Al’ajabi Pert 1 Hausa Novel

Al'ajabi Pert 1 Hausa Novel

****** AL’AJABI PART 1 ******

Tsaye yake ya dafa tebirin dake gabansa tare da rankwafawa kansa na kallon tebirin dake gabansa, kallo daya zaka yi masa kasan a cikin damuwa yake. Ya dago kansa tare da matsawa yaci gaba da takawa ya fara safa da marwa a cikin faffadan ofis din nasa, tsawon lokuta ya shafe yana kaiwa da komowa ya rasa me ke masa dadi.

 A tsayen ya zura hannunsa ya zaro wayarsa dake al‘jihu ya lalubi lambar wanda yake son kira tare da karata a kunnensa ya taka a hankali izuwa kan kujerarsa ya zauna, hannunsa daya na rike da wayar yayinda dayan hannunsa ke dafe bisa tebiri dake gabansa. Hello!! ya fada dai-dai sanda aka daga wayar sannan ya dora da cewa “ Ranka ya dade yarinya nan fa har yanzu bata zo ba ina tsammanin ma b zuwa zata yi ba, gaskiya na gaji ga yamma na dada yi kuma na gaya maka uzuri gareni ga yamma na dada yi.“ Cikin rarrashi wanda ake yiwa wayar yace “ Ahma kayi hakuri ta taho go slow ne ya riketa amma yanzu zata karaso.“ Ahmad din ya kara bata rai ya kauda wayar daga kunnensa ya ajiye wayar bisa tebirin dake gabans ya kwantar da kansa jikin kujerar ya zubawa kofar shigowa ofis din ido, sai daya shafe wasu mintuna ashirin din babu alamun wani zaizo sbd takaici runtse idonsa yayi kamar barci yakeyi sai dai a zuciyarsa 2nanin irin fadan dazai rufeta dashi kawai yake. As-salamu-alaykum.

 Wata zazzakar murya tayi sallamar data saka Ahmad saurin dago kai tare da gyara zamansa yana me kallonta har izuwa sanda ta zauna tana me fadin “gani na iso“. 2nanin da yake tayi a baya sai yayi saurin kawar dashi domin kallo daya yayi mata yasan tafi karfin wulakanci ko a tozartata ba karamin kwarjini garet ba, zunzuru2n kyau kuwa ba‘a magana lallai Alla yayi halitta. ya fada a zuciyarsa. Amma dai kinsan kin bata min lokaci ko?? ya fada yana dubanta. ba tare da alamun nadama ba tace “ Eh nasani “. To me yasa?? koda dai ance wai go slow ne ya rikeki?? Ya tambaya ba tare daya dubeta ba shima. Tayi saurin girgiza kai tace “ gaskiya karyane hasalima ban taba hawa titi fayau irin yau ba, ni din ce kawai ban taba hawa titi fayau ba motoci irin yau ba, ni din ce kawai ban gadamar fitowa d wuri ba.” A karo na biyu ya sake dubanta da sauri ya danyi shiru na dan lokaci sannan ya kawo gwauron numfashi ya gyara zama yace ” Ance min in jiraki za’a miki dan interview na yan mintuna kuma a daukeki aiki a baki ofis kai tsaye, koda bansanki b amma nasan tabbas wanda ya tsaya miki babba n don ban taba ganin inda akai hakan ba sai akanki don wasu da wuya suke neman aikin basu samu ba wata kila hakan ne yasa kike wani ji dakai kina gadara aikin ma ba wani damunki yayi ba.” Ta tsuke baki sanda ya kawo karshen zancen nashi tace ” Gskyne ba damu na yayi ba kusan m ince maka tilastani akai sbd ansan nice zan taimaka muku ba kune zaku taimaka min ba, batu wanda ya tsaya min kuwa koda a fadar shugaban kasa ya nema min aiki ba wanda ya isa ya hana bare nan.” Tayi nuni da ofis din a wulakance.

Ahmad ya sake binta da kallo a zuciyarsa yace ” Wannan tafi ni bala’i.” Ya gyara zamansa tare da jawo laptop din dake gabansa ya mayar da hankalinsa gareta jim kadan ya dago kai yace ” Meye sunanki?? ” Kanta na duban tebirin dake gabanta tace ” HUMAIRA “. ya danyi shiru kadan kamar me sauraron kara jin wani abu daga gareta, jin tayi shiru yasashi ture laptop din daga gabansa ya dubeta yace ” Yakamata kiyi min adalci, kin bata min lokaci a zuwanki amsa tambayar ma sai kin sake bata min wani lokacin??” Au wai kana nufin full name?? To sunana HUMAIR ISMAIL. Ta fada tana me kallonsa. Ya jawo laptop sanda yayi tsaki kasa-kasa. Meye level din karatunki?? Ta amsa da cewa ” Masters degree “. Yayi saurin dubanta cikin mamaki a ransa ya sak maimaitawa ( masters ) tab!!!!! Wacce jami’a?? Ya sake tambayarta kansa nakan laptop din. Ta dan kauda kanta kadan tace ” oxford university ENGLAND.” Bai san sanda ya sake dubanta ba cikin mamaki, yarinya dole kiyi girman kai!! Ya fada a zuciyarsa. Yayi saurin kauda kada ta fahimci halin da yake ciki yace ” kinzo da takardunki ne??” Babu bukatar zuwa dasu 2nda ba maular aiki nak ba dazan rinka yawo da takardun makarantaba hakanan..

Bala’i!!!! Lallai wannan tafi ni masifa. Ya danyi shiru zuwa jimawa yace ” last question!! Relationship??” Tayi shiru kamar bata jiba ya sake maimaitawa da hausa da fadin ” budurwa, bazawara ko matar aure?? wannan abu ne da dole a sani a duk inda mace zatai aiki a duniya. Fuskar Humaira tayi saurin canjawa izuwa yanayi naA damuwa tace ” Don Allah kasa UNKNOWN kawai.” Ahmad ya hade rai cikin takaici ya shafa kansa ” Wai ke wace irin mutum ce don Allah ?? Ya kike meman kisani ciwon kaine?? baki ma san ke budurwa ce ko bazawara ko matar aure ba?? ” Tayi saurin gyada kai tace ” Eh bani da tabbacin zama daya daga cikinsu.” Ahmad ya mike cikin tsawa yace ” wallahi karyan hakan baya taba yiwuwa dole a samu kina daya daga cikin wadannan azuzuwan “. Ta mayar masa da martani da cewa ” ba wani dalili da zaisa inyi maka karya 2nda ba aljanna zaka bani ba don haka karka kara karyatani akan abinda baka sani ba.

 Ta dubeshi hawayen dake idonta suka yi gaggawa zubowa ta dora da cewa: ” Na rantse da Allah idan nace maka ni budurwac nayi karya!! Idan nace maka ni bazawara ce nayi karya!! Haka idan nace matar aure ce ni karya nake!! Ni kaina bansan da sunan da zan kira kain ba. Ahmad wanda fusata ta sashi mikewa yayi saurin komawa ya zauna idonsa ya zaro sbd mamaki, da AL’AJABI zuciyarsa ta fara sake-saken tayaya ma hakan zata faru?????????

 Ahmad yaci gaba da kallonta kawai har yanzu mamaki ne cike fal kuma rubuce a fuskarsa, Abinda ke yawo a zuciyarsa shine: Babu alamar wasa a tare da ita, hasalima hawayene ke zuba bisa idanunta a halin yanzu kuma gashi ta rantse, Tabbas hakan na nuni da cewa har cikin zuciyartane abinda take fada. abin AL’AJABI mafi girma da kunnuwansa suka taba jiye masa kenan. Tunani daya da yayi wanda ya kore 2nanin da yakeyi a baya shine: To kodai don ni namiji ne yasa ban fahimci abinda take nufi ba?? Tabbas shine dalilin. Ya bawa kansa amsa dai-dai sanda ya dubeta tar da zaro wasu takardu dake gabansa ya dora a gabanta yace ” Yanzu dai shikenan kiyi hakuri ki daina kuka ga kundin takardun da kike bukata a aikinki bari nasa masinja yayi miki jagoranci izuw ofis dinnaki, daga yau kece babbar me kula, da adana bayanai na wannan ma’aikatar ALLAH YA TAYA RIKO.”

Yakai karshen maganar dai-dai sanda ya waiga tare da kiran sunan masinja, BALA!! BALA!!! Da sauri ya karaso tare da dukawa yace “Yallabai” Ahmad ya dan kwantar da kansa bisa kujerar da yake zaune yace ” Kuje da ita ofis no: 11 ka hadata da sakatariya zanyi mata waya.” Da sauri bala masinja ya amsa da ” To Yallabai ” Ya wuce yayi gaba. Humaira dake zaune ta mike ta jawo jakarta wadd ta dade da dorata bisa faffadan tebirin dake gabanta, ta debi takardun da Ahmad ya bata ta zuba a ciki tare da gyara zaman bakin glass din dake da fadin rufe idonta daya matukar kara mata kwarjini. Ta dan bishi da kallo kawai ta juya ta nufi kofar fit daga ofis din, Yayi saurin cewa ” Koda ba yanzu ba ina fatan na sami labarin rayuwarki wanda ta yiwu ya warware min rudanin dana ke ciki.” Tayi saurin dakatawa tare da dawowa da baya a hankali tace ” Idan har ba kana yin haka bane do ka gano hanyar karya zuciyata ba to na rokeka ka bari, ka kalleni a humaira kawai karka takura waje binciken wacece ni sbd ba abune me samuwa a wurinka ba, Ta dan kara daga muryarta tace ” Bakina bazai taba iya furta labarin daya faru dani baya ba kamar yadda kwakwalwata ba zata juri tunano hakan ba, idan kana son mu zauna lfy dakai karka kara taso min da wannan zancen.”

Takai karshen zancen cikin tsawa a dai-dai lokaci data canja gaba daya kamar ba ita ba. Taja da baya ta fice da sauri. Ahmad ya bita da kallo lkc guda ya mike izuwa tagar ofis din ya hangeta ta glass kai tsaye wata tsaleliyar mota kirar TOYOTA PRADO ta dosa ta bude motar ta shige, motar tata tabi bayan tsohuwar HONDA CIVIC wadda bala masinja keja don yi mata rakiya. Ahmad ya kauda kansa daga wurin ya fara takawa a hankali cikin ofis din, Yarinyar nan fa ba karya takai tayi takama ko gadara, kallo daya yayiwa motarta yasan ta fito ne daga gidan masu akwai, t amma meye mummunan abinda ya faru da rayuwarta har yasata shiga yanayin da take ciki?? menene musabbabin hakan??.

Abin nema ya samu don haka wlh sai na sani kot halin kaka. Ya fada a fili, ya juya ya rufe laptop dinsa tare da jawo bakar jakarsa ya zirata a ciki, jakar tasa na hannunsa yayi waje. Kai tsaye motarsa ya nufa yabi tsaleliyar hanyar data nufi kudu, a ransa ya darsa cewa ya fasa zuwa inda yayi niya 2nda yamma ta riga tayi. Duk da sanyayyar wakar mawaki justin bieber dak tashi a hankali cikin motar tasa baisa ya manta d abinda ke ransa ba. Mintuna Ashirin ya kwashe ya gangaro cikin katafariyar unguwar tasu, rukunin gidaje na NEWCLAX QTRS.

 tsararriyar unguwa ta gani da fada. Worn daya yayi a bakin tafkeken koren gate din y fara budewa a hankali bisa jagorancin wani siririn matashi wanda yayi saurin cewa ” sannu da dawowa “. Ahmad ya gyada kai tare da fadin yauwa. Ya wuce da motar yayi parking dinta a harabar gidan ya wuce izuwa cikin, shigowarsa falon keda wuya yaji kyas!! Alamun daukar hoto, yar kyakykyawar budurwar ta tuntsire da dariya tace ” gaskiya yaya hoton nan yayi kyau, bari a kara maka daya.” Ya dan harareta kadan yace ” ke baki da wani aiki saina daukar hotunan mutane a waya ko??” Ya karasa ga daya daga cikin kujerun dake zagay a katafaren falon, momi dake zaune kanta na kallon TV din dake jikin bango ta juyo gareshi tac ” Ahmad an dawo kenan??” Wallahi momi sai yanzu, Ya fada cikin ladabi. Dai-dai lokacinne saudat ta dire farantin juice dak hannunta ta tsiyayo lemon a dan karamin kofi ta mika masa, Ya amsa tare da cewa ” Thank U my blood sister, yau dai kina da kirki “. Ta juyo tace “yau kawai??” Ya gyada kai yace ” iya yaune kawai “. Ta juya ga momi dai dai sanda ta karasa ga kujer ta zauna tace ” momi kinji shi ko??”.

Momi ta mike tare da cewa “zaku fara surutun naku kenan? to bada ni ba bari na shiga ciki lokacin sallah ya gabato.” Shigewarta sashin nata keda wuya Ahmad ya daw kujerar da saudat ke zaune yace ” yauwa ina da tambaya watakila keki sani don nidai nayi iya tunanina na kasa ganowa amma fa gsky zaki gaya min pls”. Tayi murmushi tace ” fadi muji idan na sani “. Ya gyara zama yace ” Tayaya mace zata zama ba budurwa ba, ba bazawara ba, kuma ba matar aur ba?? Sannan da wane suna za’a kirata?? ” Saudat ta danyi shiru can tace ” waye yayi maka wannan tambayar?” Ya girgiza kai tare da cewa ” ba ruwanki kawai ki amsa min idan kin sani “. Saudat ta kyalkyale da dariya tace ” Amma yaya anyi saurin juya 2naninka daka kasa gano amsa me sauki irin wannan, mace na iya zama ba bazawara ba, ba budurwa ba, ba matar aure ba IDAN……….!?

Hakan na iya faruwane kawai idan fyade akayi mata, kaga ta tashi daga budurwa, kuma ba bazawara bace sannan ba matar aure ba. Ahmad yayi shiru cikin salo na nazari jim kadan y girgiza kai yace ‘ gaskiya baki fada dai-dai ba wacce aka yiwa fyade ai ta zama bazawarako??” Saudat tayi shiru kawai tabishi da kallo, tabbas ya ta gsky kuma ba dai-dai ta fada ba. Ahmad yadan harareta kadan ya tashi izuwa kujerarsa yace ” ke dama idan ba danna waya ba me kika sani??” Saudat tace ” to ai ko ba komai nayi kokari 2nda nayi tunanin abinda kai baka yiba.” Ahmad ya kauda kai yace ” kinyi tunani amma useless ne “. Tabishi da kallo tace ” kasan abinda za’ai? “. Ya girgiza kai alamar A’a.

Tace “bari mu tambayi momi 2nda ita tsohon hannu ce ta yiwu ta sani sai ta fada mana,” Ta yunkura da nufin kiran sunan MOMI, Ahmad yayi saurin dakatar da ita yace ” KE! rufa min asiri, bar don Allah. ” Ta kwantar da kanta jikin kujerar ta kyalkyale da dariya tace ” Amma dai yaya duk sanda ka samo wannan amsar don Allah nima ina jira sbd ina son nasan yadda akai hakan zata faru don nidai ina ganin da kamar wuya…..” Ahmad ya mike rike da jakarsa yace ” kada kiyi saurin karyata abinda baki sani ba, kiran salla ake bari na shiga ciki nayo alwala. ” Tabishi da kallo kawai har ya shige dakin nasa, ta juya ta kwanta bisa doguwar kujerar tare da cigab da danna wayarta.

 Zaune take cikin faffadan ofis din ita kadai ba tare da kowa ba, babu alamun motsin wani tsit ofis di yake sai dai na’urar dake nuni da shigowar sako dake kadawa a hankali lokaci zuwa lokaci. laptop ce a bisa tebirin dake gabanta gefe guda takardune da files tuli da ita kanta bata san adadi suba. Sai dai gaba daya hankalinta da 2naninta ba akan aikin dake gabanta yake ba, uban tagumi kawai ta zuba da dukkanin hannayenta biyu, glass din data saba sakawa a idonta ajiye yake a gefe wanda hakan ya fito da hawayen dake zubawa a idanunt a zahiri. 100% na hankalinta ya tafi ne ga karanta wasikar jaki, koda ba’a fada ba tabbas abinda take tunani nada alaka da wani matsanancin yanayi da take ciki. uk da na’urar dake huro iska tako ina daga sassa ofis din amma hakan bai hana ta hada wani zazzafan gumi ba wanda ke ketowa daga sassan jikinta, hadewar da gumin fuskarta da hawayen dake kwaranya daga idonta suka yine yasa suka jika takardun dake gabanta sharkaf.

Nisan da tayi yasa bata ji shigowarsa ba duk da sallamar da yayi ta kwalawa, Ahmad yayi turus a gabanta yana dubanta kawai dai dai sanda fuskarsa ta canja daga murmushin da yakeyi, ya zauna a kujerar dake fuskantarta sai dai har yanx bata dawo hayyacinta ba bare ta fahimci cewa wa ya shigo inda take, da alama bata ma san a inda take ba. bayan ya gama yi mata kallon AL’AJABIN ne kum ya kira sunanta. HUMAIRA hade da dukan tebirin dake gabanta. Firgigit! tayi tamkar wacce ta tashi daga barci, tab inda take da kallo kamar wacce ta ganta a sbn waje. Lokaci guda tayi kokarin goge hawayen dake idont ta kakalo yake ta maye gurbinsa dashi tace ” Ah….Ahmad yaushe ka shigo??” Ya dan bita da kallo yace ” Humaira kukan me kikeyi??” Tayi saurin girgiza kai tace ” kuka kuma? ni… ba kuka nake yi….ba.” Ahmad ya danyi guntun murmushi yace ” Humair a rayuwa damuwa bata taba buya domin ita abac da ba a zuciya kawai take zama ba rubutu takeyi da manyan baki akan fuska wanda kowa sai ya gani, kuma koda ma tana buya to ta yiwu girman taki damuwar ta wuce a boyeta don da zata boyu da kin boyeta. Ya rankwafo da kansa gareta yace ” Me zai hana bani dama nasan wani abu a rayuwarki, ta yiwu in da hanyar taimakonki koda da addu’a ne.” Idan kana yiwa Allah ka daina yimin wannan maganar ba wani dalili da zaka damu sai kasan labarin rayuwata, Aikine kawai ya hadamu dakai k tsaya a iya haka ko don tsare mu2ncinka a idona. Ahmad ya daga kafadarsa kadan yace ” 2nda ba zaki fada min ba shikenan, dama nazo ne na san dake gobe muhimman kayan aikinki zasu karaso saiki shirya.” ya mike tare da cewa ” see U next time “.

 Ahmad!! Ta kira sunansa dai dai sanda yake gaf d ficewa, ya tsaya cak a hankali kuma ya dawo izuw gabanta. Ta dago kai tace ” Don Allah kayi hakuri kayi min uzuri kwakwalwata ce ba zata juri tuno dukkan abinda ya faru dani a baya ba, amma ta yiwu wat rana ka sani.” Ahmad ya zauna bisa kujera yace ” Humaira wasu lokutan kunshe abu a rai cuta ne furtashi kuma warakane, yana da kyau na rike wani hujja koda guda dayane wadda zan rika nayi miki uzuri idan na ganki a yanayin dana ganki yau.,” Hawaye suka sake gangaro mata idanunta suka bude karrr tace ” Tunda uwata ta haifeni ban taba ganin mutum mara yarda ba irinka, baka taba yiw mutum uzuri? kai kawai abinda kake so shine a ranka?? To bazan fada maka ba, tunda baya cikin sharadi abinda dole sai ka sani kafin ka zauna dashi, idan ka kara yimin wannan tambayar ba zaka kara ganina ba har abada. Akan me?? Ta fada da karfi sannan ta dora ” Na zabi nayi aiki ne badon kudi ko don na samu wani abu ba sbd nafi karfin wannan, sai don ina tunanin hakan zai rage wani yanki na damuwa idan kuma kace takurata zakai kake bijiro min da wata damuwar abu me sauki na hakura.” Takai karshen doguwar maganar tata da ajiyar zuciya. Ahmad yace ” Nida kike ganina mutum ne me so samun labarai musamnan na al’ajabi, daga cikin labaran dana samu akwai a 2nanina naki shine za zamo na farko a ban al’ajabi, baki da wani zabi dolene nasan labarinki a yau.” yakai karshen maganar cikin daga murya. Lokaci ta kara sauyawa ta hade rai ta kara fusata gami da harzuka ta kauda kanta domin ta gama zuwa iya wuya, Dame wannan mutumin yake takama daya isa yayi mata dole. Ta mike ta rufe laptop din dake gabanta ta jefa masa mukullin ofis din ta jawo babbar jakarta ta rataya cikin tsawa tace masa ” Don ina aiki dakai ba yana nufin ka cutar da kwakwalwata bane, idan badon na kaskantar da kaina ba kai nafi karfin ka min dole wlh. Ga mukullinku nan tafiyata itace mafi sauki daga wannan matsin lambar taka.

Ta ture kujerar kusa da ita cikin sauri ta nufi kofar ficewa. Ahmad ya jawo mukullin ya rikeshi a hannunsa cikin sauri ya waiga kafin ta fice yace ” Ba wani abu bane idan kin tafi hakan shine ma ya tabbatar min da mummunan zargin da nakeyi akanki.” Duk da batai niyya ba amma sai da tayi saurin waigowa duk da cewa daf take da ficewa. Ahmad ya juyo sosai ya dora da cewa ” Na yarda da cewa ke MUGUWA CE, tabbas ke ba mutuniyar kirki bace, a rayuwarki babu komai sai ta’asa da rashin kirki, na tabbata wani mummunan abu kika aikata wanda yake bibiyarki kuma ya hana miki kwanciyar hankali……” Ya dakata da maganar yana kallonta. Idanunta suka zaro kamar zasu fado ‘iiihhhhhhh!!!! bakinta ya fada dai dai sanda ta rike bakin nata, zuciyarta ta fara saka mafi munin maganganun da aka fada mata, lokaci guda kwakwalwata ta gaza jurar amsar kalaman, kanta yayi nauyi tayi saurin dafeshi, idanunta suka fara juyewa wanda yazo dai dai da sanda kafafuwanta t gaza daukar ganga jikinta, cikin sauri kwakwalwarta ta tuno mata abinda yace.

Na yarda da cewa ke muguwa ce, tabbas ke ba mutuniyar kirki bace, ………. na tabbata wani mummunan abu kika aikata daya hana miki kwanciyar hankali…… Dai-dai lokacinne ta karasa sulalewa kasa cikin yanayi na suma…. Wai wai wai wannan al’amari akwai rikici.

Tsaye yake kofar dakin kula tare da yin aikin gaggawa na asibitin yana kaiwa da komowa, mintuna talatin kenan da kawowa kuma likitoci suka hau aiki amma ba wani bayani har izuwa yanzu. Zuciyarsa nata yi masa sake-sake kala-kala, me yasa zaiyi haka?? Don me ma ya ma zan takura akan abun da bai shafeni ba?? Kada fa nayi silar kashe yar mutane ko na jawo mata w……….

Hango fitowar likitan daga dakin da yayi ne yasa ya dakata daga zancen zucin da yake yi ya tunkar inda yake da gaggawa, doctor ya akai?? ya ake ciki?? zata lafiya kuwa?? Ya tambaya cikin tashin hankali. Likitan ya dubi nurses din dake tare dashi yace ” kuyi ku samo abin nan yanzu “. To suka fada tare da wucewa. Ya juyo ga ahmad yace ” Karka shiga damuwa da yawa zata sami sauki bada jimawa ba insha Allah, mun shawo kan abin sai dai har yanzu bata farfad ba. Idan mahaifinta ko mahaifiyarta sunzo ina son ganinsu a ofis.” Ya wuce da sauri. Ahmad baiyi wata-wata ba ya fada dakin kai tsaye izuwa gabanta yabi ta kallo cikin sanyin jiki, ALLA SARKI humaira zuciyarsa ta fada. Ya danja da baya ya zauna a kujerar dake gefen gadon da take kwance har yanzu idonsa akanta yake. Abinda ya fara fado masa arai shine: Tayaya za’ai iyayenta ko wani nata yasan halin da take ciki tunda bashi da zabi dole sai hakan ta faru.

Tuno da wayarta da yayi wacce ke rike a hannuns yasa yayi saurin dagota kai tsaye ya shiga contact dinta, abin mamaki ba wasu lambobi ne da yawa ciki ba, ya tsa ya a dai dai lambar da aka sa MY MUM, ya danyi jim kamar me jin tsoron kiran bisa dole ya danna kira tare da karata a kunnensa. Yayi shiru ya kasa magana har sai sanda wacce t daga wayar tace ” humaira lfy shiru har yanzu?? Ahmad dakyar yace ” ba ita bace ni sunana Ahma ina fatan kece mahaifiyarta??” Ehh… nice…. mahaifiyarta lfy dai ko?? Ta tambaya da sauri. Humaira ta yanke jiki ta fadi yanzu haka muna asibiti….” Subhanallahi!!!! Ta fada cikin rudewa tare da cewa kuna wane asibitin ne?? Ahmad cikin sanyin murya yace ” ALBARKA HOSPITAL dake nan cikin……..

“kafin yakai karshen maganar ta katse wayar. Yabi wayar da kallo lokaci guda ya juya ga fuskar humaira yabi ledar ruwan da aka jona mata da kallo izuwa inda yake a rataye can sama, ya dafe kai, ko kadan baya son kallonta musamman idan ya tuno abinda ya faru kafin shigarta halin da take ciki. mintuna talatin ya sake shafewa kafin mahaifiyarta da wata da baisan ko wacece ba suka zo, da tambayarshi suka fara. Ahmad yace ” muna cikin magana to sai ta mike lokaci guda kuma ta yanke jiki ta fadi. mahaifiyartata tace ” to yanzu me likitan yace??” Ahmad yace ” cewa yayi idan wani yazo daga cikinku yana bukatar ganinsa. Mahaifiyar tata ta dafe kai tace ” humaira ban taba ganin mutum irinki ba, ace ke ba zaki taba manta baya ba? ba zaki taba daina tunanin abinda ya wuce ba? Wasu hawaye suka gangaro mata, wacc suka zo taren ta fara rarrashinta, Ahmad kuwa binsu kawai yake da kallo. Ta juyo ga Ahmad tace ” sai kayi kokari ka tafi tunda munzo kada dare yayi maka. Ya gyada kai kawai ba tare daya motsa ba, ya dade kafin ya tashi ya mika musu wayar humaira kamar mara laka a jiki a haka ya fita daga dakin. zuwansa motarsa keda wuya yayi arba da jakar humaira ya dago ta tare da jujjuyata a hannunsa yasan tabbas tana ji da kyakyawar jakar tata sbd kusan kowanne lokaci da ita yake ganinta. Kamar ya fita yakai musu ita sai kuma ya fasa ya jawo kofar motar tasa ya kunnata yabar harabar asibitin. Jikinsa a sanyaye yake tukin, jinsa yake kamar sabon mara lfy a haka ya iso gida, da sauri ya wuce izuwa ciki yadda yake so kuwa momi bata falon sai saudat kadai kwance tana danna wayarta Ta amsa sallamar tasa kanta nakan wayar tare da cewa yaya ka dawo??

Ehh… na dawo ya fada tare da wucewa da sauri kafin ta dago kai izuwa dakinsa, dai dai sanda ta tashi zaune tabishi da kallo a ranta tace ” Wanna lfy?” jim kadan ta dan daga kafada tare da komawa ta kwanta. Yana shiga dakin nasa ya mayar da kofar ya rufe ya jingina a jikinta idonsa ya ciko da kwallah a hankali ya karasa ya jefa jakar tata kan makeken gadon dake dakin, fadawar jakar keda wuya ta bude abinda ke cikinta ya fito wanda yayi saurin canja fuskar Ahmad. Wani katon littafi ne me tsawo, fadi da yawan gaske. Ya zauna a gefen gadon a hankali ya jawo littafin ya kare mai kallo a haka a hankali kuma ya bude bangon littafin idonsa yayi saurin kara zarowa sanda yaci karo da hoton humaira me matukar kyau da haiba a kasa an rubuta AISHA HUMAIRA ISMA’IL ya karewa hoton kallo sannan ya bude shafin gaba anan ma hoto ne amma ba nata ba, wani kyakyawan saurayi ne da shekarunsa basu haura Talatin da daya 31 ba, kyakyawa ne na gaske a kasan sunan nasa ansa UMAR FARUK ABUBAKAR, Ahmad ya dade yana kallon hoton nasa ya sake bude shafin gaba nan kuma hotuna ne nata da wancan faruk din a samansu ansa FARUK & HUMAIRA, tsakiyarsu kuma dan gaf fin dake tsakaninsu ansa ONE LOVE!! daga kasa kum ansa LIFE TOGETHER DIE TOGETHER.

Littafin ya subuce daga hannun Ahmad sbd mamaki, dama halin da take ciki akan soyayya ne?? Waye kuma wannan faruk din?? Tambayoyin da suka fara zuwar masa kenan. Ya sake cakumo littafin da sauri ya bude shafin gaba na tafkeken littafin yaci karo da abinda yasa shi saurin gyara zama CIKAKKEN LABARINA. labarin humaira kenan?? ya tambayi kansa, yayi saurin gyara zamansa ya karasa karanta abinda aka rubuta a kasa, labarin farin ciki na gajeren lokaci daya jawo bakin ciki na har abada. Labari me tsuma zuciya da sanya shauki. Labari me tare da tarin Al’ajabi. Ahmad bude shafin gaba ya fara karanta labarin humaira daya dade yana burin ya sani. Cikakken SUNANA Aisha humaira, sunan mahaifin Alhaji Isma’il ishak daya daga cikin hamshakai kuma fitattun yan kasuwa a africa. Haifaffiyar garin kano unguwar Hausawa.

kuma SABAHUL KHAIRI..

 CIKAKKEN LABARINA. labarin humaira kenan?? ya tambayi kansa, yayi saurin gyara zamansa ya karasa karanta abinda aka rubuta a kasa, labarin farin ciki na gajeren lokaci daya jawo bakin ciki na har abada. Labari me tsuma zuciya da sanya shauki. Labari me tare da tarin Al’ajabi. Ahmad bude shafin gaba ya fara karanta labarin humaira daya dade yana burin yikakken SUNANA Aisha humaira, sunan mahaifina Alhaji Isma’il ishak daya daga cikin hamshakai kuma fitattun yan kasuwa a africa. Haifaffiyar garin kano unguwar hausawa……kuma Ya kasance sananne wanda sunansa ba boyayye bane sbd Allah yayi arziki na gaban kwatance, hakan yasa ya tara mutane masu yawa matuka kama daga ma’aikata, abokai da yan maula daban daban dake kaiwa dake nanike dashi a kowanne lokaci.

Ni kadai ce wacce mahaifina ya mallaka a matsayin Y’A hakan yasa na taso cikin gata, so, kauna da kulawa. Tun daga yarintata ba abinda nake nema in rasa, komai nace ina so sai an mallaka min ban taba yin kukan rashin wani abu ba. a kowanne lokaci mahaifina na nuna min ba abinda bazan samu ba sai dai idan bana so, tun dai bana yarda har na yarda domin kwakwalwata ta gaza tunano min abinda zan nema dukiyar mahaifina ta gaza samar min shi. Saboda son da mahaifina keyi min yasa kowa ke nan-nan dani da nuna kulawarsa akaina don ya samu abinda yake so a wurinsa, duk kuwa wanda ya kuskura ya taba ni to kashinsa ya bushe a wurin mahaifina. Matsala daya dana tashi da ita itace na raina mutani da nayi musamman talakawa da marasa galihu, gashi ko kadan bana son kula mutane bare na girmamasu sbd bana ganin kan kowa da gashi. ban damu na shiga harkar kowa ba kuma mafi yawa idan aka shiga tawa raine ke baci, hatta kawaye ban damu nayi ba sbd yadda nake jin nafi kowa. Ba wadanda nafi rainawa na taka yadda raina ke so irin yan aikin gidanmu kuma dole su kalleni don suna tabani sun san hukuncinsu kora ne don haka dole suka kyaleni nake cin karena ba babbaka, mutum dake da karfin taka min birki a wasu lokutan itace mahaifiyata da nake kira da MUM.

Wani lokacin idan na dauko rashin mutuncin daya wuce hankali takan kwabe ni wadda ita kadai ke yin hakan domin mahaifina komai nayi dai dai ne a wurinsa.

Tun ina da shekaru hudu aka saka ni a nursery ta musamman ba kamar saura ba, me tsadan gaske ce da kudin da ake biya a shekara daya kawai ya isa a dauki nauyin karatun yayan talakawa guda uku tun daga primary har zuwa jami’a. Direrba aka tanada don kaini kuma ya daukoni, idan ya kaini baya tafiya har sai an tashi ya dawo dani. Shekaru biyu kacal nayi aka matsar dani izuwa hamshakiyar makarantar da duk wani dan me akwai ke burin ganinsa a cikinta, wadda tun daga sunanta kasan tafi karfin talaka koma uban talaka, makarantar nada kyan yanayin data burgeni har yakai ban taba korafi da ita ba. Ina daya daga cikin dalibai abin alfahari a makarantar sbd kwakwalwata ta saurin gane abu wanda hakan ke kara min girman kai matuka. Duk da cewa makarantar kowa naji da kansa domin ba dan talaka a cikinta kowa ka gani daga gidan arziki yake, amma fa nawa girman kan yafi na kowa domin ko kawa daya ban yi ba sbd a ganina duk babu me aji dai dai dani. Sai dana shafe shekaru goma sha biyu anan primary & secondary, da shekaruna 18 na gama ta.

 A dai- dai wannan lokacinne kuma kari kan da ZUNZURUTUN KYAU ya kara bayyana, Wohoho!!!!!!!!!!! Kai idan ka ganni sai ka rantse da Allah ni balarabiya ce domin kadan zubi na bana hausawa bane, kamar yadda ake fada kuma nake gasgatawa a duk sanda na dubi kaina babu kamata a wannan zamanin indai fagen kyau ne. Nasha jawo accident idan ana tafiya dani a mota ban daga glass ba, nasha jawowa mutane karo da juna idan ina tafiya, duk wadda ke ji da kanta idan ta ganni sai ta fashe da kuka don taga karshen kyau, wasu fashewa suke da kuka suna cewa ina ma su sami 1/10 kyawu na. Kwalliya ma bata wani dameni ba sbd a cewata idan kyau bai cika bane ake neman kwalliya ta karasa cikashi amma idan kyau ya cika babu bukatar hakan. Mafi yawa harkar sharwoliya bata dameni ba koda a shigata nakanyi kokari na rufe jikina, mafi yawa kayan da nafi sawa ba wadanda basu kamata bane sbd ni ako yaushe na yarda na tsare mutuncina kuma a ko’ina. Bayan na kammala secondary a nigeria mahaifina ya nema min admission amma fa a oxford university dake kasar england, nayi murna sosai sbd ina da buri na bar kasata izuwa wata musamman kasashen turai. Da yake harka ce ta kudi nan da nan komai ya kammala kuma aka saka ranar tafiyata domin fara degree na farko a fannin kimiyar tattalin arziki wato (economics) da kuma lissafi. Ana gobe zan tafi ne bayan komai ya gama shiryuwa zaune nake nasa tafkekiyar televission din dake manne a jikin bango nesa kadan dani a cikin katafaren falon alfarma na gidanmu, cikin kwanciyar hankali nake kallon ba wani abu dake damuna. kaso 99% na hankali ya tafi ga kallon film din na DHOOM yadda jarumin film din ke raina hankalin yan sanda da dabaru daban daban, wucewar da daya daga cikin yan aikin falon tayi ta gabana yasa banga karashen abinda ya faru ba abinda ya tunzira ni kenan wulakancina ya motsa na kira sunanta da karfi.

 HANNE!! Ta juyo da sauri tana kyarma, nace ” Zo nan” Ta fara matsowa a hankali a hankali na daka mata tsawa nace ” gidan uwar wa zaki je??” Tace ” uhm… haji..ya ce ta kira…ni. “. Nace harareta nace ” kuma don ubanki shine ta gabana zaki wuce ko? Duk nan ba hanya bace??” Tayi shiru kawai tana makyarkyata bata ankara ba na zabga mata mari hade da fadin ” ba tambayarki nake ba??”. Karfin marin sai daya sa ta fadi kasa lokaci guda ta zarce da kuka.” Ahmad ya kauda littafin daga karantawar da yake yace ” Lallai wannan wulakanci har na siyarwa kina dashi ya gyara kwanciyarsa tare da mayar da idonsa ya dora da karantawa.

Karar data kwalla ne ya jawo hankalin mum ta fito da sauri tana tambayar lafiya kuwa?? Ta tsaya kawai tasamu a gaba tana kallo hade da hararata cikin takaici.

Mu Hadu A Kashi Na Biyu Al’ajabi Pert 2.

Leave A Reply

Your email address will not be published.