An Kaddamar Da Sabuwar Motar Kabu Kabu Mai Tashi Sama.

 flying taxi

Taron wasu matasa a kasar Germany, sun samu nasarar kaddamar da wani sabon jirgi mai saukar angulu, don amfani da shi a wajen sufuri “Flying Taxi” motar kabo-kabo mai tashi sama.

 Tsarin jirgin shine, zai dauki mutane biyar, kana yana tafiya da zatakai kimanin nisan kilomita dari uku 300. Misallin nisan Abuja zuwa Kano, cikin kankanin lokaci.

 Burin su shine, a takaita yawan lokacin da mutane kanyi a yayin tafiya, wanda idan tafiya zata dauki mutun awa biyar, zai iya kammalata cikin mintoci arba’in.

 Ana cajin jirgin, kana yana amfani da hasken rana wajne samun karfin tafiya. A cewar shugaban kamfanin na “Lilium” Mr. Daniel Wiegand, wannan wata hanyace da suka fito da ita wadda zata magance matsalolin sufuri a duniya.

® Voahausa

Leave A Reply

Your email address will not be published.