An Hana Kwankwaso Bikin Aurar Da Zawarawa A Jihar Kano

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta hana taron daurin auren zawarawa da gidauniyar Kwankwasiyya ta shirya a jihar.

Gidauniyar ta tsohon gwamnan jihar, Injiniya Rabi’u Musa kwankwaso ta shirya aurar da zawarawa 100 ne a filin sukuwa a ranar Alhamis.

Sai dai ‘yan sanda sun ce sun soke daurin auren ne bayan sun samu wasu bayanan sirri da ke cewa wasu za su kawo yamutsi.

Kawo yanzu gidauniyar ba ta ce komai ba game da batun.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamantin jihar Kano, a karkashin jagorancin dokta Abdullahi Umar Ganduje, ta fara tantance zawarawa da ‘yan mata.

Dangantaka ta kara tsami tsakanin Kwankwaso da Ganduje tun a watan Maris din da ya gabata, bayan mutuwar mahaifiyar gwamnan mai ci yanzu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.