarsa akanta kuma yake son sanin wani abu game da ita, kuma Ahmad nada kamala sosai yarda dashi ba wata matsala bane.

AHMAD!!!! lkc guda ta kira sunansa, ya tsaya cak! a inda yake tare da juyowa ya dawo ya dubeta a hnkl yace “Yadai?? Da wani abune??“ Ta dan kauda kai kadan tace “Kana da ma2kar girma a wajena kuma ganin kimarka sosai akwai abubuwa da yawa da kayi min wadanda zan dade ina 2nawa, bai kamata ka nemi abu naki yi maka kai tsaye ba. Zan baka karashen abnd ya faru ckn shekaru biyu daga wancan lkcn har zuwa yanzu, amma ba yau ba sbd har yanzu kwakwalwata a rikice take amma nayi maka alkawarin zaka sani wataran. Ahmad ya jawo kujerar dake gaf dashi tare da yin murmushi byn ya zauna yace “Na dade da sanin kina da karamci don na gani a lbrnki, a shirye nake na jira komai tsawon lkc kuma komai dadewa kodon na karasa jin AL‘AJABI mafi girma daban taba jin irinsa ba, soyayyar da ko lbrn littattafai da fina-finai ban taba ganin irinta ba. Ya mike tare da cewa “Nasan may be ba wani dadewa zakuyi a asibitin nan ba ko?? Ta gyada kai da cewa “A yau dinnan ma zamu tafi gd, Suman da nayi ba wani tsatsauran abu bane a wajena don hkn ya saba faruwa.“ Ya saba faruwa?? amma ba wani mataki da kuka dauka akai?? Meke sawa kina shiga wannan yanayin?? Ba zaku nemi magani ba?? Ahmad ya tambaya ckn mamaki.

Hawaye sukai saurin gangarowa ta kuma2n humaira tace “Da baka san komai game dani ba to bznyi mamakin wadannan tambayoyin ba. Wane magani?? byn maganin cutar ya dade da tfy!! Yana raye koya mu2 ma waye ya sani?? Allah ne kadai yasan a halin…da.. yak….“ Kuka ya hanata karasawa. Ahmad yadan kauda kai hade da tambayar kansa, kenan 2nda faruk ya tafi bai dawo ba har yau?? Yayi saurin dawo da kansa tare da cewa “Ki daina fadar haka ki rage yawan damuwa komai yayi zafi maganinsa Allah, gashi momin ta barki ke kadai har yanzu bata dawo ba.“ Ya kautar da zancen.“ Ta jingina kanta da bango tare da cewa “Zata dawo….ne ina 2nanin suna magana da doctor ne don data dawo tfy zamuyi“. Ahmad ya mike tare da duban agogon hannunsa yace “bari na tafi kada nayi late da yawa kinsan yau aikin mu2m biyu zan fara ga nawa ga naki, fatan karin sauki da kwarin jiki sai nazo dubiya.“ Ya fada tare da juyawa ya fice, humaira ta kara jingina kanta a jikin bangon taci gaba da abnd ta saba, kukan zuci dana fili. Tayi saurin dakatawa da kukan da takeyi sakamakon FARUK da taga ya shigo dakin da saurinsa ya tsaya a bakin gadon da take ya bita da kallo yace “humaira meye ya faru dake haka?? Ya naga kin zama haka?? Tayi saurin dago kanta tace “Faruk!! dama kana nan?? Ashe kana raye?? amma ka tafi ka barni ka manta dani baka waiwayata.“ Yayi saurin cewa “Na dawo gareki humaira zan daukeki mu tafi, zo mu tafi.“ Ya fada tare da miko hannu, ta mika hannunta har sai da hannayensu suka kusa haduwa bat!!! ya bace. Dama tasan ba‘a gaske take ganinsa ba gizo yake yi mata kuma ba yau fara ta fara hakan ba. Ta saki hannayen nata suka je kasa tabi gadon ta kwanta ta rushe da kuka wanda hkn yayi dai-dai da shigowar momi wacce ta karaso dakyar ta tsaya akan humairar zuwa can ta zauna gaf da ita tayi tagumi kawai, tasan dalilin kukan kuma koma meye 2n asali sune suka ja don haka bata da bakin takurawa humaira akan dole saita hakura.

Har tayi iya yinta tayi shiru sannan suka shirya suka fita daga asibitin, driver yaja su suka nufi gida.

 BAYAN SATI DAYA

 Misalin karfe 4:20 Na yamma Ahmad ya fito daga ofis dinsa yahau motarsa tare da bin doguwar shimfidaddiyar kwaltar data nufi kudu daga inda yake, yasan ya fito da wuri ma2ka amma dalilin hakan yana son zuwa gdnsu humaira yau kodôn cika alkawarin daya dauka na zuwa dubata har gd. Da address daya dade da sani daga gareta kawai ya dogara akan zai iya kai kansa gdn nasu, A hnkl ya shigo unguwar tasu wacce take sabuwa mallakar gwamnatin tarayya. Ya fara ratsa tsala-tsalan gdjn ckn nutsuwa, har izuwa sanda ya iso gdn daya tbbtr nan ne gdnsu humaira yaci birki. Yana daga ckn abnd yake son ji daga karashen lbrn humaira, meye ya dawo dasu wannan sbwr unguwar kuma sabon gd daga SARAUNIYA STREET da suke acan baya?? A hnkl ya danna worn me kula da gate din ya leko ta karamar kofa ya koma tare da bude tafkeken gate din Ahmad ya wuce da motarsa.

Hajiya ce zaune a daya daga ckn kayatattun kujerun falon alfarmar ta zubawa T.V dake manne a jkn bango ido, hafsa ta shigo ckn ladabi tace “hajiya kunyi bako.“ Ta dawo da kllnta gareta tace “Wanene??“ uhmm!! Yace sunansa Ahmad. hafsa Ta fada. Ahmad..Ahmad!! hajiya ta fada ckn salo na nazari. Ok!! abokin aikin humaira. kace ya shigo. y‘ar aiki Hafsa ta juya tare da fita, jim kadan Ahmad ya shigo, manyan bakin yamma. Ahmad yayi dariya kawai ya karasa ya zauna suka gaisa da momi, ta mike tare da cewa bari na 2ro maka humairar ko? To hajiya nagode. Ta wuce kawai. Ahmad ya daga kansa ya dubi tafkeken falon da kawa2warsa da yadda yake, gskyne dole ma ya yarda humaira a gdn girma take kamar yadda ya dade da sani a lbrnta. Arziki kam akwai shi don rubuce yake karara 2n daga bakin gate izuwa ko‘ina na gdn, komai na gdn na daban ne. A hnkl kansa yakai ga kyawawan ho2nan dake manne a jkn bangon dakin zagaye dashi wadanda suka kasance manya sosai ckn kyakykyawar dauka. Senior na dubiyar ce sai yau byn na gama warwarewa harna manta ma da zancen wani ciwo??

Ta fada dai-dai sanda ta zauna. kafin yace komai daya daga ckn y‘ar aikin gdn ta iso dauke da wani kyakykyawan faffadan faranti dauke da ruwa da kuma juices gamî da wasu kananan kofuna ta dire a gbnsa ta mike ta juya. ya danyi murmushi yace “Wlh kinsan ayyuka sun hadu sun cunkushe gashi kema din kinki ki dawo ofis bare ki rage wasu abubuwan, yau din ma gudowa nayi kawai don na cika alkawari amma badon na gama ba.“ Humaira tace “Ahmad kenan kana kokari sosai da aiki yana da kyau a samar maka wani ko wata ta rike ofis dina kodon rage maka wasu abubuwan.“ Yayi saurin ajiye kofin hannunsa yace “Ke kuma fa?? ko shikenan ba zaki sake dawowa ba?? Ta gyada kai da cewa “gsky bazan dawo ba ahmad sbd ni banga wani amfani ba, ina aikin nan ne wai don na rage damuwa anma ba abnd ya ragu, kuma ni ba don kudi nake yi ba, ba wani alfanu da hakan keyi min ba wani dalili da zaisa naci gaba da wahalar da kaina. Na zabi dana zauna ni kadai a haka a gd na karasa rayuwata da bakin cikin daya riga yayi aure ya tare a zuciyata, yayi tsatso tare da fitar da y‘ay‘a masu yawa. Ahmad ya bitada kll yace “amma nidai banji dadin haka ba, kenan daga yau shikenan ko??“ Zan iya cewa haka sai dai kuma idan ka kawo ziyara irin wacce ka kawo yau. Humaira ta fada. Ahmad ya gyara zama yace “2nda may be yau itace ranar karshe zanso ki karasa min lbrnki kmr yadda kikai min alkawari, sai me kuma ya faru?? Faruk ya dawo?? ko har yanzu??“ Fuskar humaira tayi saurin canjawa daga dan walwala da take ciki kadan izuwa takaici, kmr ba zata ce komai ba zuwa can hawaye suka gangaro mata ta gyara zama ta fara: “Daga nan sai komai ya kara tabarbarewa, ya lalace bawai gareni kawai ba ga dukkanmu. Gskyr faruk da ya fadawa daddy “idan yayi hakan ne don ya samu farin cikî to bazai samu ba, domin kuwa 2n daga wannan lkcn rayuwar bakin ciki ta bude sabon shafi a gdnmu. Ni kaina bansan dalilin irin rikicewar da nayi ba, na susuce tmkr wata mahaukaciya haka na zama a wannan lkcn.

Ko abnc bana iya ci duk na rame iya karshen ramewa tamkar bani ba, magana kuwa babu zancen ta fito daga bakina sai dai 2nani, kuka kuwa na fili dana boye na ido dana zuci ba wanda bana yi. Ba abnd nake 2nani face FARUK!!! wanda ya nuna min son da duk duniya ba wanda yayi min rabinsa, ya fifitani fiye da kansa, ya soni sanda kowa ke guduna. Amma gashi an rabamu, ya tafi baisan inda ya dosa ba baisan inda zashi ba, ga lalurar rashin gani ba lallai ya samu wanda zai taimakeshi ba…..“ ( sheshshekar kuka ) …..“Ina zashi?? Kuma wajen wa?? Shi kansa bai sani ba amma a hakan ya zabi ya ajiyeni a gd ckn aminci shi yasha wuyar shi kadai. Wannan kawai SO ne da dole zan rinka 2na faruk dashi har abada. Munyi aure dashi amma bamu san meye dadinsa ba, wata mu‘amala irin ta auratayya bata shiga tsakaninmu ba har muka rabu kllm ckn jiyyar junanmu muke. (Wannan ne dalilin da yasa idan aka tambayeni game dani budurwa ce ko bazawara ko matar aure nake cewa ban sani ba.) Idan nace ni bdrw ce sai na tuno nayi aure, idan nace bazawara ceni amma kuma ai bansan wani da namiji ba a dny, Ta wani bangaren ma sai inga ina matsayin sakin da aka tilastawa mu2m yayi?? Hkn nasani a ckn rudani. Bayan wata daya da faruwar abin ne aka tbbtr zaiyi wuya rywt ta dore a haka ba tare da dayan biyu ya faru ba, kodai na mutu kn kuma na haukace. dole tasa aka shiga neman faruk ido rufe aka yita nemansa baji ba gani, har kyauta daddy yasa ga wanda ya kawo lbrn inda faruk yake amma har aka gaji ko alamar za‘a sameshi babu. Bai bar wata kofa koda daya da zata bada dama asan inda yake ba. A raina banji faruk ya tafi har abada ba shi yasa har gobe ina mafarkin dawowarsa. gdn da muke kansa dole tasa muka barshi sbd halin da nake shiga, a duk sanda na kalli inda faruk ya taba tsayawa, wannan shine dalilin da yasa muka dawo wannan gdn da muke ciki. Kuma 2n daga wancan lkcn har zuwa yanzu abubuwa da yawa sun faru wadanda zasu fadu dama wadanda ba zasu fadu ba…“

Tayi shiru kawai. Ahmad ya gyara zama tare da cewa “Wato wasu abubuwan ban zaci zasu iya faruwa a gaske haka ba sai da naji lbrnki, ALLAH SARKI HUMAIRA!! gsky kinga abbw da yawa a rywrki na ban mamaki, amma kuwa daddynki ance ya rasu ko??“ Ya tambaya dai-dai sanda ya dago kai ya dubeta. Humaira tadanyi shiru jim kadan tace “Haka duniya ta dauka.“ ckn rashin fahimta Ahmad yace “ba haka bane kenan?“ humaira tace “magana ta gsky ba mu2wa yayi ba da ransa amma na tbbtr halin da yake ciki shi kansa ya kwammace ya mutu…..“ Subhanallahi!! meye ya sameshi haka?? Ahmad ya tmby cike dason jin amsa. wasu sabbin hawaye suka gangarowa Humaira tace “Yana asibitin kwararru mallakar gwammatin tarayya (federal hospital).

Watanni shida da suka gabata ne ya kamu da wata irin cuta da likitoci kansu suka tbbtr a garin nan dai ba‘a taba samun me irinta ba, hakan yasa a duk kasarnan ba inda suke da masaniya akan cutar bare su bada mgnnta, barînsa shi yafi kokarin neman magani don inma anyi a banza. inji kwararrun likitoci. Yana can magana, ji da gani ba wanda yake iya yi. Sakayyan faruq ne..

Jikinsa baya motsi tamkar gawa, an killaceshi a inda ba kowa akalla tazarar meter 300 da inda wasu mutanen suke. Shakar numfashi ma sai da kundun robar oxygen yake yi, ba wanda ke iya shiga inda yake sai da tsauraran matakan kariya gudun kamuwa da cutarsa ta alakakai. Yana mawuyacin hali ma2ka da gaske, munyi iya kokarinmu akansa ta hanyar amfani da dukiya ta wuce misali amma a banza, mun karyata asibitoci masu yawa da manyan likitoci masu yawa amma duk inda muka je ba abnd yake sauyawa daga abnd likitocin farko suka fada mana. Dole tasa daga karshe muka hakura muka dawo dashi nan AMK TEACHING HOSPITAL inda muka guda 2n farko, abnd kawai lktcn suka gaya mana shine cutarsa sabuwar ce har yanzu masana na duniya bincike sukeyi akanta, da zarar an samu ingantacciyar hanyar maganceta zasu sanar damu domin sunsan kudi ba matsalarmu bane ko nawa ne zamu iya kashewa kai tsaye. Sai dai rashin lfyr daddy zai wuya ya tash….“

 Kuka ya kwace mata wanda ya haddasa ta kasa karasa dogon zancen data dauko. Ahmad ya grgz kai tare da cewa “wato humaira duk wanda ke korafi akan yawan damuwarki to baisan tarihinki bane, Ashe wannan ma na daya daga cikin wani yanki na damuwarki?? Humaira tace “bazan ce maka A‘A ba amma magana ta gsky ban wani damu da halin da daddy na ke ciki ba sbd shine ya jawa kansa koma meye, sun rufe ido sanda suke da dama sun sakawa wanda yayi musu alheri da sharri. Sbd kawai wata jarabta da Allah yayi masa gashi kuma shi ya kamu da wadda tafi ta faruk din, halin da daddy ke ciki a matsayin skyy na daukeshi. Bazan manta sanda faruk ke fadawa daddy cewa ‘Na tafi kmr yadda kake so amma ka sani idan wai kayi haka ne don ka samu farin ciki to ba zaka samu ba, kuma ka saurari taka UKUBAR don dole sai tazo…. domin guguwar kaddarar data 2nkaro ba wanda zata bari.‘ Allah sarki gsky faruk BAWAN ALLAH ne gashi dai duk abubuwan daya fada suna ta bayyana, dalili daya ne kawai yasa nake son daddy ya warke, sbd na kalli ckn idanunsa snd zanyi masa wata tambaya guda daya tak!! Amma badon haka ba ya…..“

 Ahmad yayi saurin katseta sanda tare da grgz kai sanda ya fahimci abnd take son fada, ya bita da kallo zuwa can yace “bai kamata kice haka ba mahaifinki ne fa!! Koba komai yakamata yaci darajar wannan, duk dan adam ka iya aikata kuskure a rayuwarsa. Na tbbtr shi kansa ya dade dayin dana-sanin akan abnd yayi, abnd yakamata kiyi yanzu kawai shine kiyi masa addu‘ar samun sauki. Sannan kuma humaira ki rage yawan damuwa da 2nanin da kikeyi sbd ba komai zasu haifar miki ba face matsala babba, wasu lktn sai kin manta rywr baya kafin ki iya shimfida sabuwar rayuwa.“ Humaira ta gyara zamanta tare da mayar da kanta izuwa inda take fuskanta tace “Nagode da shawarar daka bani,“ ta juyo ta kalleshi tare da cewa “amma ka sani bazan taba iya cire tunanin Faruk a ckn zuciyata ba dashi zan mutu na koma kabarina.“ Humaira ta riga tayi nisa ba zata ji kira ba. Ahmad ya fada a zcyrsa lkc guda ya mike tare da duban agogon hannunsa yace “yamma na dada yi bari na tafi, nagode sosai humaira da kasancewata mu2m na farko da kika bawa dama nasan abubuwa da yawa game da ke.“ Humaira ta dago kai tare da cewa “bari na kira maka momi kuyi sallama mana!!“ Ahmad ya grgz kai dai-dai sanda yadan taka gaba kadan yace “A‘A basai ma kin kirata ba idan ta fito ki fada mata na tafi. Nagode.“ Ya karasa fada tare da dunkule hannunsa a kirjinsa ya juya ya fice.

Ta mike tare da komawa kan kujera ta kwanta, hafsat ta shigo ta dauke farantin juices data kawo. Humaira na daga kwancen take canja tashar da take kallo da remote din dake hannunta yanayin da momi ta fito dashi yasata dakatawa tare da tambayar lfy kuwa momi?? Ta karaso jknta a sanyaye tace “daga Asibitine can inda daddynki yake aka kirani wai ana bukatar ganinmu da gaggawa, anya….“ Humaira ta cgb da harkar gbnta tare da cewa “meye ai bazai wuce kudi suke bukata ba wadancan sun kare ko kuma sun gaji da ajiyarsa anan zasu bukaci a daukeshi akaishi wani wurin.“ Momi tayi shiru tana me klln humaira kmr tahau kanta da duka, can tace “wai ke wace irin mu2m ce?? mahaifin naki na ckn hali irin wnnn amma bakya nuna wata dmwrk akai ko? To ki shiga hnklnk wlh. Kuma ki shirya zamu tafi yanzu,“ Ta juya izuwa ciki. Humaira ta dago kai tare da cewa “Tare dani??“ Momi tayi saurin juyowa a fusace da fadin “Eh don ubanki, ko ba zaki bane??“. Humaira ta mayar da kanta kawai tare da cewa “Allah ya wuci zuciyarki“. Tayi tsaki ta juya izuwa ciki. *Mintuna ashirin kacal suka kwashe suka fito daga gdn, zundumemiyar mota kirar Toyota PRADO suka hau direban ya tuka su suka bar harabar katafaren gdn nasu suka hau titin dazai sadasu da asibitin. Momi duk ta rude sai salati kawai takeyi fatanta kawai Allah yasa ba mutuwa yayi ba. Zaiyi wuya idan lfy a irin kiran da aka yi mata. Innalillahi wa inna ilaihir-raji‘un. Abnd take ta maimaitawa kenan. Humaira kuwa a zahiri nuna tayi ko a jknta kmr yadda ta saba yi, kalle-kallenta kawai take. A haka har suka iso harabar tafkeken asibitin kwararrun, ta ko‘ina mutanene ke shiga da fita wasu da marasa lfy wadanda ke iya iya shiga da kansu da wadanda ake dauke dasu, grmnsa ya wuce yadda ido ka iya hango karshensa. Kll daya zaka yiwa asibitin kasan ya wuce tsarar karami ko matsakaicin asibiti sai ka kirashi mafi kurewar girma. Kwararrun ma‘aikatane kawai ke kaiwa da komowa duk ta inda ka ratsa, asibitin AMINU KANO TEACHING HOSPITAL kenan daya daga ckn mafiya girma, shahara da kwarewa a fadin africa. A hankali momi da humaira ke ratsa sashe-sashe na asibitin izuwa sashen da nasu patient din yake, ofis din da zasu je don jin halin da ake ciki. Akan hanya suna gaf da shiga wani jami‘i ya taresu “inane kuna zuwa??“ Ya tambaya ckn dagulalliyar hausarsa. Momi tayi saurin cewa patient dinmu ne a sashen an kiramu ana nemanmu.“

 Mu2min ya grgz kai tare da cewa “No baku da kowa anan yanzu an dauke kowa daga nan, babu wani patient naku.“ Momi najin haka ta dafe kai tare da cewa “shikenan ya mutu sun daukeshi muje mutuware kawai, zata sulale kasa humaira ta tarota tabi jikin humaira izuwa kasa ta zarce da kuka ALHAJI ya tafi, innalillahi wa inna ilaihir raji‘un… Abinda take nanatawa kenan 2n ckn kuka me tsanani, dan katon mutumin dake tsaye ya dubesu tare da cewa “Alaji?? which Alaji?? Kuna nufi me cutar nan daya dade anan?? Humaira ta dago kai tare da cewa “Eh..Ehh shi.“ Ya daga kansa tare da cewa “wannan ba mutuwa yayi ba.“ Momi da humaira sukayi saurin dago kai kukan da momi keyi ya tsaya, To yana ina?? Meya faru?? Momi ta tambaya. Ehh! an fita dashi anan wurin. Ya fada. Me yasa to?? Humaira ta sake tambayarsa. Ya dauke kai yace “Oho!! bana nan don a tambayeni kuje ofishi ku tambayesu mana.“ Momi tayi saurin mikewa suka koma da baya izuwa ofis din dake gaf dasu kai tsaye momi taja hannun humaira suka fada. Doctor meya faru?? ina patient dinmu?? Bangaren da yake ma gaba daya a kulle me yake faruwa?? Momi tayi saurin tambayarsa. Dan siririn farin mu2min dake zaune bisa kujera yasa faffadan tebiri a gaba dake dauke da files akansa. Ya gyara zaman glass dinsa da dan yatsa yace “Alhaji isma‘il mahmud??“ Humaira da mominta suka dubi momi tayi saurin cewa “Eh.. shi muke nufi doctor.“ To bismillah ku zauna ko?? Ya fada tare da yi musu nuni. A hankali suka karaso tare da zama bisa kujerun dake fuskantarsa cike da zakuwa da jin abinda zai fito daga bakinsa. Kafin yace komai saî murmushi mai kama da dariya ta kwace masa yace “Ta ina ma zan fara??

 To magana ta gsky Alhajinku ba mu2wa yayi ba hasalima an tafi neman lfyrsa da yakinin samun sauki da yardar Allah.“ Ban fahimta bafa doctor. Momi ta fada. Ya gyara zama tare da cewa “Ah! dama kamar yadda kuka sani ne mun fada muku duk sanda aka samu sahihiyar hanyar da za‘a bi ta neman lfyrsa zamu sanar daku, akalla sati biyu da suka wuce muka samu rahotanni daga wani Babban asibiti a kasar finland akan sunyi gwajin aiki akan cutar kuma sunyi nasara gagaruma. Toda muka tbbtr da hakan munyi iya kokarinmu akan mu sameku sai ya zamana lambar da kuka bane da address mun nemesu mun rasa, akalla wajen kwana goma kenan sai yau muka gani muka kiraku. Lkcn da muka rasa yadda zamu yi ne kwatsam! sai ga wata gidauniya me suna FISABILILLAH FOUNDATION da suka ji abinda ke faruwa da kuma halin da ake ciki na bukatar aiki da gaggawa sai suka dauki gbrr daukar nauyin fita dashi bama tare da kun sani ba, sune suka dauki dawainiyar komai kuma yanzu haka ina tbbtr muku sun isa finland harma an fara aiki kuma komai zai kammala ya kuma warke ras a kasa da wata daya. Amma badon anyi haka ba a hasashen da mukai bazai kai yanzu da ransa ba Allah ne kawai yayi da kwanansa a gaba, ta silar wannan gidauniya.“ hawayen dake idon momi ya hade da murmushi daya ziyarci fuskarta yanzu ta juya suka kalli juna ita da humaira, humaira ta wani dauke ba wani alamun jin dadi data nuna. Momi ta juya gareshi tace “Alhmdllh!! bansan irin godiyar da zanyi garesu ba dama ku kanku gsky kunyi mana kokari sosai, FISABILILLAH FOUNDATION!!

 Ta fada tare da yin shiru tace “Na dade ina jin lbrnsu wajen aikata abubuwa irin wannan kuma kmr yadda sukayi mana muma munyi alkawarin daukar dawainiyar kashe linkin abnd aka kashe akanmu ga wasu marasa lafiyan dake bukatar taimako. Idan da hali ina so a sadamu da wannan gidauniya donyi musu godiya, idan kuma da wani tallafi da suke bukata don ci gbnsu muna iya basu tallafi muma.“ Mu2min ya gyara zama yace “maganar gsky gidauniyar nan ba zasu taba yarda asan su bama bare aje ayi musu godiya ko wani abu makamancin haka, amma ba2n kashe kudi akalla Alhajinku an kashe kusan miliyan biyar akansa…“ Mu kuma zamu bada naira miliyan goma, samu masu bukatar aiki da basu da hali ayi musu har sai kudin sun kare. Farin mu2min ya gyara zama yayinda murmushinsa ya kasa boyuwa yace “Hajiya wato da ace za‘a rinka samun irin hakan da ba karamin nasara za‘a samu ba, sbd sau tari zaki ga wadansu akan wasu kudi da basu taka kara sun karya ba wlh sai dai patient dinsu ya mutu sbd basu da yadda zasu yi. Zaki zubar da hawaye idan kika ga rai ya salwanta akan rashin kudi naira dubu ashirin ko goma ke kasa da haka ma, kuma mafi yawan wadanda yakamata su taimaka basayi. Momi ta gyada kai tare da cewa “Mun dauki izinah daga abnd ya faru kuma insha-Allahu zamu dage wajen aikata ire-iren abubuwa irin wadannan. Ah idan mun isa gida zan aiko maka da chak din kudin da kuma… dan ladan albishir naka kaima.“ Takai karshen maganar tana murmushi. Likitan me lambar kwarewa mafi kololuwa ya gyara zama ckn murmushi yace “A madadin ni kaina da duk wadanda wannan taimako zai shafa dama hukumar wannan asibitin muna mika godiyarmu, Allah ya saka alkhairi.“ Momi da humaira suka mike momi tace “ Mun gode sosai sai yan aiken nawa sun karaso“ To hajiya muma mun gode. Ya fada. Suka juya tare da ficewa ya mayar da kansa ga abnd yake yi. Motarsu suka hau kai tsaye suka nufi gd momi nata farin ciki da annashuwa. Suna isowa gd worn daya direban yayi tafkeken gate din ya fara budewa jim kadan motar tasu ta wuce izuwa harabar gdn, momi da humaira suka fito daga cknta kai tsaye suka wuce izuwa ckn gdn. Tafiya kadan sukayi suka iso katafaren falon alfarmar gdn nasu, humaira ta cire mayafin dake jikinta ta wurgashi kan kujera ta taka ta tafi da nufin wucewa izuwa dakinta.

HUMAIRA!!! Momi ta kira sunanta ta juyo a hnkl, Zo nan. Momin ta fada. Ta tako a hnkl tazo gbnta. Zauna!! momi Ta sake fada tare da yin nuni da hannunta izuwa kusa da ita. ba tare da gardamar komai ba humaira ta zauna. Momi tamkar me jin nauyin yin maganar abnd take son fada sai data jima sannan tace “Humaira!!“ ta kira sunanta tare da dorawa da fadin “Na fahimci rashin farin ciki da nuna bakin cikinki karara a lkcn da aka ce daddynki zai samu lfy, nasan dalilinki nayin hakan amma dole zan gaya miki hakan da kikai bai dace ba. Koba komai mahaifinki ne baki da tamkarsa a duniya kuma baki isa ki canzashi ko kankareshi daga wannan matsayin ba har abada. Na yarda muma munyi kuskure akan abnd mukayi kuma kema yakamata ace kin dade da fahimtar hakan kuma kinyi mana uzuri, wlh mahaifinki nasonki kuma yana kaunarki ma2ka zan shaidi hkn a ko‘ina, abnd yayi yana ganin gata ne don ya rabaki da wahala sai dai bai sani ba ya rabaki da farin cikinki na har abada ne. Kiyi hakuri humaira ki maida komai wurin Allah ina da yakinin ba haka kawai abnd ya faru ya faru ba lallai akwai wata izinah da Allah zai nuna mana, amma ki daina dauka cewa mahaifinki makiyinki ne kinji.“ wasu fararen hawaye suka yi saurin gangarowa ta kuma2n humaira ta grgz kai ckn kasa da murya tace “Bawai bana son daddy ko rayuwarsa bane wlh nafi son inga ya rayu fiye da kowa sbd bana son a nunani a kirani marainiya har karshen rayuwata, amma momi faru..k… duk sanda na 2na bansan inda yake ba ya mutu ko yana da rai?? A dadi yake ko a wahala??

Nakanji na tsani duniya da duk abnd ke cknta, lkt a asibiti ya bamu tbbcn akwai yakinin daddy zai warke yaci gaba da rayuwa ckn walwala da nishadi, inama kuma ace akwai wanda zai bani tbbcn faruk na raye kuma yana rayuwa ckn farin ciki da nishadi??? Dazan samu lbrn hakan kawai ya wadatar dani amma babu.“ gudun hawayen nata ya karu. Momi ta kauda kai tayi saurin mayar da kwallar dake neman kwararowa daga idanunta, tana tausayawa humaira ma2ka. Ta dafa kafarta tace “Nayi miki alkawarin daga sanda mahaifinki ya dawo to duk inda faruk yake a fadin duniya sai an nemoshi ma2kar dai yana da rai, koda nawa kuma za‘a kashe akan hakan.“ Humaira tayi saurin hada hannayenta ckn na momi ckn sheshsheka tace “Don Allah ku taimakeni momi… ina son na kara ganin faruk koda sau daya ne tak a rayu..wata..“ kai wannan love haka.. Allah ban wadda xatasoni kaman haka..!

  HUMAIRA!!! Momi ta kira sunanta ta juyo a hnkl, Zo nan. Momin ta fada. Ta tako a hnkl tazo gbnta. Zauna!! momi Ta sake fada tare da yin nuni da hannunta izuwa kusa da ita. ba tare da gardamar komai ba humaira ta zauna. Momi tamkar me jin nauyin yin maganar abnd take son fada sai data jima sannan tace “Humaira!!“ ta kira sunanta tare da dorawa da fadin “Na fahimci rashin farin ciki da nuna bakin cikinki karara a lkcn da aka ce daddynki zai samu lfy, nasan dalilinki nayin hakan amma dole zan gaya miki hakan da kikai bai dace ba. Koba komai mahaifinki ne baki da tamkarsa a duniya kuma baki isa ki canzashi ko kankareshi daga wannan matsayin ba har abada. Na yarda muma munyi kuskure akan abnd mukayi kuma kema yakamata ace kin dade da fahimtar hakan kuma kinyi mana uzuri, wlh mahaifinki nasonki kuma yana kaunarki ma2ka zan shaidi hkn a ko‘ina, abnd yayi yana ganin gata ne don ya rabaki da wahala sai dai bai sani ba ya rabaki da farin cikinki na har abada ne. Kiyi hakuri humaira ki maida komai wurin Allah ina da yakinin ba haka kawai abnd ya faru ya faru ba lallai akwai wata izinah da Allah zai nuna mana, amma ki daina dauka cewa mahaifinki makiyinki ne kinji.“ wasu fararen hawaye suka yi saurin gangarowa ta kuma2n humaira ta grgz kai ckn kasa da murya tace “Bawai bana son daddy ko rayuwarsa bane wlh nafi son inga ya rayu fiye da kowa sbd bana son a nunani a kirani marainiya har karshen rayuwata, amma momi faru..k… duk sanda na 2na bansan inda yake ba ya mutu ko yana da rai?? A dadi yake ko a wahala?? Nakanji na tsani duniya da duk abnd ke cknta, lkt a asibiti ya bamu tbbcn akwai yakinin daddy zai warke yaci gaba da rayuwa ckn walwala da nishadi, inama kuma ace akwai wanda zai bani tbbcn faruk na raye kuma yana rayuwa ckn farin ciki da nishadi???

 Dazan samu lbrn hakan kawai ya wadatar dani amma babu.“ gudun hawayen nata ya karu. Momi ta kauda kai tayi saurin mayar da kwallar dake neman kwararowa daga idanunta, tana tausayawa humaira ma2ka. Ta dafa kafarta tace “Nayi miki alkawarin daga sanda mahaifinki ya dawo to duk inda faruk yake a fadin duniya sai an nemoshi ma2kar dai yana da rai, koda nawa kuma za‘a kashe akan hakan.“ Humaira tayi saurin hada hannayenta ckn na momi ckn sheshsheka tace “Don Allah ku taimakeni momi… ina son na kara ganin faruk koda sau daya ne tak a rayu..wata..“ Ta zarce da kuka tare da kwantar da kanta bisa cinyoyin momi wadda ta shiga Rarrashinta.

BAYAN WATA DAYA

A mafi yawancin lkt mutane kan nuna maka soyayya a zahiri har su rika kokarin wuce makadi da rawa wajen nuna sunfi kaunarka fiye da kowa a duniya, amma idan da wata masifa zata afka maka sune na farko wajen rige-rigen gudunka. Duk da irin dukiyar Alh. isma‘il da yadda mutane da yawa ke cin gajiyarta ta bangarori da dama, da abokai hamshakai fitattu da yake takama dasu amma ya gane kuransa sanda ya shiga rashin lfyr data haddasa kowa ya guje shi, duk wanda ya ziyarceshi sau daya baya mararin ya koma musamman idan yaga matakan da ake dauka kafin shiga inda yake. Lallai gskyr masu magana da suka ce harka ta duniya da me rai kuma me lfy ake yinta, shikam ya yarda da hakan don ya gani da idanunsa. byn shafe wata guda curr!! da yayi a kasar finland ckn nasara aka kuma sa ranar dawowarsa, nan fa yaransa, ma‘aikatansa da duk wanda keda alaka ta kusa kota nesa dashi aka fara dafifin isa airport don taroshi. **Misalin karfe 11:30 na safe fitaccen filin sauka da tashin jiragen saman AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT din yadau harama tare da daukar shiri na musamman daga ma‘aikatansa wadanda 2ni suka fara tbbtr da shiri ga inda katafaren jirgi saukar farko a yau zai sauka. Ba tare da jimawa ba kuwa makeken jirgin na EUROPE AIRLINE ya dira a tirbar kasa daga sararin samaniyar daya shafe a awanni yana shawagi, daya byn daya mutanen jirgin suka fara fitowa yayinda jami‘ai suka hau kan aikin don tbbtr da cewa ba wani bata gari daya shigo ckn jrgn.

Ckn wadanda ke fitowar harda Alhaji isma‘il, byn komai ya kammalu sun gama gaisawa da mutanen dake tsaye suna dakon fitowar tashi ne kuma jerin gwanon tsala-tsalan motocin y‘an tarbar tasa suka fice daga airport din tare da darewa bisa kwalta suka nufo gdnsa. Ya warke sarai tamkar bashi ba tamkar kuma bazai taba dawowa haka ba, sukan dan taba hira kadan da wdnd ke tare dashi a motar msmmn idan yaga wani abu da ya canja masa a hanyar da suke bi. Min2na klln suka kwashe suka iso gdn nasa tafkeken gate din gdn ya bude jerin motocin suka wuce ciki a jere kmr yadda suka taho. Ckn min2na biyu kacal alh. isma‘il yayi godiya ya sallami kowa da kowa duk suka watse, shi kadai ya juya ya shige ckn gdn nasa.

*MINTUNA TALATIN DA DAWOWARSA*
Zaune yake bisa daya daga ckn kujerun dake zagaye da makeken tebirin dake zagaye da kayan abnc kala-kala, Ya dukufa akansa ckn annashuwa. Hajiya na tsaye bisa kansa tana tsiyaya masa juices a kofi ya dago kai tare da cewa “wai yaushe rabona da cin abnc irin wannan harna manta.“ Kada dai kace can turai din abncnsu ba dadi. Momi ta fada sanda ta juya ga plask dake kusa da ita. Ya hadiye lomar dake bakinsa yadanyi dariya yace “hmm.. wai turawa!! wadannan abncnsu ai jagwalgwalo ne kawai, banda dole madai… amma abcnsu ba wani ciyuwa yake ba.“ hajiya ta zauna ckn murmushi tace “To da fatan dai an dawo lfy?? yadan gyara zama yace “alhmdllh!! tfy gashi tayi kyau sosai, saura kuma cuta daya daban samu waraka ba har yanzu kuma ta yiwu har abada. …Na sani abu ne mawuyaci idan maganin cutar zai samu, gsky nayi kuskure ma2ka da har na kyamaci mu2m me karamci da mu2nci akan wata larura sai gashi ni naci karo da wadda tafi ta. Ina ma ace zan…..“ Isowar da humaira tayi wajen tare da dafa daya daga ckn kujerun wajen ta ari murmushi ta yafa a fuskarta, daddy ya dago tare da dakatawa da cin abncn.

Humaira tace “You are wellcome my dad.“ Daddy yace “my daughter yanzu nake shirin tambayarki ashe kina ckn gdn ma.“ Ina nan daddy ai banji shigowarka ba sai danaji hira tayi yawa…“ Ya katseta da cewa “Eh mana gata nan tasani a gaba sai zuba muke,“ Suka danyi shiru nadan lkc daddy ya bita da kll yace “Ya 2nanin faruk kuma???“ Lkc guda fuskarta ta fara sauyawa daga murmushin data kakala a baya, a hankali kuma hawaye suka fara ciko idonta har izuwa sanda suka gangaro bisa kumatunta. Ta juya da sauri tabar wurin. Daddy ya ture abncn dake gbnsa tare da dafe kansa yace “wai ba abnd ya ragu game da ita??“ Sai dai abnd ya karu. Momi ta fada. Daddy ya grgz kai tare da cewa “gsky hajiya mun cuci yarinyar nan, ban taba zaton abin nan zai zama haka ba,“ yakai karshen maganar yana me grgz kai tare da yin ajiyar zuciya. Tunanina kawai yaushe ne zan dawo mata da farin ciki?? Tayi dariya ta gaske bata karfin hali ba?? Yaushene walwalarta zata dawo kmr yadda take 2n asali?? Domin idan har bamuyi taimaketa da hakan ba zuciyarta ba zata taba yafe mana ba ko ta daina kllnmu a wadanda suka kawo karshen farin cikin rayuwarta wanda ni kuma bana son hakan, ina so ko byn raina tayi alfaharin cewa ni mahaifinta ne, amma ta yaya??“ Momi taci gaba da klln inda idanunta suke kmr me yin nazarin wani abu jim kadan tace “Hakan na iya yiwuwa idan da rabon zai yiwu, muna da damar da zamu iya yi mata hakan ta hanyoyi da dama saura kuma mubarwa Allah yayi zabinsa.“ Daddy ya gyada kai tare da cewa “A yadda nake ji a shirye nake na kashe ko nawa ne don dawo da farin cikin y‘ata, sai dai bansani a ina FARUK yake?? Tsorona ace ya mutu don hkn na nufin dorewar bakin ckn y‘ata har abada.“ Insha-Allahu ma bai mutu ba yana nan da ransa kuma zamu sameshi na tbbtr shima duk inda yake tunaninsa yana nan shima, ka cgb da cin abncnka yana wucewa fa.

Ta fada sanda ta mike ta cgb da shirya kayan dake ajiye bisa kayataccen faffadan tebirin, yadan dago daga dafe kan da yayi “Au ni harna manta wlh.“ Ya fada sanda ya jawo plate din daya ture dazu. Byn dan lkc ya dago kai tare da cewa “Yauwa idan an jima da daddare zamu je AMK hospital dukkanmu.“ Ta dago kai da sauri da cewa “Baka gaji da kwanciya a gadon nasu ba kenan??“ Yayi dariya yace “Allah ya tsaremu da kwanciyar gadon nan, kinsan dole sun cncnci jinjina ta musamman kuma bata baki kawai ba….“ Yauwa dama ban gaya maka ba, jin dadi da farin ckn dana shiga sanda naji lbrn yadda akai bansan sanda na bawa su hukumar asibitin ten millions ba sbd muma yadda akayi mana ayiwa wasu.“ Ya mayar da kansa ga plate din dake gbnsa tare da cewa “Kin kyauta ma2ka da haka, amma akwai wadanda nake son zanyiwa kyauta ta bajinta sannan kuma ina bukatar a hada ni da masu gidauniyar nan.“ Momi tace “FISABILILLAH FOUNDATION!! ance fa basa bukatar asansu ko ayi musu godiya bare a basu tallafi, duk abnd sukeyi don Allah ne kuma suna da yakinin sunfi karfin hakan, ni a yadda nake gani ko su waye ma amma ba kananan mutane bane suna da arziki na wuce misali.“ Nima ina tsammanin hakan amma ina so naga waye?? wacece?? ko kuma su waye?? Ina sha‘awar ace nima an hada gwiwa dani wajen aikata kyawawan ayyuka irin wadannan.“ hajiya tayi murmushi tare da juyawa izuwa dan karamin firjin dake ajiye nesa kadan da inda suke. Hakan nada ma2kar kyau kuma tunani ne me kyau kayi dama a kllm duk abnd ya faru ga mu2m ilimi yake karawa indai yana da hnkli, mafi kyawun dukiya itace wadda ake sadaukar da ita ga wadanda basu da hali, ake taimakon masu bukata kuma ake amfani da ita wajen saukakawa wadanda ke ckn matsi.“ Hira ckn nutsuwa taci gaba da gudana a tsakaninsu.

 sai Misalin karfe 7:30 na dare ne tsaleliyar motarsu kirar mercedez (G. compressor) ke keta shimfidaddiyar kwaltar da hasken fitula ya gaurayeta tamkar rana, ko‘ina ka kalla mutane ne keta harkokinsu a ko‘ina ba tare da fargabar cewa dare ya tawo ba. Su uku ne sai direba cikon na hudunsu, kallo daya zakayi musu koda kuwa daga wajene ka hangi motarsu akwai alamar arziki yaji ya wadacesu. A hnkl direban ya karya kan motar ya sadata da inda aka tanada don yin parking na motoci byn da suka iso, jim kadan Alhaji isma‘il tare da hajiyarsa suka fito sai humaira data fito ta dayar kofar suka zagayo suka jera suka nufi ciki. Tfy kadan sukayi suka iso ga tafkeken ofishin oga kwata-kwata, ba tare da wani jinkiri ba suka danna kai don kuwa ansan da zuwansu, ganinsu keda wuya ya mike tare da fadin “you are wellcome Ya hajj, suka gaisa ckn grmamawa. Daddy yace “kaga yadda Allah yayi damu kuma.“ farin lukutin mu2min wanda fuskarsa ke cike da annashuwa yace “Alhmdllh!! naji dadin hkn ma2ka, lallai wato alhaji… amma dai bismillah ku zauna ko!! bari a kawo muku dan abin sha.“ A‘ah ai ka barshi ma kawai me girma M.D da yake ba lallai mu wani jima ba, zuwa kawai mukai mu jaddada godiya da abnd akai mana, gsky wato idan akwai wani award ma kun cancanceshi a wurina.“ M.D din yayi dariya yace “ai ko ba award aikin mune hakan ba kuma akanka muka fara dawainiyar shigewa gaba a fita waje ayi masa aiki ba munyi da yawa, ai mu burinmu duk wani patient namu muga ya sami waraka koma a ina ne, kai!! naji dadi sosai wlh.“ Ya fada yana me binsu da kll. Shiru yadan gudana tsakaninsu jim kadan Alhaji isma‘il yace “Ah me grm M.D gaisuwa da rokon iri nazo, ina so a hada ni da shugabannin gidauniyar nan fuska da fuska idan hali.“ Yayi saurin grgz kai tare da cewa “hmm… alhaj kafin kai mutane da yawa sunyi yunkurin hakan amma baya samuwa sbd su basa bukatar asansu ba kuma na zaton zasu bada damar a hadu dasu, don haka ba zaka taba sanin kosu waye ba har abada.“ kosuwaye da wannan gagarumin taimako.

Humaira dake zaune a kujera ta dago kai tayi saurin zaro ido, FARUK!! sai ta juya ga kanta tace a zcyrt “yau kuma gizon da fuskar keyi min har ta dawo naga wani a matsayinshi?? kmr yadda spring ke tashi idan aka dagashi yayinda aka danneshi haka daddy da momi suka mike, suka dubi juna tare da juyawa suka dubeshi ckn hadin baki suka ce FARUK!! ya tsaya kyam a tsaye ya saki murmushi yace “na‘am!“ Kai!! wai suma FARUK suke gani?? Kenan da gaske shi din ne?? Humaira ta tambayi kanta lkc guda ta mike tana binsa da kll, kmr an jata kuma ta fara takawa izuwa inda yake ta tsaya cak a gbnsa. Ta saurara ko zata ji ta farka daga irin mafarkin data sabayi amma ina!! gani tayi da gaske tbbs wannan kam gaske ne. FARUK!!!! ta kira sunansa. Na‘am HUMAIRA!!!! ya mayar mata da martani. Kaine?? Ashe zan ganka?? dama zaka dawo?? Kwarai nine humaira na dawo gareki kuma bazan kara nisanta daga inda kike ba har abada. Ta dan matsa gaf dashi tadan gifta hannunta a saitin idanunsa da cewa “kana gani yanzu??“ Ya gyada kai kawai alamar EH.

 caraf hannuwansu suka hadu da juna wasu hawaye suka fara gangaro musu suka kurawa juna ido kawai tamkar gumaka. Momi da daddy tsyw kawai sukai suna kllnsu. tyy wdnn zasu rabu dynsu ya samu sukuni?? Soyayyarsu ta zama NATURAL LOVE ba zuciya kawai ba har jini da tsoka. Sai da aka tabasu sannan sukai firgigit suka dawo daga suman murnar da sukai, a hnkl hnns ya rabu da juna, taja da baya tace “Na cika burina na kara ganinka na tbbtr kana ckn aminci da rayuwa me dadi ko yanzu na mu2 ban mu2 da takaici ba, amma yanzu kafi krfn ka zama babban mu2m abin takama da tunkaho a duniyar arziki da tarin dukiya.“ Faruk ya grgz kai yace “duk abnd na mallaka ba nawa kadai bane namu ne tare dake, mu zamu tfyr dasu domin duk abnd na mallaka sunana da naki ne a jiki wato FARUK*HUMAIRA, don na yarda a raina cewa ba abnd zan mallaka a duniya da zaisa naji na gujeki ko bana sonki.“ sbbn hawaye suka gangaro mata ta dubeshi ckn daga murya tace “gasu nan ka gaya musu yadda ka zama haka, yadda kayi arziki fiye da nasu, ka warke daga larurarka har ka dawo kayi silar wrkwr tasu cutar, ka fada musu.“ Takai karshen mgnr da karfi. Faruk ya grgz kai yace “ynz ba lkcn wannan bane shi yasa na zabi muyi irin wannan haduwar, Allah ne ya sauya al‘amarina daga baki ya koma fari.

Ya dan taka kadan daga inda yake yace “bigewa kawai nayi da gini akai idanuna suka dawo gani, daga nan ne na amshi dukiyar dana gada a wurin mahaifina dake wurin Ummi na shiga kasuwanci Allah yasa masa albarka harna zama haka, Nayi bincike na gano ku da kuma hnyr dzn biyo muku.“ sbd nadama Daddy kasa yayi faruk yayi saurin tareshi da fadin “A‘A har abada mahaifi baya taba zubewa dansa, kome kayi min baka bukatar neman yafiyata kuma dama 2ni ni na yafe maka. Daddy ya bishi da kll, faruk yace “dama kawai nake nema a karo na biyu ka mallaka min humaira. Dama taka ce duk wanda yayi yunkurin rabaku shine a wahale. Daddy ya fada. Suka dubi juna murmushi hade da dariya suka fara tashi daga fuskokinsu. Daga nan suka kasance tare rywar farin ck sbw ta dawo har zuwa karshen rywrsu. FARUQ&HUMAIRAH..

THE END.

 ALHAMDULILLAH!!!

Leave A Reply

Your email address will not be published.