An Kai Uwar ‘Yar Da Aka Yi Wa Fyade Sashin Kula Da Masu Tabin Hankali

An Kai Uwar ‘Yar Da Aka Yi Wa Fyade Sashin Kula Da Masu Tabin Hankali

Daga Aminu Ahmad

Maryam ita ce mahaifiyar yarinyar nan, ‘yar wata shida da ake zargin an yi wa fyade kwanakin baya.

Maryam wadda ake yi wa inkiya da ‘yar China,  rahotanni sun muna cewar tana shaye-shaye ne da ya wuce kima inda har hankalinta ke gushewa, lokaci-lokaci.

Rahotanni sun nuna cewar tun yarinyar tana jaririya ‘yar wata biyu, uwar take barinta, ta tafi yawonta, inda take kwashe kwanaki da dama bata dawo gida ba, ballantana ta san halin da ‘yarta ‘yar watanni shida ke ciki.

Na kusa da ita sun tabbatar da cewa a duk lokacin da ta dawo gida to, ta kan dawo ne ba a cikin hayacinta ba, wanda ko a lokacin da aka yi zargin  yi wa ‘yar ta ta fyade, kwata-kwata ba a san inda ita mahaifiyar take ba, kasancewar ta kwashe kwanaki bata gida shi ya sa ake zargin akwai lauje cikin nadi.

Idan ba ku manta ba dai labarin fyaden da aka yi wa wannan yarinya ya yi ta yawo a kafafen sadarwa na zamani, abin da ya ja hankalin mahukunta a kasar nan, saboda yanayin labarin da aka bayar. To, ashe ba a nan labarin ya tsaya ba.

Za mu kawo muku cigaban labarin dangane da kurar da ke neman tashi kan wannan al’amarin.

©Zuma Times Hausa

Leave A Reply

Your email address will not be published.