Allah yayiwa tsohon gomnan Gombe Alh Abubakar Hashidu rasuwa.

Alh. Abubakar Habu Hashidu shine gomnan farko a jihar Gombe.
Ya rasu yanada shekara  74 a duniya. 
Ya samu nasarar zaben gomna a jam’iyyar APP  a shekarar 1999 ya kuma sauka a shekarar 2003.
Hashidu ya samu nasarori  wajen kokarin ganin jihar ta zauna kafarta sannan yayi kokari wajen samarda ayyuka dayawa saidai bai samu nasarar kammalawa ba sakamakon faduwa zabe da yayi a shakarar 2003.
Hashidu ya taba zama ministan ruwa da albarkatu da kuma ministan noma a karkashin mulkin Babangida.
Allah yajikansa da rahma. 

Source: HausaLine.Com https://ift.tt/2uU0IoH

Leave A Reply

Your email address will not be published.