Amnesty Ta Zargi Sojojin Nigeria Da Kisan Gillar Mutane 150

Shugaba Buhari wanda tsohon janar din soji ne, ya yi yakin murkushe ‘yan tawayen Biafra.

Kungiyar kare hakki bil’adama ta Amnesty International ta zargi jami’an tsaron Nigeria da kisan akalla masu zanga-zangar lumana150 a watan Agustan bara.

Kungiyar ta ce sojojin sun yi amfani da muggan makamai wajen murkushe masu zanga-zangar da ke neman kafa kasar Biafra a kudu maso gabashin kasar.

Rundunar Sojan dai ta musanta zarge-zargen inda ta bayyana masu zanga-zangar a zaman barazana ga tsaron kasa.

Yunkurin kafa kasar ta Biafra ne dai ya haddasa yakin basasa a kasar kusan shekaru 50 da suka wuce.

Leave A Reply

Your email address will not be published.